Chapter fifty- one

142 20 0
                                    

Ammabuwa jiki a sanyaye tace "toh  Ammi, Allah ya baki lafiya uwata ta gari, Allah ya dadda karewa kuma Allah ya bar mana ke".

Sake matsowa tayi ta rungumeta gam a jikinta sa'anan tayi musu sai da safe ta fice daga cikin dakin.

Huda na ganin Ammabuwa ta fice daga dakin, itama ta mike tace "Ammi ina zuwa  bari na gayawa ya' Ammabuwa ta tawo mana da kayan sawa gobe, yanzu zan dawo".

Ammi kai kawai ta gyada mata, ta fice daga dakin.

Tana fita tabi bayan Ammabuwa wace take tafiya tare da Anty Rakata suna tataunawa.

Anty Rakata ta dubesu tace "ke kunga dai wanan asibitin na masu kudi ne. Duba fa yanda ko ina yake tsab" Anty Rakata ta fada tana karewa ko ina kallo.

Ammabuwa tace "ai kam ina jin sai dai mu koma asibitin gwamnati don bazamu iya da wanan nan ba".

Huda ta katse musu maganar da sukeyi tace "yanzu ya'ammabuwa ajiye wanan nacin naki zakiyi a gefe na cewa sai kin biya kudin komai da kanki don Muhseen ya rigada ya biya mana kudin komai na asibiti".

Ammabuwa ta dubeta tace "Muhseen fa kikace? Muhseen ba saurayin kawarki bane?"

Anty Rakata tace "kai! Daman wanan yaron shine saurayin Summaya?"

Wani irin kallo Huda ta watsa mata cike da jin haushinta tace "ya'ammabuwa ki samu ki koma gida kafun dare yayi sosai kinga hanya babu kyau gashi kuma gobe kinada aiki da safe. Dan Allah ki tafi da Anty Rakata".

Suna cikin wanan maganar sai ga Summy ta karaso cikin sauri tana kiran Huda. Huda mikewa tayi taje ta tadda ita.

"Huda ya jikin Ammin yanzu? Zan iya shiga na dubata?"

Huda tace "eh tama soma bacci dana baro ta. Yanzu ya'ammabuwa zata wuce gida ni zan kwana da ita".

"Toh bari na gayawa mahmud ya kaisu mana, inyaso ni sai Muhseen ya kaini gida".

Huda tace "noo Summy karki damu, ba sai kinyi wanan wahalar ba".

Anty Rakata dake tsaye tana sauraron maganarsu, takaici ne ya isheta tace "laa...yanzu Huda bakin cikin naki har ya kaiga haka? kawarki tace zata sa a kaimu har gida da mota ki wani ce a'a? Wanan wani irin bukulu kikeso kiyi mana?".

Harara Huda ta watsa mata don ji tayi kamar ta rufe Anty Rakata da duka tsabar haushinta da takeji.

Dariya kawai summy tayi tace "bakomai Anty, idan kun shirya tafiya yanzu sai nayi mishi magana ya kaiku".

Ammabuwa itama ta karaso tayiwa Summy godiya sosai tace dan Allah ta mika godiyarta zuwa ga Muhseen.

Summy tace babu "babu komai ya' Ammabuwa, insha Allah zaiji".

Bangaren su Muhseen kuwa, sun fito daga office din Ashraf suna tafiya tare, Ashraf ya soma fada mishi cewa ya samu gida. Yace " zanso kaga gidan kuwa Muhseen, gidan yayi babu laifi kuma gashi kusa da asibiti. So ina tunanin kwanan nan zan tare insha Allah".

Cike da sanyin jiki Muhseen ya juyo yana dubansa yace "Ashraf yanzu tarewan me kakeso kayi fisabilillah? Na gaya maka kwanan nan zanyi tafiya me zai hana ka cigaba da zama a gidan".

Ashraf ya sake ajiyar zuciya yace "ba haka bane Ashraf, nasan kana son mu cigaba da zama tare but I think lokaci yayi nima daya kamata na samu muhalina nakai na, kaga rayuwar nan babu tabbas kuma yanada kyau mutum yasan matsayinsa ya tsaya a inda Allah ya dora sa, koba haka ba?"

Cike da rashin fahimta Muhseen yake kallonsa yace "ban gane ba? Meya kawo wanan maganar kuma?"

Ashraf zai bashi ansa kenan sai ga Summy nan ta karaso cike da zumudi tana fadin "Habibi, nayiwa driver magana daya kai su yayar Huda gida inyaso nida kai sai mu wuce gida tare? Koya kace?" Ta karasa maganar tana aika masa da tsadaddar murmushinta.

🔥Huda🔥💄Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon