Chapter Five

513 56 1
                                    


Ammi ce ta bata ansa da "Ban gane ba, yanzu duk kayan da kike dasu huda basu isheki ba sai kin nema kari? A da So nawa zan sa a dinka miki kaya in kawo kice style din bai miki ba, ke ba dinka miki shi yanda kikeso ba. kaza kaza, mene mene. Ba abun da baki fada akai. Eh? Wai wani irin kishi ne dake huda wanda har yayyar taki ma bazaki kyale ba? Kema kinsan batada issasun kayan zuwa aiki, ina ranan kika bude wanan shegen mara kunyar bakin naki kika ce mata tsumokara take sawa zuwa wajen aiki. Ita bata san meye gyaran jiki ba. Ba abunda baki fada mata ba, yanzu shine zaki dawo kice kina son irin dinkin jikinta?"

Tabe baki huda tayi tace " ni gaskiya ammi sai an mun sabon dinki, kawai ni irin lifayar nakeso, ni yaushe rabon da amun sabon dinki a cikin gidan nan.

Ammabuwa na jinsu bata ce komai tunani kala kala ne ke mata yawo aka daga bisani da katse musu maganar da "ammi ni zan wuce aiki yanzu kar nayi lati." Ta mike tazo ta tsuguna a gaban ammi. Ammi ta soma mata addu'ar da neman kariya kamar yanda ta saba musu idan zasu fita.

Wani irin haushi ne ya ziyarci zuciyar huda ganin ammi ta basar da maganar sabon dinki datace ayi mata. Kallon Ammabuwa da sabon dinkin dake jikinta tayi, nan take taji wani irin kishi ya taso mata, ta Kalla gefenta taga butan shayi da sauran ruwan lipton a ciki wanda aka sha aka rage. Shedan yaci galaba akanta bata san sanda ta dauki butan shayin ba tayi kamar zata kai waje, daidai inda Ammabuwa take tsugune ta saita bayanta ta sake butan shayin ruwan lipton din ya juye a bayanta. Wata razananan Kara ammabuwa ta sake ta mike da sauri jin ruwan dumin da aka juye mata a baya. Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, A firgice ammi ta mike ta ruko Ammabuwa. Huda na tsaye sai faman zaro ido takeyi ga bayan ammabuwa duk ta bace.

"Na shiga uku na lalace ni fanneh, nikam me na haifa na kawo duniya? Mezan gani haka huda? Kina son ki kashe yayarki ne?," Ammi duk tabi ta rikice ta kamo ammabuwa wace take kokarin cire kayan jikinta.
"Zo nan naga bayan ki."

Huda ce Ta marairace fuska tana fadin "Yaya Ammabuwa dan Allah kiyi hakuri wlh nazo daukan butan ne bansan yanada zafi ba ya kubuce mun a hannu".

Ammi ce ta fara mata fada kamar zata rufeta da duka.
Ammabuwa ta kamo ammi tana fadin "Ammi ki kyaleta kawai ruwan bai konna ni ba, kayan ne kawai ya bace, bari naje na chanza ta" Ammabuwa ta fadawa ammi hawayen da suka ciko a idanunta suka gangaro mata bisa kuncinta ta sa hanu ta share ta fice daga dakin.

Ammi ce ta nufo inda huda take tsaye gadan gadan. Huda ta fara matsawa baya
ta marairaice fuska tana fadin "wayo, dan Allah kiyi hakuri ammi, wlh da gaske nake, ban san butan nada zafi ba ta kubuce mun."

Ammi ta karaso ta dauko butan tasa hanunta ta dafa " taji sanyi babu alamun zafi a butan"

"Karya kike huda, butan nan babu alaman Zafi a jikinta, da gangan kikayi"

"Wlh ammi ba da gangan bane akwai zafi butan, konani tayi".

"In ma da zafi huda sai ki rasa inda zaki sake, sai a bayan yayar taki. Da ruwan da zafi kika konata fa? Ammi zuciyarta a raunane take kallon huda, gaba daya ta tsorata da yanayin yarinyar. Bata taba kawowa a ranta cewa bakin halinta ya kai ga haka ba musaman ga yayarta. Ta tsaya tayi shiru tana kallonta don tama rasa mai zatayi wa huda don in ta biyewa zuciya sai ta kasheta a banza.

"Nasan kin aikata hakan ne don kawai kina kishin ta saka sabon kaya, meyasa kike da kishi ne haka huda?"

"Ammi yaya Ammabuwa batada abunda zanyi kishi da ita akai. In ma akwai abunda zan yi kishi da ita, bai wuce irin so da kulawan da kike nuna mata ba fiye ga wanda kike nuna mun. Ammi kinfi son yaya Ammabuwa akai na."

Ammi ajiyar zuciya ta sake ta soma magana a hankali " huda daga ke har yayarki Ammabuwa duk ni na tsugana na haifeku, dukanku matsayinku daya a wajena. Babu wacce nafiso fiyye ga dayar. Kema kin san da hakan. Amma huda na hango wani abu a tattare dake, kinada bakar zuciya, kuma in har kika bari yayi tasiri akan ki toh zaki sha wahalan zama tare da mutane. Keh ya' tace kuma dole na fada miki gaskiya idan kinyi ba daidai ba, dole na dawo dake kan hanya idan naga kina neman hanyar bata.

🔥Huda🔥💄Où les histoires vivent. Découvrez maintenant