Chapter fifty

212 25 0
                                    

Ran Ashraf ne ya sosu da abunda ta fadi yace "yanzu Huda kin gwamace ki nema taimako wurin Muhseen da ki nema nawa? Yanzu ke a tunaninki zan ganki cikin irin wanan halin naki taimaka miki?"

"Kamar yanda ka fadi Ashraf, na kiraka ne a matsayinka na likita da kazo ka duba mun Mahaifiyata, amma you were not there. Muhseen ne kadai yazo ya taimaka mun".

Ashraf cike da jin tausayi yace "Huda kema kinsan you can always count on me kuma kinsan bazan taba ganin kiranki naki dagawa ba. Mantawa nayi da wayata a gida ina sauri saboda emergency kiran da aka mun." Ya karasa maganar yana kokarin matsowa inda take.

Huda ta daga hannu ta dakatar dashi tana fadin "dakata Ashraf, yanzu ba wanan bane damuwata ba. The only thing i care about right now, shine lafiyan mahaifiyata don haka ka sarara mun".

Tana gama fadin haka ta juya ta tafi ta barshi tsaye a wajen.

*********
Bangaren Ammabuwa kuwa tsaye take a bakin window hankalinta a tashe, tayi zurfi cikin tunani, sai faman kwararo addu'oi takeyi babu iyaka. Tana tsaye a hakan ta soma jin wani irin daddaden kamshin turare ya soma ziyartar hancinta. Cikin sauri ta waigo taga Dr Abdul tsaye kyakyawar fuskarsa babu yabo babu fallasa yana tsaye yana kallonta.

Cike da damuwa, kirjinta na bugu ta karaso ta soma tambayarsa "Doctor, ya jikin nata yanzu?"

Dr Abdul yace "Alhamdulillah da sauki jikin, don yanzu mun samu ta fito daga crises nata kuma ana mata CAT scan. Karki damu, Insha Allah she'll be fine".

"Toh Allah yasa doctor, Nagode sosai Allah ya saka da alkhair wlh bansan me zance dakai ba don yanzu haka ma kunyarka nakeji wlh. Ban gama biyanka kudin aikinka nada ba gashi wani ya sake sawo kai".

Dr Abdul ya lura da yanda jikinta yake bari yana rawa yace " calm down Ammabuwa, muje ki zauna tukuna sai muyi magana"

Daya daga cikin kujerun wurin ya kaita suka zauna, ya juyo yana fuskantar ta yace " Ammabuwa, nine fa likitan mahaifiyarku. Kuma nace miki babu wani chargi dazan muku, inaso ki kwantar da hankalinki ki cire wata damuwa a ranki. Addu'a kawai zaku cigaba da mata".

Zatayi magana ya katseta da " kuma ina so ki dauki wani zancen biya ki ajiyeshi a gefe. This is not about Ashraf ko Huda. Let's make this between me and you. Ko ya kika ce?"

Ammabuwa ta girgiza masa kanta tace "gaskiya doctor bazan iya ba. Dole na biyaka kudin aikin ka".

Dr Abdul dayaga batada niyan amince masa akan batun biyan yasa shi fadin "toh shikenan, naji zaki biya amma bada kudi ba. Yanzu abu daya nake bukata a game dake".

"Wani abu kenan?" ta tambayeshi.

Dr Abdul yana kallon cikin kwayar idanunta yace "inaso Ki ajiye wanan doctor din a gefe ki ringa kirana da sunana Abdul.".

Yana gama fadin haka, ya da'an sakar mata murmushi sa'anan ya mike ya tafi. Ita kuwa ta bishi da kallon mamaki don tama rasa me zata ce.

Dr Abdul yana barin wajen sai ga Anty Rakata nan ta karaso cikin sauri hannunta rike da bargo da wata leda mai dauke da flask din ruwan zafi tace "ya jikin Ammin yanzu? Melikitan yace? Kinga gashi ma na taho muku da bargo da ruwan zafi don nasan zai iya yuwa ku kwana anan".

Ammabuwa ta dubeta tace "toh yaran fa? Wa kika barwa su?".

"Karki damu nayiwa zuwaira magana, ta tura babbar yar'ta Asma'u taje ta zauna mun dasu kafun na dawo".

Ammabuwa jiki a sanyaye tace "toh shikenan Anty Rakata".

Bangaren Huda kuwa bayan ta tafi ta bar Ashraf tsaye a wajen ta sauko kasa ta tadda Muhseen da Summy tsaye suna tataunawa.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora