Chapter Seventy-five

164 17 0
                                    

Firgigit... Muhseen ya farka daga baccin da yake yana furta kalman innalillahi wa ina illaihi raji'un! zufa na faman tsarko mishi ta ko ina.

Gabadaya a rikice yake don mafarkin daya gama yi ba karamin gigitashi yayi ba. Sai faman zari ido yake yana dube dube yana karanto adduo'i.

Meke shirun faruwa ne? Ya tambayi kanshi.
Me mafarkin nan yake nufi?

Tunanin Summy ne ya fara fado masa nan take ya zabura ya zaro wayarsa daga saman bedside table ya duba time yaga karfe uku saura na dare babu shiri ya duro daga kan gado ya shige bayi ya dauro alwala ya fito ya hau kan sallaya ya soma jero nafilfili yan rokon Allah yasa yafi karfin zuciyansa don shi har ga Allah yasan yana kaunar Summy har cikin ransa kuma bazai so yaci amanarta haka ba. Hudan ce gabadaya tazo ta rikita masa lisafinsa yana zaman zaman sa.

Sai daya tsaya yayi sallan asuba tukuna ya koma kan gado amma ya nema bacci ya rasa, har gari ya waye idonsa biyu.

Bai tsaya wata wata ba, don babu abunda zuciyarsa ke hasko masa illa yaje yaga Summynsa ko zai samu sasauci cikin zuciyarsa.

Ko daya kirata a waya ta sanar dashi tana gida yace gashi nan zuwa. Yana isa gidan ta fito cikin sauri ya karasa ya kamo hannunta cikin nashi ya rike gam tamkar za'a kwace mishi ita. Ganin yanda ya rikice mata baya cikin nutsuwa ne yasa Summy ta soma tambayarsa, "Habibi lafiya? What's wrong?"

Muryansa na rawa ya soma fadin "Summy... baby, i love you so much. Kece farincikina kuma kece rayuwata. Bazan iya rayuwa da wata macen in bake ba. Ina matukar sonki Summy na". Ya fada yana dada matsowa kusa da ita tamkar zai shige jikinta zuciyarsa na harbawa da karfin gaske. Sosai yake jin tsoro hade da fargaban yanda yake kokuwa da zuciyarsa akan tunanin Huda.

Cike da mamaki Summy take kallonshi don bai taba rikice mata haka ba yana furta mata kalman so, sai taji dadi har cikin ranta ta sakar masa lalausar murmushi tana jin sonsa na kara huda tsokar dake makale cikin zuciyarta.

A hankali Muhseen ya kamo fuskarta cikin tafin hanunsa yana shafawa yace "baby daga yau bana son wani abun da zai kuma seperating dina dake. Zan dinga kaiki makaranta da kaina kuma naje na daukoki da kaina daga yanzu har sanda akace ke matata ce. I want to always be with you".

Cike da jin dadi Summy tace "nima haka habibi. Shiyasa nake son na rokeka alfarma da'ya".

"Wace alfarma kenan baby? Ya tambayeta yana kafeta da idanunsa.

"So nake ka bawa Huda off na rana daya ta rakani kasuwa muje mu duba kayaki na fitan anko."

Jin ta ambaci sunan Huda yasa bugun kirjin Muhseen ya karu, yayi saurin hadiye abun dayaji ya taso ya tokare masa makoshi sa'anan yace "sure why not, anything for you sweetheart. And there's another thing. Yau idan mun hadu da Huda inaso nayi magana da ita".

"Maganar me kenan habibi, tayi maka wani abu ne?" Summy Ta tambayeshi cike da damuwa."

"No ko kadan. She's doing her work perfectly okay." Ya danyi jimm yana nazari sa'anan ya cigaba da fadin "kawai gani nayi she doesn't have to be working for me tunda ba binta kudi nakeyi ba, Besides Ashraf ya rigada ya bani wanan kudin toh aikin me kuma zata cigaba da mun? Kema ki duba ki gani baby. There's no need"

Shiru Summu tayi tana nazari daga bisani tace " ai Huda tasan Ashraf ya rigada ya biyaka wanan kudin".

Cike da mamaki Muhseen yace "ta san da hakan? kin fada mata ne?"

"Yess ranar muna hira na sanar da ita".

Shiru Muhseen yayi kansa a daure, toh idan tasan cewa Ashraf ya rigada ya biya meyasa zatayi insisting akan sai lallai tayi masa aiki? Kallon Summy yayi daga bisani yace "Yanzu muje na saukeki a makaranta tukuna karkiyi latti. Idan mun hadu da Hudan sai mu tattauna naji ta bakinta".

🔥Huda🔥💄Where stories live. Discover now