Chapter fourty-eight

184 19 0
                                    

Cike da tashin hankali Ammi take kallonta, Huda ta da'an sassauta murya tazo ta tsuguna gabanta tana fadin "kiyi hakuri Ammi, kawai dai ina cikin wani yanayi ne na tashin hankali. Yanzu haka ma kaina ciwo yake mun, Zan shiga ciki na da'an kwanta".ta karasa maganar tana mikewa sa'anan ta shige cikin daki.

Ammi tabi bayanta da kallo cike da tashin hankali tana tunanin meye ya hada Huda da Ashraf da har zata daga hankalinta haka.

Huda tana shiga daki ta nema wuri a gefen gado ta zauna, tasa yatsa daya a baki tana ciza a hankali wasu hawaye masu zafi suna gangaro mata bisa kunci.

Wani irin haushi da tsana da kuma dana sanin haduwa da Ashraf ne ke cinta a rai, Ta kai kusan 20 mins a hakan tana zaune, Ammi tayi sallama ta shigo.

Huda na ganinta ta kawar da kanta gefe tana share hawayenta.

Ammi tazo ta zauna kusa da ita ta kamo hanunta  tana fadin "Hudah, dan Allah ki fadamun abunda ke damunki, nifa mahaifiyarkice idan baki fada mun abunda ke damunki ba, wa zaki fadawa eh? Yanzu Meya faru tsakaninki da Ashraf?"

Huda tayi shiru tana jinta bata ce komai ba.

Idanun Ammi ne suka sauka kan jakar data dawo dashi, ta hango lifayar da kuma turaren wutan data hada mata ta bawa Summy, Hannu tasa ta janyo jakan tana fadin "Huda baki bawa Summayya sakona ba, ko kin manta ne?"

Huda ta dubeta ta jajayen idanunta tace "Ban manta ba Ammi, amma nidai gaskiya bazan iya bawa Summy waeanan cheap kayan ba don tafi karfin su, ita da takeda laces da atamfofi masu tsada, turaruka ma musamman takesa ayi mata daga kasan waje. me zatayi da waenan?"

Ammi tayi shiru tana kallonta zuciyarta na tafarfasa tace "Amma wanan turaren musamman na zauna na hada mata da kaina, lifayan nan kuma tun daga maiduguri aka aiko mun da ita banyi amfani da ita na a ajiye..."

Huda ta katseta da "Nidai Ammi har yanzu kin kasa ganewa, ina nufin Wanan nakasashiyar Summy tanada komai babu abunda ta rasa, toh me kuma zatayi da waenan kayan?"

Cikin zafin rai Ammi tasa hannun ta buge mata baki tace "kanki daya kuwa Huda?!bana ce kar na sake jin kin kira Summaya da wanan sunan ba?!"

A fusace Huda ta mike tana dafe bakinta tace " Toh akan me bazan kirata da hakan ba?! Dubeta fa babu abunda ta rasa tanada komai, rayuwarta na tafiya daidai kamar yanda ya kamata, batada wata matsala! Ni meyasa rayuwata bazata kasance haka ba?!"

Ammi itama ta mike ranta a bace ta soma magana cikin kakausar murya tace"wlh Hudah idan na sake jin kin furta wata mumunar kalma akan kawarki Summayya saina saba miki agidan nan. Yar banza shashasha kawai, mara kirki wace bata san mutuncin dan Adam ba. Yanzu zaki fadamun abunda ya hadaki da Ashraf ne ko saina tattaka ki anan!"

Cike da zafin rai Huda ta soma fadin "meye ma Ashraf baiyi mun ba Ammi! Ashraf ya yaudareni, yaci amanata."

"Ban gane ya yaudareki ba?"

"Ammi Ashraf ya sani tunanin cewa yanada kudi ashe talaka ne shi, matsiyaci, bashida ko sisi!"

Ammi ta dafe kirji, muryarta na rawa tace "yanzu Huda daman saboda kudi kike tare da Ashraf?"
Duka da mari ta soma kaiwa Huda ta ko ina tana fadin "meke damunku ne Huda! Wani irin rayuwa ne wanan kika jefa kanki ciki! Wani irin bala'i ne wanan!...o ni na shiga uku, yanzu saboda kin gano bashida kudi shiyasa kika rabu dashi?!" Ammi ta karasa maganar tana kuka tana dukanta ta ko ina.

Huda itama tana kuka ta kwace kanta daga dukan da Ammi take mata tace "Na gaji Ammi! Ku kyaleni! Ko meye zaku ce bazan taba yarda ba, don nasan kudi sunfi komai muhimanci, sunfi mun komai a rayuwar nan!"

Ammi ta dafe kirjinta dake mata mahaukacin bugu, muryarta na rawa tace " ban taba tunanin a rayuwata zanyi haihuwar dana sani ba, Huda ina dana sanin kawo mutum mai bakar hali irinki duniya! Huda kinada bakar zuciya, kinada kishi. Na rasa yanda zanyi na fahimtar dake ki gane cewa rayuwa ba haka take ba..."

tana cikin maganar numfashinta ya soma fita sama sama, idanunta suka kage.

Cikin sauri Huda ta karaso ta kamata tana fadin "Ammi! Ammi!!..."

Amma inaaa, Ammi bata nan ta rigada ta fita daga hayacinta. Sulalewa tayi kasa a sume.

Wani irin razananen kara Huda ta sake tana girgizata tana fadin "Dan Allah Ammi kiyi hakuri ki tashi, wlh na tuba ki yafeni! Bazan sake ba. Wayyo Allah Ammina dan Allah ki tashi". Sai faman girgiza ta takeyi amma Ammi ko motsi batayi.

A rude ta mike ta fito parlour taje ta dauko wayarta, jikinta na bari ta soma neman Ashraf a layi.

Sai dayayi ringing sau uku tukuna aka daga.

Muryanta na rawa ta soma fadin "Ashraf dan Allah kayi hakuri nasan yanzu ba lokacin daya kamata na kiraka bane amma ina bukatan taimakon ka".

Muryar da batayi kama dana Ashraf bane ta soma ji ana fadin"Huda..Huda saurareni kiji, ba Ashraf bane. Muhseen ne".

"Muhseen ina Ashraf? Dan Allah ka bashi wayar".

Muhseen yace "Ashraf baya nan yana asibiti an kirashi emergency kuma ya manta da wayarsa a gida. Meke faruwa ne Huda? Ya naji muryarki haka?"

Cikin muryar kuka ta soma mishi bayani tana fadin "Muhseen Ammi ce babu lafiya gata nan ta fadi a sume. Dan Allah Kuzo ku taimaka mun kar na rasa ta".

"Subhanallah! Hold on Huda, please ki daina kuka ya isa haka, yanzu zansa a turo da ambulance nima gani nan tafe. Zan sanar da Ashraf, Just hold on please".

Yana gama fadin haka ya katse kiran, a rude ta koma cikin daki.

Already makwabta sun soma shigowa saboda ihunta da akaji. Anty Rakata ce akan gaba, tana shigowa taga yanayin Ammi, a guje ta koma cikin gida ta dawo hannunta rike da cup na ruwa tana kokarin watsa mata tana sallati.

Ba jima ba sai ga Ammabuwa itama ta shigo, tana ganin mutane a cikin gidan hankalinta ya soma tashi nan take ta gano babu lafiya.

A guje ta karaso ciki ta tadda Ammi da Anty Rakata da wasu mata suna kokarin daga Ammi.

Wani irin ihu Ammabuwa ta sake ta fada kasa tana ruko ammi tana tambayar Huda abunda ya sameta.

Huda na kuka tace "wlh ya'ya Ammabuwa bansan meya sameta ba, kilan jininta ne ya sake haurawa don lafiyanta lau dazu, amma nayi waya yanzu za'a kawo mana ambulance a kaita asibiti".

Anty Rakata ta katseta tace "kusa hannu mu daurata kan gado".

Haka gabadayansu suka sa hannu aka kamo Ammi aka daurata akan gado.

Gabadaya kowa hankalinsa a tashe yake, Huda kuka, Ammabuwa kuka.

🔥Huda🔥💄Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora