Chapter Sixty - one

185 19 4
                                    

Maganganun Ashraf ba karamin kona mata rai sukayi ba don haka cikin sauri tazo tasha gabansa tana fadin "karyanka wlh Ashraf, it's obvious ka kasa mantawa dani. Kuma nasan bazaka taba iya cireni a ranka ba".

Wani irin kallo Ashraf ya watsa mata sa'anan yace "kin cika ji da kanki Huda, you're so arrogant and full of yourself. Yanzu ke a tunaninki bazan iya mantawa dake bane ko meye?"

Zatayi magana ya daga mata hannu yace "ban hanya na wuce. Yanzu ma zan bar gidan, don ganin ki a wanan gidan ya kara bata mun mood dina, kuma daga yau ban fatan wani abu ya kara hadani dake ko yasa na sake cin karo dake a rayuwata".

Wani irin dariya ta sake sa'anan tace "Ashraf kenan, ai nima ban kaunar na kara ganinka, kuma sa ido kayi kallo nan bada jimawa ba zaka samu labarin cewa nayi aure, kuma hadaden namijin daya ansa sunansa namiji zan aura!".

Murmushi kawai Ashraf yayi ya girgiza kai yace "amma ina tausaya mishi wlh, nidai shawara daya zan baki. Karki nuna masa maitan son kudinki a filli don haka zai iya sa yaja baya dake".

Matsawa baya tayi ta soma wani irin juyi a gabansa tana karkada masa jikinta sa'anan tace "in case bakayi noticing ba Ashraf, ni dinan da kake gani full package ce, babu namijin da zai gani bai kyasa ba, ba'a haife namijin da zai ganni ya iya resisting dina ba. At anytime zan iya samun namiji mai kyau, mai kudi da zai iya kula dani ba matsiyaci irinka ba."

Tsaki ta buga masa ta juya zata tafi, juyawan da zatayi taci karo da Muhseen wanda shima ya fito kenan yana nemansu.

Matsawa baya tayi ta soma bashi hakuri tana fadin "Yi hakuri Muhseen, banga fitowan ka bane". Tana gama fadin haka ta juyo ta kalli Ashraf wanda yake tsaye yana binsu da kallo, wani irin shu'umin murmushi ta sakar masa ta da'ga masa gira daya tana nuna masa Muhseen da gefen ido.

Kura mata ido Ashraf yayi yana kokarin ya fahimce abunda take nufi.

Shikam Muhseen bai san wainan da ake toyawa ba yace"Summy ce tace nazo na dubo ku, lafiya dai ko?"

Huda tace "lafiya na da'an fito shan iska ne. Amma na kusan tafiya yanzu don dare ya rigada yayi". Ta fada sa'anan ta karasa ciki.

Muhseen ne ya juyo yana duban Ashraf yace " ko zaka dauki motata ne ka kaita gida".

Ashraf yace "akan me? babu inda zani, ai bani na kawota ba".

*******************

Bangarensu Ammi kuwa, Ammabuwa ta hada musu abunda zasu ci na dare suka zauna a parlour suna ci.

Tuwon shinkafa ne da miyar alayahu wanda yaji kifi.

Ammabuwa ta dubi Ammi tace " Ammi nasan Anty Rakata tanada surutu da gulma da sauransu amma wani sa'in tanada gaskiyanta".

Ammi ta dakatar da abunda takeyi ta dago tana duban Ammabuwa tace "me kuma ta fada yanzu?"

"Wai tana tunanin akwai abunda ya faru tsakanin Huda da Ashraf".

Ran Ammi ne ya bacce tace "wai wanan wace irin mata ce haka?! Ta cika gulma walahi!"

Shiru Ammabuwa tayi bata ce komai ba, Ammi ta sake ajiyar zuciya tace "da gaske ne, Huda da Ashraf sun rabu.

Cizan lebanta na kasa Ammabuwa tayi cike da jimmami da jin haushin yar' uwar nata tace " yanzu mai bawan Allahn nan ya yiwa Huda fisabilillah".

Ammi tace "yar'uwar taki ne sai a hankali Ammabuwa, bata jin magana kwata kwata, ban san ina takeso ta jefa rayuwarta ba. yanzu dai karki sake ce mata komai. Tunda ta nace bata sonshi kuma ta rabu dashi, Allah yasa hakan shine yafi zama alkair. Addu'a kawai zamu cigaba dayi har Allah yasa ta dawo kan hanya".

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora