Chapter twenty-four

260 24 0
                                    

Summy sallama tayi ta shiga parlourn daddy, nan ta tadda shi zaune yayi shiru yana nazari.

Daddy dagowa yayi ya ansa sallamar diyarsa, ita kuma ta nemi wuri ta zauna tana fadin "daddy gani, Nani tace kana kirana".

Daddy ya dan nesa sa'anan yace "eh daman akwai wata magana da nakeso ne muyi dake. Kuma ba komai bane illa batun maganarki da yaron nan Muhseen. Jiya na samu ganin kawun nasa Alhaji Sufyan, kuma mun dan tatauna dashi. Amma sai naga kamar maganar da kawun nashi ya fada mun yasha banban da wanda ya fada mun".

Gaban Summy ne ya fadi ta dago tana duban mahaifin nata tace "maganar me kukayi daddy?"

Yace mun akwai wani company da suke so su bude a can kasar Japan kuma inajin Muhseen din zai koma can da zama don ya kula da company din".

Gaban Summy ne ya kara wani irin mumunar faduwa.

Daddy ya cigaba da fadin "kuma na tabbata shi Muhseen din bai sanar dake hakan ba. ko kunyi wanan maganar dashi?"

Summy ta girgiza kai tace "a'a daddy".

"Toh kin ganni. Nifa bana son irin wanan rudanin, idan yasan bai shirya ba ni bana san wani boye boye ko wasa da hankali. Ya fito filli ya fada. Don ni naga kamar shi kawun nasa ma kamar baya sonki tare da Muhseen din sai faman yimun tambayoyi yakeyi game da matsalar kafarki wanda ni kuma ban aminta ba. kema kinsan when it comes to that issue I don't take it likely with anybody!" Daddy ya karasa maganar cike da dagin murya.

Summy matsowa tayi kusa dashi ta soma kokarin kwantar masa da hankali tana fadin "Daddy nasan halin Muhseen, kilan yana jiran lokaci ne yayi tukuna kafun ya sanar dani. Kuma batun kawun nasa ina jin so yake ya kara fahimtar abunda yake damuna da kuma matsalar kafa da nake fama dashi. Banga laifinsa ba daddy".

"Keh kinji irin tambayoyin da yake mun ne kuwa, gaskiya ni bazan yarda da irin wanan ba, shi kuma Muhseen din da kike kokarin karewa, wani irin lokaci yake jira?! This is quite important, ai ya kamata ya sanar dake in har kina cikin lissafin sa!"

Summy ta kwantar da kai tace "Daddy kayi hakuri, zamu tatauna dashi akan wanan issue din. Insha Allah komai zai tafi daidai kamar yanda ake so".

Daddy ya sake ajiyar zuciya ya soma magana a hankali "Summayya kinga ke kadai ce Allah ya mallaka mun a duniya,  I don't want anybody to hurt you, kuma duk mai shirin yaga ya bata miki bazamu taba shiri dashi ba".

Summy murmushi ta dan sake sa'anan tace "Daddy ka kwantar da hankalinka insha Allah babu abunda zai faru, don na tabbata Muhseen bazai taba yin abunda zai bata mun ba".

Daddy yace "toh shikenan, amma dai kiyi taka tsantsan, you have to be very careful princess. Don't trust too easily don kawai kinji kina son mutum".

Summy ta danyi shiru sa'anan ta dago tana duban daddy tace "Daddy.....wai meyasa kake tunanin babu wanda zai iya sona saboda lalurar kafata?"

Daddy murmushi ya dan sake sa'anan yace "Princess kenan, ba haka bane. kema kin san duk duniyan nan wanda zai zo yace yana sonki a bayana yake. Kuma kullum addu'a nakeyi Allah ya baki wanda zai kula dake kuma ya soki tskani da Allah ba dan wani abu ba".

Summy murmushi ta Sake tace " Ameen ya rabb Daddy, nagode sosai Allah ya bar mun kai".

Daddy ya ansa da "Ameen".

Summy tace "Daddy daman yanzu mukeso muje school Nida Huda akwai dinner da department dinmu sukayi organising."

Daddy yace "toh shikenan babu matsala amma ku tabbatar kun dawo gida da wuri".

Toh daddy insha Allah bazamu jima ba".  Summy ta fada ta mike, sa'anan ta fita daga parlourn, ta haura sama zuwa dakinta.

Tana shiga ciki ta tadda Huda har ta gama shiri ita take jira.

🔥Huda🔥💄Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt