Chapter seventy- seven

132 19 0
                                    

Cikin sauri Muhseen ya juya yana jin yanda zuciyarsa ke masa matsanancin bugu ya bata ansa da "idan pressure ya mun yawa nakan so na kasance ni kadai to avoid interruptions kuma bana bukatan  kowa a kusa dani".

Tana jin ya fadi haka ta dauko jakarta hade da fadin "toh tunda haka ne bari na barka. You need time to yourself" ta karasa maganar hade da mikewa.

"Nooo...please you don't have to. Kiyi zamanki" Muhseen ya fada yana karasowa inda take.

Hannu tasa cikin jakarta ta ciro wasu files ta mika mishi tana fadin "daman waenan documents din na kawo maka, dazun mommy tazo office bata taddaka ba, shine nace bari na kawo maka. I think it's concerning your wedding".

Karban documents din yayi daga hannunta yayi mata godiya ya ajiye su kan table sa'anan ya juyo yana dubanta. Irin kallon da take binsa dashi yasa yaji gabadaya jikinsa ya mutu. Cizon full lips dinta na kasa tayi tace "toh sai anjima kenan Muhseen ni zan wuce".

Muhseen dayake a rikice yake bai san sanda ya furta "kiyi zamanki mana, akwai inda zaki ne? Kodai wani na jiranki ne?"

Dariya ta da'an sake tana shafo wuyanta tace "a'a. Kawai ina sauri ne kar nayi dare kuma aikin da Ammi ta sani zanje na kammala mata".

"Oh okay toh shikenan. Ki gaishe mun da ita".

"Zata ji" ta fada masa.

Shiru sukayi suna kallon juna, Huda na kallon yanayinsa taga duk yabi ya rikice wani irin farin ciki ta dinga ji can kasan ranta because her plan is working. Muhseen kam sai faman kokuwa yake da zuciyarsa yana jin yanda take kara matsanancin bugu akan kyakyawar yarinyar dake tsaye gabansa.

Gani yayi ta soma matsowa har tazo ta tsaya gabansa tana kallon cikin kwayar idanunsa muryanta kasa kasa tace " zaka shigo office ne gobe?"

"yess.. insha Allah zan shigo" taji ya bata ansa muryansa na da'an rawa.

"Toh Allah ya kaimu" tana gama fadin haka, ta wuce shi har jikinta na gogan nashi bata jira taji me zaice ba ta fice daga parlourn. Wani irin iska mai zafi Muhseen ya fuzar daga bakinsa ya dafe kirjinsa dake masa bugun pat!..pat! Tamkar zata huda kirjinsa ta fito. Zufa ne ya soma keto masa ta ko ina ya soma furta kalmar innalillahi wa inna illairaji'un.

Bangaren Alhaji Safwan kuwa, suna dawowa gida shida da'ansa Jubril suka karasa cikin parlourn hade da sallama kowa ransa a bace. Musamman Alhaji Safwwn da yake ganin zamansa a kano bazai cigaba da yuwa ba saboda ganin su Ashraf a garin. Yana gudun kar asirinsa ya tonu. Matarsa maimuna dake zaune a parlour tare da Amal suna kallon tasha a tv ne suka ansa sallamar.

"Oyoyo daddy" Amal ta fada hade da mikewa taje ta fada jikinshi tana murna.

"Sannu da zuwa Alhaji" Maimuna ta fada itama ta mike ta karasa inda yake tana mishi sannu da zuwa.

Jubril yana tsaye ta wajen kofar shigowa bai karaso ba don ranshi a matukar bacce yake akan yanda mahaifinsa ya dinga yi, tunda suka hadu bai samu rest of mind ba sai faman fada yake masa. Shiyasa shi yafi gwamacewa ma yayi zaman sa a Lagos..

Alhaji Safwan yana zama ya dubi matarsa yace "ku shirya jibi zamu tafi Dubai"

"Dubai kuma?" Dukaninsu suka fada a tare.

"Haba Daddy... me kuma zamuje yi a Dubai bayan ga aiki a kasa". Jubril ya tamabayeshi cike da damuwa.

"Alhaji lfy zamu tafi cikin gagawa haka?" Maimuna itama ta tambaya suna bin Alhaji Safwan da kallon mamaki banda Amal data soma murna tana tsalle don ita daman uwar son yawo ce.

Ran Alhaji safwan ne ya soma bacci a fusace yace "kunga idan bazaku ba sai ku fada mun na tattara inawa na koma inda na fito. Haba! banida right nace zan fita na kebe da iyalina, daga ke har da'nki sai kun mun gaddama?!"

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora