Chapter One

1.5K 91 1
                                    

Huda zaune take a gaban karamin mudubin dake cikin dakinsu tana kare wa kanta kallo. Kyakyawar Fuskarta dauke da makeup, sanye take cikin wata haddadiyar green lace, dinkin ya kama jikinta sosai kuma ya bayyanar da shape dinta. Farar fatar jikinta sai shekki takeyi tsabar kulawan datake bawa kanta.

Tsuke karamin bakinta tayi a gaban mudubin tana kara shafawa lips dinta janbaki, sa'anan ta janyo jakarta inda take zuba gwalagwalanta ta dauko tsarka da yankunne ta sanya. Turaruka kalla kalla da suke zube a gaban mirror ta dauko ta fara bin lafiyar jikinta dashi.

Tana cikin haka yayar ta Ammabuwa tayi sallama ta shigo dakin hannun ta rike da kayan wankin data kwaso daga igiyan shanya. Daman ko wani weekend take zama ta wanke kayan data je aiki dasu cikin sati.

Huda ta ansa sallamar ta cigaba da abun da takeyi. Bayan Ammabuwa ta zube kayan akan gado ta juyo tana duban huda dake kokarin saka takalmi allamun fita zatayi.

"Huda ina zakije haka?" Ta tambayeta. Yatsine fuska huda tayi kamar bata son magana sa'anan tace "dazu su asta suka kirani a waya wai an mana fixing lectures, kuma lecturer din yace zaiyi attendance."

"Shine kika ci wanan uwar kwaliyyar kama zakije wani biki ko party? Huda ina hanaki akan irin waenan shigan da kikeyi. Kullum nida ammi nasihar mu kenan gareki amma ke kwata kwata baki jin magana. Allah yayi ke mai taurin kai ce. Kina jin kanki keh big girl ko kin faso gari toh Kar ki bi duniya a hankali Kuma kada ki bar kanki inda Allah ya ajiyeki koh, kiyi ta bin kawayen banza suna hure miki kunne. Kullum ina kara tunnasar miki da rayuwa juyi juyi ce baza mu dawwama a haka ba huda, in kika kwantar da hankalin ki wata rana komai zai zama tarihi."

Ai tunda Ammabuwa ta bude baki ta fara mata fada, huda tayi kicin kicin da fuska ta bata rai kamar hadari ya taso. Ita arayuwarta bata son irin sa'idon da yayyarta take mata. Kullum sai ta sata a gaba tana mata irin waenan surutun. Wai dole ne? Rayuwarta ce ai a barta ta sakata ta wala, lokacin ta ne.

"Nidai gaskiya yaya ammabuwa kina takuramun fa dayawa, haba kullum sai nayi abun magana agidan nan, bana taba abun arziki, yanzu dan kwaliyyan nan ma danayi ya zama wani aibu?" Ta fada maganar ciki ciki tana turo baki cike da fitsara.

" ni kike fadawa wa haka huda, rashin kunyar da kika saba zaki min yanzu? wallahi yau zan sassaba miki a gidan nan sai dai ki fasa zuwa lecture din. Jimin shegiyar yarinya ana kokarin gyara rayuwarki ta dawo kan hanya kullum sai kara tuburburewa kike. Kullum so kike kiga ammi tana zubda hawaye a kanki?".

Suna cikin haka ammi dake tsakar gida taji hayaniyar su ta shigo dakin da sauri da taddasu. Tana tambayar ammabuwa meke faruwa.
" duba yar ki ammi, duba shigar datayi wai haka zata tafi makaranta fissabillillah. Ammabuwa ta fada tana nuna Huda. "Ammi na gaji da yiwa yarinyar nan fada, inta kaini bango wlh dukan tsiya zanyi mata a gidan nan".

Ammi ce ta juyo ta kalli huda wace take ta cika tana batsewa ita a dole an takura mata a gidan. Kayan da ke sanye jikinta ammi ta bi da kallo "sa'anan tace ke dauko hijab ki saka kafin ki bar gidanan"
Huda zatayi musu ammi ta daga mata hannu allamun bata son jin wata magana . Cikin  jin haushi da kunnar rai Huda ta janyo jakarta ta ciro hijab ta sanya badon taso ba ta dauki jakar makantar tayi fuuuu ta fice daga dakin ko sallama bata musu ba haka ta bar gidan.
Ammi da ammabuwa suka bita da kallon takaici da addu'an shiriya. Don inda sabo sun saba gani ira iren haka daga huda. Ammi kuwa zuciyarta radadi takeyi akan  irin rayuwar da yarta ta jefa kanta ciki tasan ba irin tarbiyan data bawa yayanta ba kenan. Kwata kwata huda ta fita zakka. Ga yayyarta ammabuwa babu ruwanta ga addini kuma tasan ya kamata duka duka shekara uku ammabuwa tabawa huda don yanzu akkala huda ta kai shekara ashirin da biyu a duniya. Ita kuma Ammabuwa shekararta ashirin da biyar. Su biyu ne kadai suka rage mata a duniya.

Wacece Huda?
Huda da Yayarta Ammabuwa gaba da bayansu shuwa arab ne. Mahaifinsu mallam Grema kamsallem mutumin maiduguri ne, neman na halal ya kawo shi garin lagos. Tun dayazo ya fara dan buga buga daya dan samu canji  ya koma maiduguri ya auro ammi ya kawota nan agege dake cikin garin lagos. Hakka ammi ta dinga zaman hakuri dashi don wani sai'in sai su yini babu abun da zasu ci a gidan nan. Sai ya fita ya nema ya kawo tukuna zasu samu abunda zasu ci. Suna cikin zaman wanan kuncin ammi ta haifo diyarta mace aka sa mata suna Ammabuwa. Ammabuwa ta taso cikin wuya da wahala don ko kayan arziki ba iya sa mata, har talla ammi ke dauro mata taje ta dawo don dai su samu abun da zasu ci. Gashi ammabuwa akwai farin jini kasancewarta kyakyawar yarinya gata da ladabi da biyyaya kowa na santa a unguwansu har yan kyauta tana samu daga wurin mutane. Ammabuwa bata fara makaranta ba sai data kai shekara biyar alokacin ammi ta sake haifar wata diya mace aka rada mata suna Aminatu Beine amma sai suke kiranta da huda saboda sunan mahaifiyar ammi data ci. Ranar sunan huda kuwa mutane har zuwa kallon babyn sukeyi saboda tsananin kyawunta. Kamar balarabiya sak, kuma kamar su daya da ammi.
Itama huda haka ta fada layi aka cigaba da gwagwarmayar rayuwa da ita.
Huda na shekara goma shabiyar lokacin tana SS2 ita kuma Ammabuwa zata zana waec dinta kenan don dukkansu makarantar gwamnati suke zuwa.

🔥Huda🔥💄Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz