Chapter Eighty- five

176 15 0
                                    

Hakuri Huda ta shiga bawa Ammi ganin ranta ya bace sosai tace "Ammi dan Allah kiyi hakuri wlh ba haka nake nufi ba. Ina fa'din haka ne saboda nasan irin mutanen da zaku tarar a ciki, masu kud'in nan ba mutunci bane garesu yanzun nan sai su soma maka kallon kaskanci idan sun gano kai ba irinsu bane. Ni kuma bazan iya juriyar ayi muku wulakanci ba Ammi".

Ammi wace ranta yayi mugun mugun bacci bata saurareta ba ta shiga yi mata fa'ada sosai ta inda take shiga ba tanan take fita ba tace idan batayi hankali ba zatayi mugun saba mata a wajen.

Huda ta cigaba da bata hakuri tace wlh ba haka take nufi ba, kawai dai tana son su kiyaye ne saboda irin mutanen da zasu tarar ciki.

Ammabuwa ta ta'be baki tace "Allah yasa hakan ne, Ammi zo mu tafi". Haka suka karasa ciki ko ina fess yasha gyara. A cikin gidan akayi da'an decoration ga mutane sosai an halarci wurin. Summy na ganinsu cike da farin ciki ta karaso tazo ta tarbe su, tayi kyau sosai na dinkin farin material gown yasha ratsin black flowers da head baki data daura fuskarta tasha makeup sai faman daukan ido takeyi. A hankali ta karasa dasu inda su Mommyn Muhseen suke suka soma gaisawa ta kira nani tace ga mahaifiyar Huda tazo su gaisa. Da da farko Nani tayi shakan zuwa don tana tunanin duk halinsu da'ya da Hudan. Amma sai tazo taga sabanin haka, don Ammi da Ammabuwa cike da fara'a suka gaisa da ita, Nani taji da'di sosai yanda taga Ammabuwa na magana cike da kunya da tsantsar girmamawa yasa taji ta shiga ranta faral da'ya. Tare suka karasa ta nema musu wurin zama suka zauna. Huda kam tun shigowarsu ta kama hanyarta ta shiga cikin sauran kawaye. Ammabuwa sai faman waige waige take ko zata ga shigowan Mahmud amma taji shiru, ko giftawan shi bata gani ba hankalinta yayi mugun mugun tashi.

Huda can baya taje ta ciro wayarta ta soma neman layin Muhseen amma bata sameshi hankalinta ya da'ga, tasan bazai halarci wanan taron ba saboda na mata ne kawai amma still tana son taji daga gareshi. Tana cikin haka sai ga Halima nan tazo nemanta tazo ta tayasu da da'an wani abu, haka ta mike ta bita tunani kala kala na mata yawo aka.
Ammabuwa sai bayan 20 minutes taga shigowar Mahmud yaje yayi parking sa'anan ya fito da wasu kayaki a hannu ya shige cikin sauri, jiki na bari ta mike tace ma Ammi tana zuwa. Ammi tace mata toh.

Can gefe ta ganshi yana tsaye yana magana da nani taga ya mika mata kayan daya ruko, taja ta tsaya kirjita na harbawa tana jiran ya gama magana da Nani tukuna ta karasa. Tana ganin sun gama magana ta karasa cikin sauri tana kiran sunansa, Mahmud ya waigo ya ganta yaji yanda kirjinsa ke tsananta bugu, amma kallo da'ya yayi mata ya dauke kai.

"Mahmud dan Allah ka tsaya ka saurareni mana. Please". Ta fa'da tana marairace masa fuska tamkar zatayi kuka.

A hankali ya juyo yana dubanta da fararen idanunsa masu tsuma rai, fuskarsa a daure yace mata "Ammabuwa kinga dai ina kan aiki nane yanzu. Banida lokacin magana, dan Allah ki sarara mun".
Yana gama fa'din haka ya juya yayi waje.

Hankali a da'ge ta kuma bin bayansa tana fa'din "Mahmud ka yiwa Allah ka tsaya ka saurareni nasan duk saboda Abdul ne kake mun haka, nasan ka ganmu ranan tare..."

"Ni ban tambayeki wanan ba. Bance kiyi mun bayanin komai ba! Kina iya ganin duk samarin da suke unguwanku ma I don't care, rayuwarki ce kije kiyi duk yanda kikaga dama Ammabuwa!"

"Mahmud wai meyasa kake mun haka ne?! Na gaya maka babu komai tsakanina da Abdul, Fitan da mukayi dashi a ranar, nayi hakan ne don na fada mishi bazamu cigaba da ganin juna ba, saboda zuciyata ta rigada ta gama amincewa kai take so.Kaine wanda zuciyata take muradi. Dan Allah ka yarda dani Mahmud." Ta karsa maganar hawaye na zubo mata.

Ganin tana zubda hawaye ne yasa ya dan sauko hade da matsowa inda take ya kira sunanta a hankali "Ammabuwa.... da gaske kike kina sona ni kadai ne a zuciyarki?"

"Yess kai kadai ne Mahmud" ta fa'da tana da'an sakar masa murmushi still hawaye na gangaro mata.

Wani irin farin ciki ne yaji ya lulubeshi yace "koda na kasance ni direba ne, talaka kuma banida kudi? Kin amince zaki kasance tare dani".

🔥Huda🔥💄Où les histoires vivent. Découvrez maintenant