Part 1

351 21 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Nafeesat jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=106249334371950&substory_index=0&id=106248871038663&sfnsn=mo

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*EPISODE* (1)

'Yanmata ne su biyu da shekarunsu be gaxa 24years ba, suna xaune a tamfatsetsen Palo da yagaji da haduwa cikin luntsuma-luntsuman kujerun da aka qawata Palon dasu, sun hade Kansu sai latse-latsen waya suke, ihun da sukayi ne yasaka wata matashiyar yarinya da bata haura 19years ba tafito daga dakinta da gudu tana tambayansu lafiya? Bayan data xauna akan hannun kujeran dasuke, wacce ke riqe da wayan CE tamiqa mata cikin xumudi take fadin

Da Allah Ihsan duba kiga wadannan akwatunan sunyi matuqar kyau wlh, su nakeson sweety yamin gaskiya na FASA wadancan da nata6a nuna masa

Ta6e baki Ihsan tayi bayan tagama gani tamiqa mata wayan tana cewa

Ke dai aunty Nafeesa baki da aiki sai ganin abubuwa a social media kina cewa shi yaya xaimiki, duk da laifin Momy ma datake biye miki, ita kuma aunty Baseera tana xugaki shi kuma yaya yana biyewa shirmenki

Hararanta Nafeesa tayi tace

Wato shirme nakeyi ko Ihsan? To laifi ne Dan na xa6i abinda nakeso asakamin? Yanxu fa mun shigo xamanin wayewa ne ba gidadanci ba?

Ke dalla kyaleta 'yar baqin ciki CE wannan yarinyan, in kika biyeta zata maidake sakara CE, in baxata iya gani ba ta6ace anan wajen

Baseera take fadin hakan.. 'Dage kafada Ihsan tayi tana ta6e baki tamiqe takoma kan 3sitter dake nesa dasu kadan takwanta tare da mayarda earphone din dake rataye saman wuyanta cikin kunnuwanta tana latsa waya.. Wayan Nafeesa CE yasoma ringing, murmushi tayi bayan taduba me kiran tace

Kinga dan halak din yaqi ambato

Amsa call din tayi takanga akunni tana ci gaba da murmusawa lokacin datake fadin

Sweety yanxu nake tunaninka araina fa sai gashi kakira

Kyakykyawan murmushinsa me qara masa kyau da kwarjini yayi yana juyawa akan kujeran dayake, cike da nishadi yace

Allah ko Nafee na? But baki kiran ba har nariga ki?

Yafada yana lumshe fararen idanuwansa

Uhm yanxu nakeson fa kiranka, wayan ma na hannuna kakira

Tafada tana sakin murmushi qasa-qasa

I know! that's why naji ajikina, kina gida ne ko school?

Ina gida sweetyna, yaushe xaka dawo?

Maybe sai dare, xan raka Haidar duba kayanSa da'aka sauke mishi ne, kinason ganina ne?

Yaqare maganan yana kwantar da kanshi jikin kujeran.. Dariya tasaki me sauti tace

Akwai labari ne but sai kadawo

Okey kikulamin da kanki bye 👋

Aje wayan yayi saman table yana murmushi tare da kallon Haidar da yabuga tagumi yana  sauraronshi.. Gira daya yad'age 😉

Lafiya? Wannan kallon fa?

Ajiyan heart Haidar yasaki yacire tagumin dayayi yace

Ai Kaine kaxama abin kallo dole nakalle ka, mamaki wlh kake bani kamar ba kai bane kake cewa Momy ta liqa maka jaraba, but now kajone kunata xuba love har da saka rana

Ya son ranka? Kuma nan da one month asha biki ba

Al'ameen yafada yana miqewa tare da miiqa yana yarfe hannayensa

Kai 'Dansa ido tashi muje naraka ka, ka daiji abinda Nafee na tace "jirana takeyi

Tashi Haidar yayi yana dariyan shaqiyanci yace

Ai da katafi kiran nata, ba sai kanunan kana soyayya ba nasani, nima very soon xan shigo layi ai

Da ka kyautawa kanka kuwa

Cewar Al'ameen yana kad'a keeys dake cikin yatsunsa.. Fita sukayi daga office din suna xantawa..

***

RUGAN TARAU

Ruga CE dake jahar Kaduna cikin qaramar hukuman zaria.. Malam Lawali yana daya daga cikin dattawan garin kuma masani ne akan harkan magunguna na gargajiya, shiyasaka yayi fice cikin qauyen, ba ma iya nan ba har cikin birni ana xuwa amsan magani wajenshi, SBD indai kasha maganinsa to insha Allahu xaka samu sauqi sosai wasu ma sun rabu da ciwon kenan, matarsa daya inna Nafeesa da 'yarsa daya Nafeesa suna kiranta da Ummee kasancewar sunan Innanta taci, kafin haihuwar Ummee Inna Nafee tayi haihuwa dayawa 'ya'yan na mutuwa, daga an haifesu xasu mutu wasu ma tun daga ciki take 6arinsu, duk wani taimako da Baffa Lawali xai mata yayi but Abu yacitura, har saida tayi haihuwa takwas ana taran ne aka haifi Ummee, kuma tun daga haihuwarta Inna Nafee take ciwon ciki, kwanan Ummee biyar Inna Nafee tace ga garinkunan, mutuwan ya girgixa Baffa Lawali Sosai, mutuwan da suka daura akan Ummee sai gashi uwar Ummeen CE tamutu, shiyasa tataso cikin gata wajen Baffanta, yana matuqar sonta bayason ko quda yata6a ta, SBD ita CE ma yaqi aure har yanxu dan kawai kar matar uba tamuxguna mata

Ummee yarinya CE 'yar shekara 17 aduniya, fara CE Sol doguwa, tanada kaurin jiki da yalwan gashi, da kaganta kaga kyakykyawan bafulatana, tanada xanen uku-uku agefe da gefen fuskarta, macece mai tsananin kunya in nace muku kunya I mean sosai din nan, ga kawaici ga kirki tayi ne tako INA, tayi saukar al'qur'ani a makarantar allo, boko kuwa dama ba'a magananshi sbd ko primary babu aqauyen..

*

Tafiya take cikin sanyinta kanta dauke da tulu, jikinta sanye da kayan saqa na Fulani

Ummee.. Ummee..

qawarta Hajjo CE take ta kwada mata kiran batajiba, sai da har taxo kusa da ita tana sake kiranta kafin taji tadago madaidaitan idanuwanta takallota fuskarta cike da damuwa

Lafiya Ummee naketa kiranki amma bakijiba? Kamar ma ba'a duniyarmu kikeba, mike damunki?

Bud'e baki tayi cikin tsananin damuwa da yanuna a muryanta tace

Hajjo ni kaina banshan meke damuna ba, tun safe nake jina ahaka kuma gabana na fad'i kamar wani abu xai shameni, ga kuma ciwon Baffo dayau yayi tsanani har ba ya iya tashi, yanxu haka ma akwance nabarshi naxo d'ibo ruwa, bamu da ruwa ko d'igo aradu da ban fito na borshi shi kadai ba

Taqarike maganan cikin rawar murya idanuwanta taf da hawaye.. Cike da tausayinta Hajjo tadafata tace

Ayya shannu.. Ashe jikin Baffan ya kai haka? Dan Allah kidaina shoka damuwa aronki nashon ciwon Baffo ne yake shaki damuwa, kiyi haquri kinji qawata insha Allahu xaishamu lafiya dawuri, kigaisheshi kafin naxo nadubashi kinji ko?

Gyad'a kai Ummee tayi tana share hawayen da yafara sauka saman fuskanta tace

Ai banshon xaki d'ibo ruwan ba da na biyo miki, bari najiraki anan kitai kidibo shemu tai tare

A'a kitafi da Allah kinga kinbaro Baffo gida kar yajiki shiru, she naxo gaisheshi

Hajjo tafad'i haka tana tafiya

.

*Hmm in yamuku inason ganin comments.. Wanda keda qorafi ma yasanar dani qofa abude take.. Love ❤ u fans*

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now