Part 34 Aunty Karima

27 3 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

      *EPISODE (34)*
   *(aunty Kharima)*

Ummee CE cikin sauri take harhad'a girkin da tayi cikin basket, tadauko tafito palow ta'ajiye tanufi daki, cikin k'ank'anin lokaci tayi wanka tashirya cikin wani dack milk d'in atamfa da ratsin maroon and black colour, d'inkin riga da zani ne sun bala'in yin mata kyau duk da yanzu ba k'aramin sauyawa tayi ba, in kaganta baza kace itace ba, yanda tayi bala'in k'iba sosai, ga wani irin haske da tak'ara tazama kamar wata zabiya (hmm anya anya? fans me kuka fahimta?) babban gyale tad'auka tayafa bak'i bayan da tasha d'aurin dankwali me kyau, black flate shoes tasaka tad'au wayanta tafito palow, tana d'aukan basket din wayanta yasoma k'ara, peaking tayi tak'ara akunni

"Ya dai kin shirya mu had'u acan ko nazo?"

Tafad'a tana kai kallonta ga agogo dake buga 12:00pm, daga can Ihsan tace

"Ai kawai kitafi matar Yaya, dan yanzu Honey yayimin waya yana kan hanya, zan tsaya tarbansa sai anjima mutaho tare dashi".

6ata fuska Ummee tayi kamar tana ganinta tace

"Amma kikace min sai gobe zai dawo? Gashi yanzu kin saka Yayana yagaji da jirana yatafi sai dai driver zai kaini".

Dariya Ihsan tayi tace

"Afwan matar yaya, ai babban uzuri ne dani ko? Kuma wlh bansan zai dawo ba domin shi yafadamin sai gobe".

Ummee tace "ni dai wlh kin jamin, da tuni yanzu na manta da nakai, k'iri-k'iri nak'i binsa dan naji kince mubari zuwa 12:00pm, amma dai kin ma kanki wlh".

Ihsan dai dariya take tayi tana bata hakuri, batabi takanta ba takashe wayanta tafito tarufe k'ofan, tanufi wajen driver dake faman jiranta tashige suka tafi.

Lokacin da tashiga dakin da Baby ke kwance Mama ce ita kadai, bayan sun gaisa tace

"Ya me jiki? Har yanzu dai bata farka din ba?"

Mama tace "dasauki sai godiyar Allah, tana nan dai yanda take, yanzu mijinku ma yagama dubata yafita".

"Allah sarki Allah yasawake".

Ummee tace hakan cikin tausayawa tana kallon Baby da tazama kamar 'yar shekara Goma, tana sanye cikin light blue din riga da wando na marasa lafiya, idanunta arufe an saka mata oxygen

Mama tace "yanzu wai fa Muhsina nake jira tun dazu tazo tazauna da ita amma shiru kakeji, gashi ko wanka banyi ba, kuma tasan da cewa bana iya yi anan cikin asibitin dole sai nakoma gida har gashi rana tayi, wlh sam na manta na baro wayata agida bare in kirata".

Murmusawa Ummee tayi tace

"To Mama ko zakije ne sai kibarni ni nazauna".

"A'a 'yata tayiwu yau ba jimawa zakiyi ba, kibari dai nasan takusa zuwa yanzu ai, ni bansan irin Muhsina ba wlh wani lokacin shiriritanta yawa ne dashi".

"Mama kiyi mata uzuri k'ila tatsaya yin wani abin ne".

Tace "bakisan halin Muhsina bane, kibarta kawai zatazo tasame ni".

Ummee tace "mama kitafi kawai zan zauna din, dan zan kai dare anan ma".

"To shikenan 'yar nan, Allah yamiki albarka".

Mama tace hakan tana tashi, Ummee ta'amsa da

"Ameen Mama".

A haraban asibiti Mama taci karo da Muhsina tana rik'e da kwando zata shigo, k'arisowa kusa da ita tayi tana washe hak'ora tace

"Kin ganni sai yanzu ko Mama? Wlh ilham ce tazo da wata class mate dinmu muka zauna muna ta hira, kuma sai ga aunty Kharima tazo, shiyasa nace bari inyi musu girki daga nan nataho dashi".

Mama tace "ai yayi miki kyau, ina ita Khariman ko sai anjima zata zo?"

"A'a tare muka taho, tabiya ta gidan aunty Farik'a wai zasu taho tare".

Tace "shikenan kishiga Ummee tana nan wajen Baby".

Daga haka Mama tawuce ita kuma Muhsina tashige ciki.

***

Da yamma Mama da aunty Kharima ce zaune adakin Maman, suna tattauna matsalan Baby

Aunty Kharima tace "ni kam Mama me zai hana ajaraba maganin gargajiya agani? Ni inaga ciwon Baby bana asibiti bane, to abu fa kullum gaba yakeyi ba baya ba, Allah asan abun yi gaskiya, tunda Muhsina tafadamin abinda yafaru da ita jikina yasoma sanyi da lamarin".

Da mamaki Mama tace

"Me yafaru da ita din?".

Nan aunty Kharima tafada mata abinda Muhsina tasanar mata game da Babyn, tsanar da take ma Al'ameen kafin aurensu, jinjina kai Mama tayi

"Lallai kam, ai wannan ba abun 6oyewa bane, gaskiya sunyi wauta, amma insha Allahu bari Babanku yadawo zan fadamishi asan abin yi".

Baba kuwa na dawowa Mama tasanar mishi, be wani musa da shawaranta ba ya amince, dama yana shirin yanda za'ayi afitar da ita k'asan waje ne, don abun yafara damunsa, washe gari Baba yanemi Al'ameen suka tattauna akan ajaraba na gargajiya ko za'a dace, nan Al'ameen ya amince aka samo wani Malami me bada maganin gargajiya, har asibiti yaje yaduba Baby, sannan yabada maganin da za'a rik'a mata amfani dashi, Allah da ikonsa cikin wata daya har sun soma ganin sauyi, Baby bata k'ara sumewa ba, kuma an samu tana d'an cin abinci ba kamar da ba, duk da komi yin mata akeyi bata iya ta6uka komai da kanta.

Nan aunty Kharima tasake samo wani babban Malami anan Zaria, aka d'au Baby aka kaita wajenshi, tun sanda yaganta yagane aljanu ne akanta kuma su suka sanya mata ciwon.

.

_to fa?_ 🤔 _me zai faru?_

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now