🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.Littafi ne da xaixo muku da wani irin salo. Kudai ci gaba da bina dan jin yanda xai kaya.
*EPISODE (5)*
*(Yusuf)Me shagon ne yafito yana niyan kulle shagonshi yaci karo da ita, tabbas ya ganeta yarinyan da daxu tasiya lemu ne.
"Ke ammata lafiya kikaxo nan kika xauna harda buga uban tagumi?".
Mutumin yafada bayan yagama kulle qofan shagon, Kallonshi tayi tasad da kanta qasa tace
"Dan Allah yaya taimako nake nema kataimaka min, ni sunana Baby naxo garin nan ne neman qanin Dadyna Alhaji Bashir isah amma har yanxu na kasa samo gidanshi".
Ikon Allah kuma kin tabbatar anan shiyar yake xaune?.
Ni dai nasan a kaduna yake but bansan wani anguwa yake da xama ba.
Kallonta yake yana naxarinta kafin yace
"Kikace me sunanki?"
Baby..
Sunanki na asali xaki fadamin
Cikin sanyin murya tace
*"NAFEESA"*
Daga wani gari kikaxo kuma ina iyayenki suke?.
Ma tso hawaye tafara yi
"Daga garin Abuja nake, iyayena kuma 6arayi ne suka shiga gidanmu suka kashesu shine ni nasamu dama nagudo, kuma kafin Dadyna yarasu yacemin inwuto kaduna ne wajen uncle Bashir but bansan wani anguwa yake ba".
To ke Nafeesa ya akayi kika manta anguwan da yake?
"Ni bansan anguwan da yake ba, tun ina qarama rabona da nan, ko Mamina xataxo bana biyota"
Ikon Allah yanxu jibeki qatuwar budurwa ace bakisan gidan qanin ubanki ba? Aiko kinyi wauta ynxu wa gari yawaya? Iyayen naki ma har da laifinsu da basu xuwa dake,, yanxu baki da wasu dangin kuma?.
"Ina dasu amma suna Niger kuma can din ma bana xuwa"
Jinjina kanshi yayi yanaci gaba d kallonta, akwai matsala gaskiya dole yataimake ta, baxai yiwu yabar yarinya budurwa kmr wannan tana galaramba agari ba, daga qarshe tahadu d 6ata gari ko tafad'a hannu mara kyau, tunda taimako yaxama jikinsa dole itama yataimaka mata, Allah sarki gskiya tabashi tausayi.. Gyara tsayuwanshi yayi yadubeta dakyau yace
"Sunana Yusuf kuma wancan gidan dake kallon nan shine gidana, inada 'ya'yana biyu da matata Hafsa, inkin yarda xaki bini gidana ni kuma xan taimaka miki, kixauna agidana har lokacin da xakiga uncle din naki, ni kuma insha Allah xan tayaki nemanshi in ba damuwa.
Kyakykyawan murmushinta tayi akaron farko tace
"Nagode yaya Yusuf"
Shima murmusawa yayi