Part 30 Ulcer

33 1 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
_Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah_

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*Wannan shafin naku ne HOME OF QuaLiTie's WRITTer's aSSo, nayi farin ciki dana kasance daya daga cikinku, up up up Allah yaqara taimako yaqara mana baseera baki daya, 🙏🏼🙏🏼🙏🏼Allah yabamu ikon rubuta daidai ameen*

      *EPISODE (30)*
        *(Ulcer)*

Awa daya aka dauka ana duba *Baby* kafin asaka mata drip suka fito, direct office din *Al'ameen* suka nufa, bayan sun xauna *Doctor Gali* yace

"Wai me yafaru da ita ne? Naga daxu mun baro ta lafiya, ko dama bata da lafiya ne?".

"Wlh ban sani ba, tana barci ne dai tashiga wannan yanayin har tasume".

Cewar *Al'ameen* cike da damuwa

"To amma ko dama tana fama da wani lalura ne? Ina nufin kafin ka aure ta?".

Girgixa kai *Al'ameen* yayi

"Gaskiya a'a, bana tunanin tana fama da wani ciwo".

*Doctor Anwar* yace "ni abinda ke bani mamaki bamu gano wani ciwo tattare da itaba in banda *ULCER,* kuma bai wani ci jikinta ba da xata shiga wannan yanayin".

"Nima dai abin na bani mamaki sabida yanda take wani irin rama abin yana dagamin hankali".

*Al'ameen* yafadi hakan

*Doctor Gali* yace

"Bakusan illan Ulcer bane, ba yanda baya yima mutum, yanxu dai yakamata kaqara mata gwaji na musamman sabida agano meke damunta".

"Hakane kam yakamata tun wuri adau mataki tunda be xo mata dasauki ba, wataqil jininta be da qarfi ne".

Inji *Doctor Anwar*

*Al'ameen yace

"Ok insha Allah".

"Allah yabata lafiya, bari inje office inada petient".

*Doctor Anwar* yafadi hakan yana miqewa yayi musu sallama yafita.. tare da *Doctor Gali* suka qara komawa dakin da *Baby* ke kwance, duk wani gwaji sunyi mata result din dai daya ne ba abinda ke damunta illa Ulcer, shima din ba wani sosai bane, office din *Al'ameen* suka koma dan sake tattauna matsalan.

***

Lokacin da *Baby* tafarka taganta saman gado mamaki ne yakamata, ita tasan akan kujera take kwance to me yakawo ta nan? Kuma ba dakinta ba? Dakin tasoma bi da kallo kafin tagane asibiti take, dasauri tatashi xaune tana bin hannunta dake da drip da kallo.

"Me yasame ni ne?".

Tafada afili tana son tuno baya but takasa, cire drip din tayi tamiqe xata fita aka bude qofan, *Al'ameen* ne yashigo yana kallonta itama shi take kallo cike da tuhuma, dasauri yamatso kusa da ita yana fadin

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now