Part 15 Muhsin

53 2 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

      *EPISODE (15)*
       *(Muhsin)*
.

Muhsina tana cikin motanta ita kuma Baby tana cikin na Al'ameen suka tafi, koda suka kai sauketa yayi bai shiga ba yaimata sallama akan xai dawo yatafi.. Su Mama da Baba na xaune da kuma aunty Fariqa dake shayar da d'anta suna hira "saiga Muhsina ta fad'o ckin palon aguje

Mama Baba kuxo kuga Baby wlh bata mutu ba, gatanan na taho da ita.

Lokacin Baby tashigo dukansu suka bita da ido cikin tsananin mamaki, dasauri tanufi Baba tafada jikinsa tana fashewa da kuka, shi kuma ya kasa ko qwaqwqwaran motsi, Mama da Aunty Fariqa da suka tashi tsaye cikin rawar baki Mama tace

"Bab..byy ce wlh, baki mutu ba?"

Ee wlh Mama itace bata mutu ba, ni naxo da ita daga gidan da take xaune.

Cikin kuka itama Babyn tasake tabbatar musu da itace bata mutu ba, nan fa suka hau murna ana rungume-rungumen juna cike da farin ciki, sai da suka nitsa kafin Baby tasoma basu labarin abinda yafaru tun daga kashe mata iyaye da rayuwar da tayi bayan taxo Kaduna da kuma taimakon da Al'ameen yaimata batare da tafad'i soyayyar dake tsakaninsu ba, kowa saida yatausaya mata.

Baba yace "ikon Allah mutum mugun icce, ban ta6a tunanin Anas xai aikata hakan ga yaya ba, domin a washe garin ranan ma shi yakirani yafadamin kunyi gobara muka tafi tare da Walid, to tun dai daga ranan ban sake ganin Anas ba, nayi mamaki matuqa "koda nakira wayansa ma basu shiga, ashe shi ya'aikata wannan d'anyen aikin, to wlh duk inda yake sai nasa ankama shi sai an binciko min shi dole ya girbe abinda yashuka".

Wannan gaskiya ne, Allah dai yakyauta gaba, daman tsintuwan mage ai bata mage, kadubi yanda su yaya suka riqe shi da amana amma ga abinda yasaka musu dashi "wnn ma ai sai kaji tsoron taimakon.

Mama take fadin hakan

Aunty Fariqa tace "wlh kuwa Mama, Allah dai ya isan mana kan wnn axxalumin mutumin, dama gobe yaya Walid xai dawo ai komi xaixo dasauki, nasan nan da nan xasu kamo shege".

Ai maganin shege karen maguxawa  anty, in yafada hannun yaya sai ya cinye namanshi d'anye.

Cewar Muhsina

Mama tace "to ya isa hka, tashi Baby kuje daki ko kya huta".

Hakane Maama tashi kije ki kwanta kihuta kar kuma ki biyema surutun Muhsina, ke kuma Fariqa ki kirawo Karima kisanar da ita.

To Baba.

Cewar Fariqa tana daukan waya..

Baby kenan, kinga yanda kika koma duk kinbi kin qara qarmashewa? Gaskiya Hafsa ta iya kiwo, xanso inga yanda take horaki, waii wa yaga Baby.

Muhsina take fadin hakan lokacin da suka shiga dakinta sai kyalkyala dariya takeyi.. Baby da tasami wuri kan sofan dake dakin taxauna tana hararanta tace

"Ni banson iskanci Sina kinsan dai halina ynxu sai in xane miki jiki".

Dariya Muhsina takwashe dashi tana nunata da hannu

Ahakan ne xaki xane ni? Uhm yanxu fa ba da bane ko bakiga yanda Hafsa takomar dake kmr xabori bane?

Amma dai kinsan koda goma talalace tafi biyar albarka, kafin kifito duniya saida nagama shan iskan duniyan, aqalla nabaki shekara daya da watanni, so kibini ahankali ni ce dai ban sanja ba.

Muhsina tace uhm wannan kuma sai dai kifada ma Muhsin shine dai baxai manta halinki ba.

Allah sarki my lovly brother! Kinma tuna min shi, wai ina yaje ne banji motsin shiba?

Baby tatambaye ta

Muhsin na Zaria gidan aunty Karima, kinsan yana neman addmission a  ABU Zaria can xai xauna.

Wow 🙊 Muhsin din? Kice ya girma haka? Duka yaushe ma aka haifeshi har yakai matakin nan?

Au tambaya kikeyi? Lallai ne ma Baby kin cika 'yar rainin wayau wlh, to kibari inkin ganshi saiki gaxgata ya girma ko kuwa? Mutumin da ko aure akai mishi xai xauna da mata.

Dariya Baby tasaki har da tafa hannu

Amma gaskiya Sina ke 'yar iska ce, Muhsin din da bai wuce 17years ba kice ya isa aure?

Ah to ai naga kece da rainin hankali, that's why nafadi hakan.

Ok to kiramin shi mugaisa.

Baby tace hakan

Ai dama kin haqura sabida gobe nasan anty Karima xataxo kuma qafarshi kaqarta sai ya biyota "sai dai inba shi ba, "bari dai inkira miki shi.

Wayanta Muhsina tadauka takirashi, ringing biyu yadauka

Ya akayi ne 'yar qanwata?

Muhsin yace yana dariya qasa-qasa... Tsaki Muhsina tayi

Wlh Muhsin xanci ubanka, wai ni ba yayarka bace duk kabi ka raina ni?

To aike baki saniba, duk girman mace namiji shine uba gareta kuma shine yaya, dan haka saiki hakura ki amsa ahaka, Allah ne yabani girman.

Yafad'a yana sheqewa da dariyan raini

To xan kashe in ka gama iskancin naka sai kaimin magana, kuma dama albishir xan baka to na fasa kaje aunty Karima tasanar maka.

Saurin gimtse dariyansa yayi yace

"Haba 'yar uwa rabin jiki kiyi haquri kisanar dani, kinsan bana gida yanxu ina filin kwallo, kuma kafin inkoma hankalina ya tashi sai hawan ruwana yamotsa sabida tunanin abinda xa'a sanar min".

Kasan Baby ta dawo bata rasu ba?

Wacce Babyn kuma?

Wace Babyn kasan muna dashi? Babyn Dadyn Abuja "ashe ba da ita gobaran yaci ba, ga ma ta yanxu kusa dani.

Wai dan Allah dagaske kikeyi ko wasa?

Bixge wayan Baby tayi takara akunni

Hellow my lovely Bro how far?

qara yasaki cikin tsananin murna yace

"Babyyy? Wlh itace Baby ce, jama'a kuxo kugani wlh Babyn Abuja ce bata mutu ba".

Su Muhsina me xasuyi inba dariya ba ganin yanda yarikice sai xunduma ihu yake... Cikin dariya Baby tace

"Kai da Allah kanatsu ko nakashe wayan".

To..to nayi shiru, amma dai ke ce ko? Ya akayi baki mutu ba? Ina su Dady suma basu mutu ba ko? Dan Allah kibani labari kar naxauce.

Ataqaice tabashi labarin komai, sai da Muhsin yai kuka sabida tausayi.

Allah sarki Baby kinga rayuwa! Allah ne kawai xai saka miki, amma mungode Allah da yasa baki mutu ba kika dawo garemu bayan da muka d'ebe tsammani da sake ganinki, Allah yajiqan Dady da Mami Allah yakai rahmansa garesu.

Bayan hannu tasa tagoge hawayen da suka gangaro mata ta'amsa da

Ameen ya Allah.

.

***

Acikin daren ranan Nafeesa tahaifi danta qato jaxur irin ubansa sak da lukutun uwar, kuma agida tahaihu lafiyanta lau da abinda tahaifa

Sabida tsaban murna Momy kasa xama tayi sai da taxo tagansu takoma.

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now