🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar Da Dubu}}'''*⚜F.W.A📚*
*3irls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.Wannan shafin nakine my *Lovely sister Aishat Ismaeel..* Allah yabarki da mijinki yaqara donqon kauna.. Allah yabaki 'ya'ya nagari amiin
.
*EPISODE (14)*
*(Sinaa)**SIX DAYS*
Baby ce kwance saman doguwar kujera, ta cakare cikin wata baqar doguwar riga me dogon hannu sai 'yar samanta fara me hannun vest, gaban anyi flower da baqin xare, gashin kanta ta tufke shi tsakiyar kai sai taxixara d'an siririn farin dankwali, sai yaxamana gashin gaban goshinta yafito ya kwanta luf gunun sha'awa, ba ma'abociyar makeup bane dan haka babu ko dis a face dinta.
Da alamu dai charting takeyi tana ta xuba murmushi.. Wayan dake aje akan center table yasoma ringing tanaji amma ko motsi batayiba bare takalli wayan sha'anin gabanta kawai takeyi, saida akai 2missed call ana three din ne Ummee tafito daga dakinta aguje tadauka
Aslm alaikum Aunty Ihsan.
Wa'alaikumus salam! Ina kika shigane matar yaya? Inata kira baki dauka ba.
Wlh nashiga watsa ruwa ne kinsan garin da xafi, yanxu nafito shine naji wayan na tsiwa.
Ihsan tace yawwa matar yaya inaso xamu taho da qawata gidanki daga school ne, please kidanyi sanwa tare damu shiyasa nakira nagaya miki, kinsan Momy sai dare xata shigo kuma ni banason abincin sabuwar me aikin can bata iya kominta ba, tunda Saratu tadawo gidanku nadaina cin abin kowa sai na Momy.
Ummee dariya tayi tace
"To shikenan me kukeson na dafa muku?"
Mudai duk abinda kika dafa shi xamuci.
A'a kifadamin me qawar taki tafiso sai nadafa muku "tunda ni nariga nayi girkina kuma baxai ishe muba nasani.
Ihsan kallon qawarta Muhsina dake xaune agefenta tayi tad'age mata gira
Me xakici ne? Matar yaya tana tambayan abinda xa'a dafa miki.
Hararanta Muhsina tayi tace
"Bansaniba".
Dariya qasa-qasa Ihsan tayi tace
"Karki sanin, dole dai yau sai munje kinmin yini, "kinji matar yaya kidafa mana koma meye bata da xa6i".
To shikenan sai kunxo din.
Ok bye.
Cewar Ihsan tana kashe wayan... Cire wayan Ummee tayi a kunnenta tana kallon Baby ta wutsiyar ido "kafin tajuya tanufi dakinta cike da mamakin Baby, ba abinda ta iya sai dai taci takwanta sai kuma latsa waya ga iyayin tsiya.
Wai tana gidana ma ban isheta kallo ba.
Ta6e baki tayi tashige daki dan shiryawa.
***