🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
*EPISODE (39)*
*(Amazing) 2*Part ɗinta tanufa da gudu tana kuka me tsananin gaske, a palow tazube taci gaba da kukan ta har lokacin hannunta na kan kuncin ta, wayanta dake ajiye saman sofa tun fitarta tabarshi tararumo tafara neman layin Muhsina, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi ta ma kasa nemo sunan, tana dubawa tana kuka, daƙyar tasamu ta danna mata Kira, three ringing tayi peacking call ɗin, Muhsina tasoma yin magana
"Asalamu alaiykum Babylo ta Aminu, amarya awajen Aminu gimbiyar mata an tuna damu ne yau?".
Baby me makon tayi magana sai taƙara ɓare baki tasaki kuka
Subhanallah.. me yafaru ne Baby? Lafiyanki lau kuwa ko mutuwan aka sake yi?".
Cikin tsananin kuka da yaci ƙarfinta ba ma agane maganarta ta tace
"Sina nashiga ukuna, Al'ameen ne.. Al'ameen ne.. Al'ameen..".
"Mene yayi Al'ameen ɗin? Me yasame shi? Kifaɗamin mana". Muhsina tatambaye ta cikin firgita
"Al'ameen ne yamare ni Sina". Taƙarike maganan tana ƙara fashewa da kuka
Da tsananin mamaki Muhsina tace "mari fa kikace Baby? Al'ameen ɗin? Me kikai masa?".
Tace "Sina maganar nan bazai yiwu a waya ba, inda hali kizo dan Allah".
"Ok ganinan zuwa dama ina gidan Ihsan ne, Amma yanzu ganinan".
Aje wayan Baby tayi bayan ta tsinke call ɗin, tahaɗa kai da gwiwa taci gaba da rera kukan ta har sanda Muhsina tazo tatarda ita ahaka, dasauri taƙarisa wajenta tana faɗin
"Baby wai me ke faruwa ne? Me yahaɗa ku da Al'ameen ɗin?"
Ɗago kai Baby tayi tana kallonta da idanunta da sukai jazur, cikin shashsheƙan kuka tasanar mata da abinda yafaru, har lokacin da Al'ameen yasauya mata, kana taci gaba da cewa
"Sina gida zan tafi Al'ameen yanzu baya sona, bazan iya jura wannan sabon yanayin ba, wlh bakiji yanda nake ji ba".
Hannu tasa tashare hawayen da yaƙi tsayuwa mata taci gaba
"Yau Al'ameen har da cire hannu yana dukana batare da nayi masa laifin komi ba, shikenan nasan na rasa shi, ya gaji dani".
Dafa ta Muhsina tayi cikin tausayawa tace
"Ki dena faɗin haka Baby, yanzu har kina da bakin da zakice bazaki iya zama ba don kawai wannan abun ya faru? Karki manta fa shi ya yi zama dake alokacin da ke kika ƙi shi, kuma yajure har kawo uwar haka, ya yi zama dake lokacin da kike ganiyar ciwo be taɓa ƙosawa dake ba, duk saboda yana sonki yana kuma ƙaunarki ne yayi haƙuri yakuma jure, to ke meyasaka baza kiyi hakan ba? Meyasa baza kizauna ki fuskanci wata sabuwar rayuwanki ba?".
Girgiza kai Baby tayi tace
"Bazan iya bane Sina, bazan iya ba, ina matuƙar ƙaunar shi zuciyata bazata iya juran rasa shi ba,
Muhsina tace "in ko hakane dole kizauna dashi, dole ki zauna ki fuskanci ƙalubalen da tafuskanto ki, abun da kike yunƙurin aikatawa shine zai raba ku, wani ne keson shiga tsakanin ku Baby, ni na tabbata wlh abin nan dake faruwa daku wani ke shiga tsakanin ku, karki manta ke kanki hakan ya faru dake, ni kawai wacce nake zargi NAFEESA ce, in ba ita ba wlh sai dai Momyn sa, kin tuna itama bata sonki? Ko kuma sun haɗa baki duk kansu, ko kin manta cikinsu kika shigo? Ke ce bare acikin su, kinsan bare-bari basu cika zama da kishiya ba gasu da haɗin kai, don haka zasu iya miki komi don su fidda ki cikinsu, kiduba maganata Baby, wlh wannan asiri ne yanzu kuma an juya kan mijinki ne tunda an kasa cin nasara akanki, ke kuma yanzu kina ƙoƙarin ki bada hanyan da maƙiya zasu ci nasara".
Cikin sanyin murya Baby tace
"Me yakamata nayi Sina?"
"Abinda yakamata zamu faɗa ma su Mama ayima tufkar hanci tun wuri, sannan ke kuma..
Bugo ƙofar da akayi shi yasaka Muhsina yin shiru, tamaida idanunta kan ƙofar kamar yanda Baby tayi, Al'ameen da NAFEESA ne suka shigo, kallo ɗaya zakai mishi katabbatar a fusace yake, gaban Baby yaja yatsaya yana ƙare mata kallo itama ɗin idanuwanta akanshi suke ko ƙyafta su batayi, sai da yagama kalleta sama da ƙasa kana yajuya yanjanyo NAFEESA yahaɗa ta da jikinshi still yana kallon ƙwayan idanun Baby yace
"Wannan itace matata da nake son na rayu da ita na har abada, ita nake so har a zuciyata kuma ita kaɗai ce zata amsa sunan matata, ba wata macen da nake kallo matsayin mace in ba ita ba, ke kuma bansan wace ƙaddaran tasani na aure ki ba, dan haka ki tattara kayanki kibar min gida na SAKE KI.."
Yajuya yana kallon Nafeesa yace
"Hakan yayi miki?"
Murmushi tasakar mishi tace
"Good job sweety, mutafi to".
Taƙara saƙalo shi suka juya zasu fice, cikin sauri Muhsina dake hawaye tace
"Ka kuwa san me ka aikata Al'ameen? Wlh zakayi nadaman abinda kayi.."
Basu juyo ba suka fice batare da sunbi takan maganarta ba, kallon Baby tayi da idanuwanta suka ƙafe waje ɗaya, tana taɓa ta sai taga ta zube a ƙasa warwas, kuka Muhsina tasaki tabi ta ƙasan tana jijjiga ta, sai dai ga duk kan alamu ta daɗe babu numfashi atare da ita, dasauri taɗau wayanta takira Mama tana kuka tasanar mata, cikin tashin hankali Mama tace "gata nan zuwa yanzu" ba'a ɗau lokaci ba kuwa sai gata ta iso da drever, tare da Muhsina suka kama Baby suka fito da ita suka sanyata cikin motan da Mama dazo, driver yaja suka fita Muhsina na biye dasu anata motan
Asibitin da suke zuwa 'yan gidan su suka nufa, suna zuwa aka amshe ta akayi emargancy room da ita, sai lokacin Mama tasamu takira Baba tasanar mishi, kankace me shima ya iso hankalin shi duk atashe, awa ɗaya aka ɗauka ana duba ta kana aka fito da ita aka sauya mata ɗaki, nan likitan da taduba ta tabuƙaci ganin su Baba suka bita har office ɗinta, nan take sanar musu da akwai abinda yafirgita ta ne har tasamu ɗaukewar numfashi, sai dai zata ɗau lokaci kafin tafarfaɗo, baya ga haka ba wani abu kuma
bayan sun fito daga wajen likita Mama da Muhsina suka shiga ɗakin da Baby take ciki, shi kuma Baba yatsaya nan waje yafara neman layin Dady, bayan ya ɗauka yake sanar mishi da abinda ke faruwa, su ma sosai suka shiga wani yanayi dajin wai Al'ameen ya saki Baby, nan suka shirya suka taho asibitin shi da Momy, sun jima sosai kafin su koma gida, kuma har lokacin bata farfaɗo ba sannan babu labarin Al'ameen, suna komawa yane mi layinshi yace mishi yayi maza-maza yazo yasame shi, Koda Al'ameen yazo nan Dady yarufe shi da faɗa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, kuma yabashi umarnin da yamaida ita, amma buɗan bakin Al'ameen sai cewa yayi
"Dady gaskiya bazan iya zama da ita ba, sabida ko kaɗan bata dace dani ba, ba zan iya zama da me girman kan tsiya ba, kuma ma ni Dady mace ɗaya nake da burin in zauna da ita, Nafee na ta ishe ni".
Momy da Dady sakin baki sukayi suna jin zantukan shi, ba komai yabasu mamaki ba sai yanda yaƙi bin umarnin Dady, abinda be taɓa yi ba ko da wasa, su kuma basu sani ba Nafeesa tashirya mishi abinda zai faɗa, tunda tariga ta mallake sa, haka Al'ameen yafice gidan batare da yaƙara sauraron Dadyn sa ba
Tabbas ba ƙaramin damuwa Dady yashiga ba, kwata-kwata yakasa sukuni da wannan sabon halin da Al'ameen yanuna musu.
.
_to fa, me zai faru?_ 🤔