Part 36

34 2 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat Ismaeel lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.


      *EPISODE (36)*

Cikin tsananin tsoro da rawan baki tace

"Me..me kasa.ni ina..ina aiikata.wa?".

Cike da takaicinta yace

"Kina tunanin bansan baki zuwa asibiti gaida Baby bane? Ko kina tunanin bansan tunda kikaje sau daya baki sake taka kafarki kinje ba? Haba Nafeesa, haba Nafeesa wannan wace irin rayuwa ce? Ace kuna zaune gida daya da mutum bashi da lafiya baki damu dashi ba? Ai ko bakomi 'yar uwanki ce musulma, in ma kishi ne yahana ki zuwa kyaje albarkacin tana 'yar uwanki musulma, yanzu kenan da mutuwa tayi baki da asara, bazaki ta6a damuwa ba ko?".

"Amma ai bakaga ta mutun ba yanzu ko tana raye, kuma ai sai kayimin uzuri tunda bana zama agidan ne, sannan da laifinka tunda baka sanar min tadawo ba bare naje na gaishe ta".

Nafeesa tafadi hakan cike da borin kunya

Al'ameen yace "yayi miki kyau, ai yanzu sai ki kama k'afa kije kigaishe ta tunda nafada miki, wannan dalilin ne yasaka tun farko na hofantar da lamarinki tunda baki damu dasu ba, kuma naqi sanar dake Ummee na da ciki tunda ko nafadamiki ba damuwarki bane, damuwana ne ni kadai, wlh wannan ba rayuwa bane kisanja d'abi'a Nafeesa, ciwo yana wuyan kowa".

Yana kai nan azancen shi yatashi yafice, ga duk kan alamu ranshi ya sosu.. Bakin ciki da takaici ne yazo mata iya wuya tafashe da kuka, abinda take gudu kenan tun farko gashi ya tabbata, wai yau ita Al'ameen ke ma fad'a akan wadannan banzan, shikenan yadena sonta duk adalilin su, sai da tayi kukanta ma'ishi kafin tatashi tanufi daki tad'au gyale da keey din mota tafito, packing space tanufa tashige motanta tafice, tun acikin mota tayi kiran Samra tace "gata nan zuwa".

***

"Hmm dama abinda nake miki gudu kenan, tun farko nayi tunanin haka gashi ya tabbata".

Cewar Samra tana kallon Nafeesa da tagama sanar mata halin da take ciki

"To yanzu ya ake ciki? Wani mataki zaki dauka akansu? Dan wlh gab suke su raba ki da mijinki, rabuwa na har abada, kafin hakan yafaru ke ki gaggauta fid dasu, ya kikace?".

Ajiyan zuciya Nafeesa tayi tace

"Samra kibani shawaran abinda zanyi, wlh ni narasa ma me zanyi".

Samra tace "abu me sauki wajen wannan Bokan kawai zaki bini nakaiki, shi zai miki aikin da har abada zakiji dadinsa".

Nafeesa tace "kina ganin zai iya zid da cikin nan? Watanshi fa bakwai, kuma naji ance in ciki ya girma baya fita".

Dariya Samra tayi tace

"Hmm bakisan aikin Boka bane, tun aciki za'a kashe abinda ke cikin, kuma abinda yakamata kiyi yanzu mallake Al'ameen zakiyi, yazamana ke kadai yake gani ba wata macen da zai ta6a so aduniya sai ke, kinga koda ya rabu dasu baki da damuwa ba zai qara aure ba, wannan yayi ko kuwa kina da wani abinda kikeso ayi?".

Nafeesa tace "wannan shawaran tayi, sai dai bansan ya zanyi ba, me zance ma Al'ameen in zamu tafi? Kuma kinsan dole kwanaki zamuyi".

."ke yanzu bakisan qaryan da zakiyi yabarki ba?".

Shiru Nafeesa tayi na d'an wani lokaci kana tace

"Yawwa nasan me zance dashi, dama yadad'e yana fama dani nariqa ziyartar dangin mahaifina amma sam ni nak'i, su kansu sunyi mitan sun gaji har suna cewa raba ni akayi dasu, dama waye be san halin kanuri ba? Kinga sai ince mishi zani ganin dangin mahaifina, ko kwana nace mishi zanyi bazai hanani ba duk da anan Kaduna suke".

"Good yanzu sai ki fara shiri nan da kwana biyu sai mu tafi in ya yarda, in kuma be yarda bA sai musan abin yi".

Haka dai Samra da Nafeesa sukai ta shirya yanda tafiyan nasu zai gudana, dan haka Nafeesa na komawa gida aranan tasanar da Al'ameen ziyarar da takeso taje ma dangin mahaifinta, kuma zata kwana biyu tana zaga dangi, taci sa'a tana fadamishi ya amince tunda bata ta6a tambayanshi zuwa wani waje har takwana ba, bare kuma wadannan danginta ne.

Washe gari komi na tafiyarsu ya kammala, da yamma takai Arif gidan Momy domin ba dashi zata tafi ba, dakyar Al'ameen ya amince da zata barshi din, shima sai da Momy tasaka baki akan baza aje dashi ba abata shi zata rik'e shi, the following day da misalin 11:30am jirginsu tad'aga zuwa k'asan Ghana, agidan k'awar Samra suka fara sauka, sai da suka huta sukaci abinci kafin suka d'unguma dukansu zuwa wajen Boka.

.

*****

Ita kuma Ummee tun safe da tatashi, ta tashi ne da ciwon ciki me tsanani  wanda har sai da aka dangana ga asibiti, abun mamaki nak'uda ne gadan-gadan ya tunkaro ta, nan da nan aka kaita d'akin kar6an haihuwa

*Few hours ago*

Har lokacin Ummee tana naquda bata haihu ba, lokacin tuni su Baby, Ihsan dake da d'an k'uttun cikinta, Momy  Dady duk sun k'araso, duk da sunji mamaki alokacin da aka sanar musu cikin but Momy ba qaramin murna tayi ba, kasancewarta me son ahaifa mata jikoki.

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now