Part 23 Doc. Gali

38 5 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

'''Wannan shafin naki ne qawalli roman ja6a.. Kina raina akoda yaushe baxan manta dake ba MARYAM .El. FARUK .. Kina raina nima ina ranki eh eh eh , I miss u wujiga- wujiga''' 💋😜

.

       *EPISODE (23)*
         *(Doc. Gali)*

Muhsina na nan xaune inda take tana jiranta " tashigo tana kwa6e hijabin jikinta tajefa saman kujera tabi kai taxauna, Muhsina dake kallonta tace

"Yanxu daga fita har kin dawo? Kai Beby aji tsoron Allah yanxu daga fitanki minti nawa ne?"

Tsaki Beby tayi takwantar da kanta jikin kujeran tana kallon Muhsina

So kike in kwana acan kenan?

Riqe baki Muhsina tayi tana jinjina kai, ita har yanxu abinda Beby takeyi akan Al'ameen mamaki yake bata, ya xa'ayi tsana irin haka yashiga inba da sa hannu ba; " ajiyan xuciya Muhsina tayi tana kallonta tace

"Wai ke Beby duk bayanin da naimiki daxu baki fahimta ba? Kina fa da ilmi ke ba jahila bace, sannan ke wayaiya ce kinada wayonki, duk bayanin da nayimiki yaci ace kin gane".

Baby da idanuwanta kamar su fad'o qasa sabida harara tace

"To kifahimtar dani kin tsaya kinamin xancen banxa, ko in nagane xancemiki bangane bane iyee?"

Taqarike maganan cikin fusata har da d'ago kanta

Ahh su aunty Baby abun bana fada bane, wai ni naga namiki bayani ne dalla-dalla amma kamar ba bahaushiya ba kingaxa ganewa.

To daman uwar wa yace miki ni bahaushiya ce?

Rufe baki Muhsina tayi tana dariya " Baby ko haushi ne yaturniqe ta tatashi tayo kanta xata duketa, dasauri Muhsina tariqo hannayenta cikin dariya tace

"Please Baby yi haquri ban sakewa".

To uwar wa kikema dariya? Ko kinga naxama mahaukaciya ce?

Cewar Baby tana huci

Haba ke kuwa ai abun bana fada bane, nifa da kikace ke ba bahaushiya bace shine abin yaban dariya, ko dama da dangin uwa ake ado?

Fixge hannunta Baby tayi taxauna gefen gado

Ki shaqeni dan ubanki sai in fadamiki.

Wai ke aina kika koyo xagi kamar wata bamagujiya? kiyi hakuri da Allah nifa duk wasa nake miki.

Tsaki Baby tayi batace komai ba bcox haushinta da takeji

Yawwa mukoma maganarmu,, ni dai ina tunanin son rabaku akeyi da Al'ameen, kiduba d'imbin son da kike mashi amma kawai rana guda ace kin tsane shi, ni ina xargin ko ammiki asiri ne, " kuma nan da nan asiri xai kamaki sabida ko axkar na tsari bakiyi.

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now