🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*Wannan shafin nakune Nafisat's Group Novels Fans.. Iya wuya ana tare* 🤝
.
*EPISODE (16)*
*(Walid)*
.Washe gari sai ga aunty Karima babbar 'yar Uncle Bashir tabugo sammako da ita da Muhsin da babbar 'yarta Ru'kayya, sa'ar Muhsin ne sai dai yabata watanni tara.
Ba'a jima ba saiga aunty Fariqa itama tasake dawowa da 'ya'yanta biyu Asiya da nagoyan Salim, dayake ita anan Kadunan take aure kuma ba nisa gare suba, diransu kenan shima Walid (Isah) ya iso, d'a na biyu ga Uncle Bashir, babban soja ne sosai da akeji dashi "a Kano yake aiki, nan fa gida yakarad'e da murna da hayaniyansu.
Yanxu ma xaune suke a palow sunata hira har Baba "in kadauke Walid da bashi cikinsu... Baby ce tace
"Anty amma dai ba school daya xa'a hada Muhsin da Ruqayya ba ko? Domin wadannan sai dai suhana daliban karatun sabida rashin jinsu".
Dariya kowa yayi.
Anty Karima tace "ita ai s.s 3 yanxu take bata gama ba, da ko ni sai in bama Abbansu shawaran kar yahadasu".
Mama tace to wai meyasaka baki barta agida ba? Gandamemiya da ita kinbar yara kinxo da ita.
Tambayeta Mama wlh kuka taitamin wai saita biyomu, Abbansu yace in taho da ita tunda bata xuwa school "shugaban makarantansu ya rasu suna hutu, su kuma sauran kinsan suna makaranta.
To ya isa haka, kun tasamin 'yar jikallena kunata xind'anta, kuma kuna ganin ina muku alama amma bakusan yakana ba.
Cewar Baba
Muhsina tace "ai Baba gayinan kiris yarage tasaka kuka".
Dariya sukayi
Baba yace "to kubar hiran muje aci abinci, Baby kirawo yayanku a part dinshi".
Baba ni xan kirashi.
Cewar Ruqayya tana tashi da gudu tafice
Ikon Allah wai yarinyan nan yaushe xatai hankali ne? qatuwar budurwa data isa taxauna adakin miji.
Aunty Fari'ka tace "ai duk wani wauta na 'yan fari akanta yaqare".
Wayan Baby ce tasoma tsiwa, dasauri tatashi tanufi daki kowa yabita da kallo... Dariya Muhsin yakwashe dashi
Wannan sauri haka Baby? Anya ba sirikinmu bane yakirata?
Rukayya da shigowarta kenan tacafe xancen
Saurayinta ne yakira, ko daxu najita suna hiran soyayya har yana cewa xaixo yadauketa taga babynshi, ita kuma aunty Baby cikin shagwa6a tace mishi "ni baxani ba".
Kowa saida yadara sabida yanda Ruqayya take kwaikwayon muryanta... Shigowan Walid ne suka tashi suka koma kan daining, Baba yace abari ajira Baby kafin kowa yaci, Walid ko da ya iso da d'an guntun yunwansa "jin abinda Baba yace ne yahada rai dama gashi soja ba wasa.
Mutum ne shi da baicika son fara'a ba bashi da surutu ko kadan, irin murdaddan mutanan nan ne da baka gane gabansu bare bayansu, dogo ne shi me qiran samudawa, ba wani fari bane amma yanada hasken fata sosai, Walid kyakykyawa ne sosai ga farin jinin 'yan mata sai dai ko kadan basa gabanshi, in kaga yana dariya to sai dai da namiji, ko 'yan uwanshi mata baya musu fara'a, yaro da kudi kenan abokin tafiyan manya "kirarin da abokansa suke mishi.
Baba ne yace
"Ubana yaushe ne xaka shigo muyi hira? Tunda kadawo kaqule adaki, ko duk gajiyan ne?"
Walid murmushi yad'anyi yace
"Zanxo Baba, akwai aikin da nataho dashi ne nake dan qarisawa".
To gara kaxo din dai sabida akwai maganan da nakeso mutattauna na wancan yaron Anas, banaso case din yadad'e ba'a kamo shiba.
Baby ce taqariso tasami waje tsakiyan Muhsina da Muhsin taxauna tana facing Walid, aunty Karima tayi saving dinsu kowa kuma yaqara da abunda yakeso.
Baby kinsan abinda Ruqayya tace miki lokacin da kika tafi amsa call?
Baby data maida hankalinta kan abinci tanaci, girgixa masa kai kawai tayi
Wlh anty Baby qarya yakemin koma me xaice miki, ni bance komi ba shine ma yace wai kin tafi yin waya da saurayinki..
Kai kurufa mana baki, banason surutu.
Walid yafad'i hakan batare da yadago daga cin abincin saba... Murmushi Baby tayi tace
"Kyaleshi Rukky koma kin fada aike tawa ce, kuma nasan halin Muhsin shine xai fada ba ke ba".
Taka 'kafanta Muhsina tayi tawaigo takalleta
Meye haka kike takani kamar bakya gani?
Nuna mata Walid tayi da yaqara tur6une fuska "tana mata alaman tayi shiru, tura baki Baby tayi takau da kanta taci gaba da surutunta.
Fariqa tace "Baby kiyi shiru mana, bakiji abinda yaya yace bane?"
A'a kubarmin Maama tayi surutunta, banason kuna takura mata.
Kuma Baba ai kewarku nakeyi ko?
Eh Maama tunda mun dade bamu hadu ba, yi surutunki yanda kikeso, ni kaina dadin jin muryanki nakeyi, da yanxu Allah baisa kina raye ba ai ba wanda xai kawo qorafin kiyi shiru, aina ma xasu ganki?
*****
.
Rayuwa tamiqa anyi sunan d'an Nafeesa, yaro yaci sunan kakan Al'ameen wato Khabeer xasuna kiransa da Arif.
Kwanaki suna ja haka ma watanni, Ummee tasake samun wani cikin kuma yaqara 6arewa kamar wancan, "ta kaima qauyensu xiyara alokacin ana bikin qawarta Hajjo, saida taxauna akasha biki da ita kafin tadawo.
Afannin soyayyan Al'ameen da Baby kuwa sai abunda yaci gaba, kusan koda yaushe yana xuwa gidan tadi ba wanda baisan shiba in kacire Baba da baicika xama agidan ba, sai Walid da shima ba ya xama kuma har yau bai koma ba, neman Anas yakeyi ruwa ajallo, in yafita gida tun safe sai dare yake dawowa, dai-daikun rana ne xaka same shi ya wuni agida, ba ruwansa da kowa ba ya shiga harkan kowa, haka rayuwanshi yake!!!