🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls are the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*Allah kakawo mana qarshen wannan cuta ta corona virus. Ya Allah 👏👏 mun tuba* 😭
*EPISODE (2)*
*Ummee*Baffo nadawo, in kawo maka furan kasha?
A'a Ummeeta baxan iya sha ba, kidai bani ruwa ne ishi nakeji.
To Baffona, xaka samu lafiya da wuri kaji?.
Tafadi hakan lokacin datake dago kansa tana kafa mishi qwaryan ruwan.. Sallama suka jiyo awaje
Baffo yace Ummeeta tahi kigani wa ke sallama.
To Baffo.
Ta'amsa tana miqewa tafice, koda tafita wani farin dattijo tagani jingine ajikin wata baqar mota, yana sanye da kaya na alfarma, xanen fuskanshi kawai xai tabbatar maka da kanuri ne.. Kanta asun kuye taqarisa wajensa taduqa har qasa tana gaisheshi, cike da fara'a ya'amsa mata yana tambayanta Baffan nata?.
Ayya Baffona ba lafiya, sai dai mushiga kasameshi ciki.
Tafadi hakan tana miqewa har lokacin kanta aduqe yake.. Dattijon cikin tausayawa yaimishi addu'a sannan yabita suka shiga ciki, har dakin takaisa sannan tafito tad'au tsintsiya tana share tsakar gidan da yacika taf da ganyen mangwaro, kasancewar gidan akwai bishiyoyin mangwaro har uku, har tagama wannan dattijon bai fito ba, sai tasami wuri kawai agindin bishiyan tai xamanta tana tunanin rayuwanta da Baffanta murmushi yalwace a kyakykyawan fuskanta.. Bayan wani lokaci dattijon nan yafito yayafito ta da hannu, dasauri taxo taduqa agabanshi.
Ummee Baffanki yace "kikira mishi Liman da Malam Mato".
Da "to Ta'amsa" ta tashi tafice, bata d'au lokaci ba tadawo tare dasu, har cikin bukkan suka shiga ita kuma takoma wajen xamanta tabuga uban tagumi tana jiran fitowansu xuciyanta cike da fargaba, ita kanta batasan iya mintocin data dauka awajen ba kafin sufito, dasauri tadago kanta tana binsu da kallo su ma kallonta sukeyi cike da tausayinta.. Malam Liman ne yace tashiga Baffanta na kiranta.
*
Baffona..
Takira sunanshi lokacin data gurfana gabanshi tana riqe da hannunshi, hawayen tausayinshi cike a idanuwanta ganin yanda yaketa numfarfashi cikin tsananin galabaita, murmushi yake mata idanuwansa akanta yace
"Ummeeta matso kusa dani inason nafadamiki wata magana".
Matsowa tayi sosai taganka kunninta wajen bakinsa, ta d'au lokaci ahaka hawaye nata kwaranya a fuskanta, jin shiru yadena magana yasata kallonshi taga idanuwansa aqafe ba ya motsi, riqo hannunsa tayi cikin kuka tana girgixashi
Baffona.. Baffona da Allah katashi Baffona, karka tafi kabarni Baffona.. Bafffooonaaaaa... Luuu tafada jikinsa asume.
*