Part 7 Hafsa

55 5 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3ggirls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*Inama daukacin masoyana godiya da nuna ma littafina kauna.. Nagode kwarai.. Ana tare* 🤝🤧

   *EPISODE (7)*
     *(Hafsa)*

Whatttt 😳...

Beby tafada cikin tsananin firgici.. Yusuf dashima yacika da mamaki yace

Me kike nufi Hafsa?

Ai nasan kunji me nace, cewa nayi xan riqa daura mata talla tana fitamin dashi, in baxata yiba sai dai tabarmin gida

Haba Hafsa wai me kikeyi haka? Ya dan yarinya tana xaune gidanki tana cin arxiqi sai kuma kiriqa muxguna mata, karki manta kema fa kina da 'ya'yan baxakiso watarana hakan yakasance dasu ba, me kika rasa agidana da xaki tsiri daura mata talla?

Beby kuwa kalman tallan ne yake ta kai kawo acikin kwakwalwanta, wani tunani ne yafado mata arai.. Tabbas DAMA ce yasameta da xata riqa fita domin dubo uncle dinta, tunda gashi har yanxu Yusuf ya gaxa, baxata xauna cikin wnn qangin rayuwan wata banxa tana yadda taso da ita ba alhanin tanada gatan ta, tanada kudin da xata daure kaf danginta, dan haka dole ne tariqa fita..

Maganan Hafsa yadawo da ita tunaninta

Wlh kaji na rantse maka da Allah Yusuf baxata xaunamin agida ba indai baxa tayi tallan nan ba, ba dole ban kuma tilasta  taba amma ga hanya nan

To baxa tayiba, ni nakawo ta dai gidan nan ko? To nace baxa tayi talla ba tunda ita ba baiwa bace

A'a yaya Yusuf xanyi, na amince xanyi..

Nafeesa kibarni da ita tunda nace baxa kiyiba to baxa kiyinba

Cikin marairaicewa Beby tace

Dan Allah yaya Yusuf karkace haka. xanyi mata karka damu ba abunda xai faru sai alheri

Shewa Hafsa tayi

Da kinma kanki qiyamul laili atoo

Tana fadin haka tashige daki

Yusuf yace amma meyasaka Nafeesa kika amince? Banason kiyi tallan nan sabida banason wani abu yasame ki, kinga ke ba sanin garin nan kika yiba, amma tunda kince haka: akwai wani asibiti can bakin titi "tunda naga masu talla na xama dayake na gwamnati ne, sai in nuna miki inyaso kiriqa xama anan, inkin siyar kidawo gida inbaki siyar ba kidawo gida dan Allah karki wuce inda baxaki gane hanya ba

Insha Allah

Cewar Beby.. Aranta kuwa tana qudurta abubuwa da dama

*

Tun daga ranan kuwa Hafsa take daurawa Beby tallan shinkafa me manja 😋 ko me mangyada, bakin asibitin da masu talla suke xama nan itama take xama, duk ranan da bai qare ba sadaka takeyi da sauran sai tabiya kudin acikin kudinta, da xaran tagama xata bada ajiyan farantin da robobin tanausa cikin gari neman uncle dinta kuma duk tana kula da inda take bi, in tagaji kuma tadawo tadau farantin ta tayi gida, wani lokacin kuma napep take hawa yanausa da ita anguwa-anguwa, duk inda taga gungun mutane sai tatsaya tatambaye su, amma Allah  baisa ta dace ba sai baqar wahala datake sha, wlh kamar ba Beby ba in kaganta, gaba daya gayu da wasu kyale-kyale da kasanta dashi duk babu

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now