Part 40

40 3 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

*⚜{{H.Q.W.A📚}}*

*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

*EPISODE (40)*

Sai dare BABY tafarka, sai dai ayanda tafarka kamar me taɓaɓɓiyar hankali, kwata-kwata taƙi nutsuwa sai zabga ihu takeyi tana fizge-fizge, ba abinda ke mata yawo a kunninta sai kalmar sakin da Al'ameen yayi mata, sai surutu take yi kamar wacce tazare, sai da aka taru aka riƙe ta akayi mata alluran barci sannan aka samu sukuni, sosai likitoci suka sake dubata Amma basu ga komi ba.

washe gari wajen 12:00pm tasake farkawa, lokacin Mama ce kaɗai a wajenta, zumbur tatashi zaune tana bin ɗakin da kallo, dasauri Mama tataso tazo wajenta tana faɗin

"Kin tashi Baby? Sannu ya jikin?"

Kallon Mama kawai take yi batare da ta amsa ba, sai kuma tafashe da kuka tana cewa

"Mama.. Mama ina yake? Mama Al'ameen ɗina ki Kira min shi, Dan Allah ki Kira min shi, Mama kinji kice min mafarki nake yi ba abunda kunnuwa na suka jiye min gaske ne ba".

Kuka take yi sosai tana son saukowa Mama ta riƙe ta tana zub da hawayen tausayinta tace

"Kizauna mana Baby, kiyi haƙuri kiɗau ƙaddaranki haka Allah yatsara".

"A'a Mama ni wurin Al'ameen zani, ki sake ni Dan Allah in tafi, Mama bazan iya rayuwa babu shi ba, kice masa ina ƙaunar sa, dan Allah Mama kitaimaki rayuwata wlh zan mutu".

Kuka takeyi still tana son ƙwacewa mama ta riƙe ta gam, ana haka likita tashigo, nan taga abunda ke faruwa takoma takirawo Nurses sukazo suna rirriƙe ta, ita kuma tana ihu tana fizge-fizge tana cewa

"Wayyo Allah wayyo ku sake ni naje wurin mijina, Dan Allah ku ƙyale ni kunji? Ku ƙyale ni nace zanje wurin mijina ne".

Har muryanta ya disashe sabida tsananin ihun da takeyi, basu jin ma abinda take cewa, ganin dai taƙi dainawa likitan taƙara sanƙama mata alluran barci, ba'ayi minti biyar ba taɓingire, hankalin fa su Baba yafara tashi da ganin halin da Baby take ciki, duk da likitoci sun musu bayanin ba abinda ke damunta halin ɗimuwa ne but sun gaza yarda, da zaran ta farka zata ishe su da iface-iface tana cewa "su barta taje wajen mijinta" kullum cikin alluran barci ake mata, akwai sanda agaban su Dady tafarka tana ta ihu tana surutu, wani abun ma ba ka sanin abinda take cewa, duk me imani idan yaganta sai ya tausaya mata, haka Dady yaƙara komawa wajen Al'ameen, musamman yai tattaki zuwa wajen aikin shi, yaroƙi Al'ameen da yamaida Baby

amma firr Al'ameen yace "Ni fa Dady bana ƙaunarta, bana ƙaunar ko wace mace aduniya in ba Nafee na ba, wlh bazan iya zama da ita ba, in ma tace zata koma to ko kare ya fita amfani awajena, bana sonta bana.."

Gauu Dady yawanke sa da mari, cikin ɓacin rai yanuna sa da yatsa yace

"Ba shawara nake baka ba umarni ne, ka gaggauta mayar da matarka, in ba haka ba wlh zan mummunan saɓa maka".

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now