Part 37 Lost

37 3 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat Ismail lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

'''wannan shafin naki ne MAMAN AMRAH, inajin dadin nuna ma littafina kauna da kikeyi, ALLAH yaraya Amra'''❤

.


      *EPISODE (37)*
       *(Lost)*😢

A wannan lokacin kuma su  Nafeesa sun isa k'urmin dajin da Boka ke zaune, har sun gurfana gabanshi kuma sun sanar mishi da matsalan dake tafe dasu, kecewa yayi da wani irin bahagon dariya, wanda sai da kafataran girman dajin ya amsa, in ka kallesa shi kanshi abin tsoro ne bare wannan baqin dajin, cikin k'aton muryansa me ban tsoro yace

"Kinzo da bukata me sauki, kuma yanzu bukatar ki zata biya".

Hhhhhhhhh yafashe da dariya, wani qaton k'warya yadauko yafara surkullen sa, sai ga wani bak'in hayaqi na fitowa daga sama yana shiga cikin k'waryan, ak'alla ankai mintuna goma yana wannan abun kafin ya'aje  qwaryan agaban Nafeesa, abin mamaki sai ga kwaryan cike da wani irin bak'in jini, sai juyawa yakeyi yana kumfa, kai kace an d'aura awuta ne yake 6arka, qara wani surkullen yayi sai ga wani d'an k'uttun kwalba da daskararren jini yellow-yellow blue-blue jajja-jajja ga dai shi nan ne dai, har da kamar wasu tsutsotsi ne ko k'wari ne aciki? 🤷🏻‍♀️

Yace "kar6i nan".

Dasauri Nafeesa tamiqa hannu jiki na rawa ta'amsa

"Wannan abun da kika gani kullum zaki riqa shafawa a k'asan ki in mijinki zai riqa kwantawa dake, ak'alla kiyi shi na kwana goma, wannan kwaryan ki dauke shi kije kiyi wanka da jinin ciki yanzun nan akan wancan dutsen".

Yanuna mata dutsen dake nesa dasu kad'an yana zare mata idanu, Nafeesa ba bakin musu jiki na rawa tad'au kwaryan tatafi tayi abinda yasata, bayan tadawo yace

"In kin aikata abinda nasaki ke da mijinki yaqara kallon wata mace a matsayin mace yaji yana sonta har abada bazai sake ba, ke kadai ce wacce zai so kuma zai kalla a matarsa, duk abinda kikasa shi zai yi kin riga da kin mallake sa, dan haka baki da matsala da sai anyi miki aiki akan yasake su, kuma kaf tunaninsa zai tafi a matsayin ke kadai ce matarsa, da zaran yasan su matansa ne zai rabu dasu, sabida baya musu kallo a matsayin MATA".

Wani dariya yakece dashi yana fadin

"Shi kuma cikin jikinta yanzu zan aika akashe shi".

Hhhhhhh.. Yafara tsafinsa nan da nan wani abu fari yawulqa 6at ya6ace

adai dai lokacin da abun ya isa ga Ummee yashiga cikinta ita kuma tasullu6o kyakykyawan d'anta me bala'in kama da ubansa, sai dai shi ba ja bane fari ne tass irin uwar, wani irin murd'awa cikinta yasoma yi, nan da nan tafara murkususu tana nishi, tuni likitoci sun ƙara rufa akanta dan duba abinda ke damunta.

A hak'iƙanin gaskiya asirin da Boka yacillo ne, sai dai rashin sa'a d'an yafice hakan yasa abin yai aiki akanta, kan kace me sun nemi numfashin Ummee sun rasa rai yayi halinsa, Kullu nafsin za'iqatul mauti.. Ko wani rai mamaci ne, ko wani rai sai ya d'and'ani mutuwa.

_(Dan Allah kuyi hakuri fans, nasan dacewa kuna bala'in son Ummee Nafeesa, sai dai bazai yiwu nabarta ba haka natsara Book ɗina, kuyi hakuri ina muku jajen mutuwarta, Allah yabaku haƙuri da juriyan rashinta lolx)_🤪🤒

Al'ameen dake riqe da yaron besan sanda yakusan sullu6ar dashi ba, sai da Doctor Anwar yayi saurin tare shi, dama ana shirin saka sa a kwalba ne yarik'e shi yahana yana faman kallonshi, lokacin da aka tabbatar masa da mutuwarta d'iff yayi yad'auke wuta sabida tsaban firgita da yayi.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."

Ba wanda be ji mutuwar Ummee ba, haka Ihsan da Baby suke kuka lokacin da mutuwar ya iske su, ita Ihsan ma har suma tayi, Momy ma har da k'wallanta sabida ba qaramin shiganta mutuwar yayi ba, in kakalli Al'ameen alokacin baza kaso kasake kallonsa ba sabida tsananin tausayi, gaba daya idanunsa sun kad'a sunyi jawur kamar jan tattasai, kuka rahma ce ga duk wanda yashiga cikin wani mawuyacin hali, sai dai Al'ameen ko k'walla yakasa zubarwa, duk yanda kuwa yaso yayi kukan ko yasami salama cikin ransa abin yaci tura.

Cikin awanni biyu ba inda mutuwar Ummee be zaga ba, har ta da qauyen su duk sun sani, bayan anyi ma Ummee sutura an kaita makwancinta sai lokacin ne Al'ameen yasami daman kuka, kuka yakeyi kamar ransa zai fita, 😭 shikenan yasan yarasa Ummee rasawa na har abada, bazata ta6a dawowa ba

ahankali Baby tashigo dakin taqariso gare shi tana zub da hawaye, hannu tasa tadafa shi, yad'ago da jajayen idanuwanshi yasauke akanta, hawaye ne suka sake wanke fuskarta na tausayin mijinta, magana takeson tayi sai dai takasa sabida yanda bakinta yake rawa, sai dai janyo shi tayi tarungume tasaki wani kuka me ban tausayi, shima cikin kuka yak'ank'ame ta yana fadin

"Shikenan tatafi tabar mu, kin gani ko tatafi Ummeeta tatafi tabar ni, meyasa zata tafi tabar ni bayan tasan da ina buqatarta a rayuwata? Ina matuqar kaunarta bazan iya juran rasata ba, bazan iya ba wlh, kice mata tadawo, kice mata tadawo dan Allah kinji?"..

Kuka yaci qarfin shi dole yayi shiru, matse baki Baby tayi tana faman shafa kanshi tana jin zuciyanta na mata zafi.

Allah sarki Ummeetan Baffo tatafi. 😭

.

***

A washe gari da daddare su Nafeesa suka dawo, anan tatarda mutuwar Ummee da haihuwar da tayi, hakan ba qaramin faranta ranta yayi ba, domin acewarta tasamu saukin aiki, ta tabbata koda sakinta Al'ameen yayi sai Dady yasa yamaida ita, sai dai tayi baqin ciki da akace yaron na nan a asibiti a kwalba, nan takira Samra tana fadamata tane mi shawaran ta, Samra kuma tabata shawaran karta sake tace zatayi wani abu akanshi, tabarshi tariqa gana mishi azaba wuya zai kashe shi, sosai Nafeesa tayi na'am da shawaranta kuma ta d'au aniyar in aka ciro shi ita zata riqe shi sabida mummunan k'udirinta.

*WATA SABUWA.*

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now