Part 38 Amazing

30 2 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

      *EPISODE (38)*
      *(amazing)*

*WATA SABUWA*

Kwana goma da mutuwar Ummee aka wayi gari Arif ya rasu, batare da ciwo ko wani abun ba daga kwanciya barci aka tashi da safe aka tarda ya rasu, hauka ne kawai Nafeesa batayi ba sabida tashin hankali, ataqaice dai sai da tayi suma biyu kamar wanda tarasa iyayenta, tayi kuka kamar zata bishi, shi kam Al'ameen ba ma a maganarshi, sai da yayita ciwo har akai mishi k'arin ruwa, to abun ne ya had'e mishi biyu, be farfad'o daga gigitan mutuwar matarsa ba sai gashi kuma yarasa d'an sa.

Allah sarki gaskiya na tausaya maka Al'ameen, haka Allah ke lamarinshi alokaci guda sai yadauke maka kowa naka yaraba ka dasu, fatanmu dai Allah yabaka hakurin rashin su.

          Abinda baku sani ba mutuwar Arif yana da dalili, a hakikanin gaskiya Boka baya ma mutum aiki sai yabada jinin shi, ma'ana sai kabada jinin wani naka nakusa Mamarka, Babanka ko d'an ka ko k'aninka ko yayanka sannan zai maka aiki, lokacin da Nafeesa ta amince da zuwa wajen Boka nan Samra takira Boka tasanar mishi da zuwansu, kuma tanemi alfarma kar yasanar ma Nafeesa da sharad'in sa na cewa sai kabada jini zai maka aiki, saboda tasan Nafeesa bazata ta6a d'aukan d'anta tabada ba, ita kuma tanaso Nafeesa tazama tamkar ta kamar yanda takauce hanya itama takauce su tafi atare, wannan dalilin ne aka wayi gar akaga gawan Arif batare da ansan dalilin mutuwarsa ba.

.

***

*BAYAN WATA BIYU*

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da aikin Boka da yaci, domin kuwa tun kafin ayi arba'in din Ummee Al'ameen yamanta da ita ma gaba daya, haka ma Baby tuni tadena ganinshi yatare gaba daya part din Nafeesa, ita abin ma d'aure mata kai yake yi ko takira wayansa baya shiga, sai tashare sa kawai don taga iya gudun ruwansa, duk da abin na ci mata rai daurewa kawai take yi. yaron Ummee kuma tuni an ciro sa a kwalba har anyi suna yaci sunan Baffan Ummee, LAWAl suna kiran sa da NURR, kuma Dady ne yace asaka mishi sunan Baffon Ummee, Nafeesa taso ta amshe shi kamar yanda taso sai dai Momy tace "sam awajenta zai zauna" kun santa akwai son taga jikokinta bare yanzu da yarage shi kadai ne Arif ya rasu, don haka sosai take son yaron kamar ranta.

.

***

Baby ce zaune a palonta ta buga tagumi duk tarasa abinda ke mata dadi, yau dai tagaji da abinda Al'ameen ke mata, dole zata cire girman kai taje har part din Nafeesa ta isko shi, in ma wani laifi tayi masa batare da tasani ba sai tabashi hakuri su koma yanda suke, tana nan zaune taji qaran bude gate zumbur tamiqe tanufi window tad'age labulen tana kallon shi, lokacin Al'ameen yafito riqe da rigan aikinsa, d'ayan hannun kuma ya riqe briefcase dinsa, part din Nafeesa yadosa batare da ko sau daya ya kalli part din Baby ba, tana kallonshi har yashige kana tasaki labulen jikinta a sanyaye, sau tari tasha leqasa in yadawo amma ko da wasa bata ta6a ganin ya kauce hanya ya kallo part dinta ba, kamar dai ya manta akwai ta cikin gidan, fita tayi ta doshi part din Nafeesa cike da tunani kala-kala, sai da tayi nocking tatura qofan bakinta dauke da sallama

Al'ameen dake zaune saman sofa ya d'aura k'afa daya kan daya yana latsa waya yad'ago yakalle ta, d'auke kai yayi yamaida kan wayanshi yana motsa bakinsa, ga duk kan alamu sallaman nata ya amsa, murmushi  Baby tayi tanufe sa cike da takunta me burgewa, ahankali tazauna gefen shi tare da riqo hannun shi tana kallonshi, hannun nata yabi da kallo tare da sauke idanunshi akanta cike da zallan mamakinta, murmushinta me kyau tasakar masa cikin sanyin murya tace

"Ga dai ni na sauke nawa girman kan na biyo ka, duk da bansan wani laifi nayi maka ba kadena kulani, gaba daya ka sauya ko part dina ka dena zuwa, in nakira wayanka ma baya shiga, please kasanar dani wani laifi nayi maka kaza6i ka hora ni haka? Bayan kasan bazan iya rayuwa babu kai ba".

Wani irin kallo yake binta dashi batare da ya fahimci ma'anar maganar ta ba, ahankali yazare hannunsa yana me d'aure fuska yace

"Me kike yi haka? Tashi anan wajen".

Dasauri tasake riqo hannunsa tana shigewa jikinsa tace

"Haba my Doctor kayi hakuri nace maka, kayafe min bazan sak.."

wani tsawa yadaka mata

"Tashi nace ko bakiji bane?".

Saurin ja da baya tayi tana binshi da kallo, kamar dai ba Al'ameen dinta ba, ko dai an sanja mata shi ne? A ranta tafad'i hakan, sai kuma tasaki dariya tace

"Dan Allah my Doctor kadena min irin wannan wasan bana so, wlh bazan iya jurewa ba kaji? Please kayi haquri".

Taqarike maganan tana marairaice fuska tana riqe kunnenta, Al'ameen fa ransa yasoma 6aci, cikin jin haushinta yace

"Wai ke wace irin banzan yarinya ce? Daga ganin mutum kinzo kin shige masa ko anan ne zaki sami abokin shashancin naki? Dalla tashi ko inyi k'asa-k'asa dake kibar min gida".

Tsaki yaja yana kau da kanshi, aranshi yana mamakin meye had'in Nafeesa da wannan yarinyan mara tarbiya? Ita ko Baby suman zaune tayi dajin zantukan shi, takasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiyo mata, nuna kanta tayi da yatsa cikin raunin murya tace

"Ni ce banza Al'ameen? Ni ni zaka duka? Ni ce fa Baby.. Babynka".

Murmushi tasaki

"To sai dai kakashe ni Al'ameen amma bazan bar nan wajen ba, sai kafadamin abinda nayi maka, in ma wasa kake min dan Allah ka gaggauta kade na nace maka bana so tun kafin nasami ta6in kwakwalwa nazauce".

Tafad'a idanuwanta na cikowa da k'walla, miqewa yayi zai tafi tayi saurin riqo hannunsa, yana juyowa yasharara mata mari kana yanunata da yatsa da kakkausan murya yace

"In kika sake gigin ta6ani uhmmm.."

Kad'a hannun sa yayi yajuya yatafi batare da yace komi ba, Baby dake dafe da kuncinta cikin tsananin firgici da mamaki ta kasa furta komi, sai hawayen da suka sauko suka wanke mata fuska, miqewa tayi tafice da gudu tana wani irin kuka, Nafeesa da tafito daga daki nan taga giftawar Baby, dasauri tayi dakin Al'ameen tana k'wala mishi kira.

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now