Part 22 Al'ameen

36 4 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

~WANNAN SHAFIN NAKU NE~

'''Ammin Faruq, Addan Zainab, Falmata Umar, Maman Malam, M.Khairat, Asma'u b. imam, Bella,Mommyn Sayyid, Real yar'pillo,  Shafa'atu''' _dama wadanda ban fade sunansu ba duk kuna raina, kuma INA jin dadin bibiyan littafina da kukeyi akoda yaushe, da Nuna kaunarku gareshi, Nagode_
❤❤❤💃💃💃💃💃👌

.

      *EPISODE (22)*
        *(Al'ameen)*

Da walakin goro amiya, ashe shiyasaka naga kwana biyu ba ya xuwa kuma naga baki damu ba? Ko hiransa ma kwanan nan kin dena min, amma...

Wayanta da yasoma qara shi yatsai da ita daga abinda takeson fad'i, kallon Baby tayi ita kuma takau da kai

Kinga gashi yasake kira, yanxu kidau wayan dan Allah kiji me xaice miki..

Sai da taita roqonta kafin ta amince shima sai akira na biyu tadauka

Hellow Babyna kina lafiya dai ko?

Lafiya lou.

Tafada cikin sanyin murya

Inata kiran wayanki baki dauka ba wai me yafaru ne? Kin tadamin da hankali wlh.

Shiru bata bashi amsa ba

Hellow.. Baby.. Helloww kina jina kuwa my Feenah?

Ina jinka.

Wai halan naimiki laifi ne? 'Yan kwanakin nan gaba daya kin sauya min, me ke faruwa ne please kisanar dani karkisa ni cikin damuwa, " dan Allah Baby kisanar dani laifin da naimiki sai in roqi yafiyarki, nagaji da wannan sabon halin da kike nuna min.

Nifa bakai mun komi ba.

Tafad'a a yatsine har da hararan wayan... Muhsina dake kallonta sai da tamurmusa

Ok naji dadi my Feenah tunda ba wani laifi da naimiki, ina nan xuwa anjima domin in qara wanke laifina ko gimbiyar mata xata dena fushi dani takuma yafemin, tunda biki yaqarato ina cikin busy sosai " ga kuma ginin da akemin shi yaqara 6oye ni banxo ba, duk da dai naga kwanakin nan kin sanjamin ba'a bani kulawa sosai shiyas..

qitt.. Baby takashe wayan tana jan dogon tsaki tawurga ma Muhsina wayanta, ai ko sai ga kiran yasake shigowa, Muhsina kallon Baby tayi sai kuma ta'amsa kiran

Hellow ya naji kin katse kiran?

Yayana ba itace ba, Baba ne yakirata takashe tatafi.

Al'ameen da bai wani yarda ba yace

"Ok ki gaishemin dasu Maman sai naxo anjima".

Yakashe wayan batare da yajira jin me xatace ba

Haba ke kuwa meyasaka kika kashe masa waya? Wulaqanci ne wannan fa.

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now