🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*INA muku albishir da cewa nan ba da dadewa ba sabon littafina zai bayyana, mai suna LABARIN DEEBIZAH, labari ne da zaizo muku da wani irin salo naban mamaki, labari ne da yakunshi ZALUNCI, TSANTSAN TAUSAYI, SOYAYYA DA ZALLAN BIYAYYA, kai abubuwa da dama ya hada, kudai nemi naku karku sake abaku labari. LABARIN DEEBIZAH.*
.
.
*EPISODE (17)*
*(Surprise)**TWO MONTH AGO*
Yanzu Al'ameen aure kakeso ka qara?
Cewar Dady da yakafeshi da idanuwa... qara sunkuyar da kanshi yayi cike da fargaban rashin yardan mahaifin nashi
yanxu inbe yardaba ya xaiyi? Shikenan yanaji yana gani xai hakura da Feenah?.. Muryan Dady yadawo dashi duniyarsa
To kafadamin mana in wani abun ke faruwa sai aima tufkan hanci, in sun maka laifi bata wannan hanyan yakamata ka hukuntasu ba, mafi akasarin maza in matansu sunyi musu laifi sai subi ta wannan hanyan dan hukuntasu, su aganinsu insun qara aure to sunyi maganinta.
Girgixa kanshi yayi
Wannan ba daidai bane, kakoma ku sasanta kajanye wannan maganan.
Cike da sanyin jiki Al'ameen yace
"Dady wlh tallahi basuyimin komi ba, wlh ni nake da ra'ayin qara auren ba sabida su xanyi ba".
Jimm Dady yayi kafin yace
"Ikon Allah, wai Al'ameen kaine da hada mata uku? Yanxu natabbatar da karya ne da Hausawa ke cewa kyan d'a yagaji ubansa, ato gashi ni banyiba kai kayi, "tunda nake ban ta6a ra'ayin mace biyu ba bare akai ga uku, kai kaf danginmu ma kadan ne ke da mata biyu, amma yau ga d'ana na cikina da tara mata 3, uku fa Al'ameen?"
Dady yaqarake maganan yana nuno ukun da yatsunshi
Yanxu to yarinyan aina take? 'Yar gidan waye?
A Abuja take Dady, amma tana xaune anan Kaduna gidan Uncle dinta Alhaji Bashir Isah inkiya Basho.
Ikon Allah! Alhji Basho dai dana sani abokin kasuwancina na sabon layi G.r.a?
Cike da qwarin gwiwa Al'ameen ya amsa mishi
Eh Dady shine, anan gidansa yake.
To kace yarinyan a Abuja take? Kana nufin 'yar marigayi Alhaji Ismaeel? But anan mukaje ma Alhaji Basho gaisuwa yace mana da 'yarsa kwalli daya akayi gobaran.
Eh Dady da ita sukayi tsammani, amma ita ta tsira lokacin da 6arayin sukaxo kashesu.
Allah sarki! To shikenan ni baxan hanaka auren taba sai dai ma insa muku albarka, kuma kaga Allah ya xa6o kaf matan naka marayu, kasan dai yanda riqon marayu yake da dumbin lada, to sai ka jure ka kau da kanka sannan kuma kayi adalci, kakasance me adalci a tsakaninsu Al'ameen, kar kace kafison wance "wance kuma bakaso, to kasani duk wanda yamuxguna ma maraya shima Allah baxai barshi ba, kakula kakula Al'ameen, Allah yatayaka riqo Allah yasanya alkhairi da albarkansa acikin aurenku.