🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*LITTAFAN MARUBUCIYAN*
*Na isa ne*
*Ga ba*
*So mai zafi*
*Nusnim*
*Rayuwata*
*Butulci*
*Nafeesa*.
*EPISODE (31)*
*Samra**ONE WEEK AGO*
Kai kawata kinga yanda kika koma ne kike wani shainnig? Wai ni kam meye sirrin ne? Naga tauraruwan naki sai 'kara haskawa takeyi, wa kuma aka danqo mana?
Juya idanuwa *Samra* tayi tana taunan chwingom, yayin da tadaura kafa daya kan daya tana turo dankwali goshi tace
"Hmm aike naki wasa ne, yanzu ne nasan duniya tana cin min tana kaini inda nakeso tunda nasami abinda nadade ina burin mallakarshi atafin hannuna, kwanan nan ma ganina wuya zai riqa miki.
Allah kawata?
Wlh kuwa ina gaya miki domin dai na mallaki *MUKHTAR ALI* atafin hannuna.
Zaro idanu *Nafeesa* tayi tana fadin
*Mukhtar Ali* dai naki? Mashahurin me kudin nan da yayi 'kaurin suna akaf Nigeria da 'ketare, mallakin *M.A Companies L.t.d?*
Dariya *Samra* tasaki tana wani irin taunan chwingom irin dai na riqaqqun karuwan nan tace
"Yes shi fa, kwanan nan zakiji na aure shi".
Muskutawa *Nafeesa* tayi tagyara zamanta dakyau yanda take ganin *Samran* sosai tace
"But taya hakan takasance? Mutumin da duk nacinki kin gagara samunshi dole kika barshi amma yanzu kike fadamin wannan zancen? Wai ma tsaya kin manta da kince min ba yanzu zakiyi aure ba? Ya akai haka please tell me?
Uhm zancen DA kenan kikeyi da nake tunanin bazan same shi ba, hmm bakisan me yafaru bane sai yanzu natabbatar da Malam shi din Malam ne ba Boka ba, yanzu nasan naje guri asalin Boka mashahurin Boka me aiki tamkar yankan Adda don bazance Wu'ka ba, hmm sha yanzu aiki yanzu wanda indai kaje da bukatanka yake biya maka nan take.
Wai me kike nufi ne *Samra?* kifitar dani daga duhun da nake na gaza ganewa.
*Samra* tace "kema kinsan faman da naitayi domin na mallaki *Mukhtar Ali* amma Malam yagaza min wannan aikin, sai gashi wannan tafiyan da nayi zuwa Jordan na hadu da wata nan da nan muka zama kawaye tamkar mun dade da sanin juna, ayanda tayarda dani lokaci daya take fadamin sirrinta nima haka na amince da ita, anan take bani labarin hatsabibin Bokanta dake mata aiki tace in shirya takaini wajensa a 'kasan Ghana yake kuma itama din anan take, shi yayimin wannan aikin rana daya kacal sai ga M.A ya bayyana gare ni, wlh zakisha mamaki yanda nake jan akalan M.A baya jin maganan kowa sai nawa, yanzu haka ce masa nayi bazan iya aurensa ba sai yasaki matarsa, tuni ya danqara mata saki, kuma ni yanzu ashirye nake narabasa da kowa nashi na mallakesa ni ni kadai, wlh ina fadamiki ba karamin Hatsabibi ne Bokan nan ba yasan aikinshi sosai, dan haka kibar wahalar da kanki wajen wancan malamin kikoma wajen wannan bukatunki tabiya nan da nan".
*Nafeesa* data zuba tagumi tana jin zantukan *Samra* har taqare kana tace
"Anya zan iya? Gaskiya bazan iya zuwa har wani Ghana wajen Boka ba, karki manta ni inada miji bansan me zance mishi ba in zan tafi, sannan kuma inajin dadin aikin Malam domin ina ganin komi daidai, aikin da yayimin kwanan nan har nafara ganin sakamako".
Daga nan tabata labarin aikin da Malam yayi mata komawan da tayi.
*Samra* tace "to menene amfanin wannan abun da kikayi? Ai kamata yayi aimiki aikin da za'a gama da ita nan take, but yanzu bakya tunanin kafin mutuwar nata agano matsalanta? Wlh ana kaita wajen Malam zai gano abinda ke damunta daga nan yayi mata magani tawarke, kinga shikenan aikinki yadawo baya tunda ai aikin aljanu ne, amma da kin aika ta barzahu tun farko ke kanki bazaki shiga zargi ba".
*Nafeesa* tace "gaskiya ne maganarki, amma ni naji tsoron kashe ta ne tun farko shiyasaka nayarda da shawaran Malam, wlh *Samra* inajin tsoron dai ace nayi kisa abinda ban ta6a tunanin zan aikata ba".
Murmushi *Samra* tayi tana kallonta tace
"Akan biyan bukatanki dole ne ki aikata, ke kishiya fa ba abin jin tausayi bane, ke in baki kasheta ba ita in tasami dama wlh sai ta kashe ki, kuma banda abinki naga ai ba daukan wu'ka kikayi kika da6a mata ba, ba'a kamaki handright kin kasheta ba, karki manta Malam ke da alhakin kasheta ba ke ba, ko lahira mukaje baki da laifi shine me laifi, dan haka kibar ma tunanin wai ke ce kikai kisan".
(Hmm kaji shashanci Allah yai mana tsari da irin wadannan kawayen 🙏🙏🙏)
*Nafeesa* gyad'a kanta tayi alaman ta gamsu, dan sosai taji zantukan *Samra* sun shigeta kuma takara samun kwarin gwiwa duk wani tsoro da takeji yafice fit, too tunda an fadamata alhakin kisan ba'a kanta yake ba, taqaddara ba itace tayi kisan ba.
Ni kam wai ya Amaryan taku take? Kina kuwa zuwa kiduba aikin naki? Kuma kin tabbatar zaman doya da manja sukeyi?
Cewar *Samra*
Ta6e baki *Nafeesa* tayi tace
"To me zanje inyi mata kayan takaici, ni fa wlh natsani yarinyan gaba daya rayuwata bana son ma ganinta, dan haka ban ma ta6a taka part dinta ba, aiki kuma na tabbatar yanaci tunda nafara ganin an kaita asibiti".
*Samra* dariya tayi tace
"Amma ke kam banza ce, ai kamata yayi kije kitabbatar, kar kina nan zaune kin saki baki asha dake, dan haka kitashi yanzu muje kiraka ni nima inason in ganta, inga wacce tahana 'kawalli na sukuni".
Hmmm.
Kawai *Nafeesa* tace tatashi suka fita sukai part din *Baby,* nocking *Samra* tai tayi but shiru kakeji, sai ta murd'a handle din kawai yabudu..
.
Hmmmmmm