🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*AGLAN NISA* '''jinjina agare ki, bazan manta dake ba SBD kin kasance wacce tasa nasamu kaina cikin wannan gida me albarka, bazan manta dake ba SBD hakan bA karamin ci gaba yasa nasamu ba, nasan da bana cikin wannan kungiya da tuni nadade da fita duniyar marubuta, alokacin da nake tunanin dena rubutu alokacin Allah yahada mu har nasamu kaina cikin wanga kungiya, hakan tasa na ha66asa don nima adama dani. Kisani bazan ta6a mantawa dake bA.''' ❤🤝
.
.
*EPISODE (33)*
*(Baby 2)*Sannu ahankali ciwo ke cin *Baby* batare da sanin *Al'ameen* ba, domin tun sanda yakaita asibiti bata 'kara bari yaganta ba, shima din tuni yafita harkanta sai dai abin na cinsa a zuciya, yakasa gane meye damuwar *Baby* meyasaka take masa haka? Abu daya dai kawai yasani duk runtsi duk wuya bazai ta6a rabuwa da ita ba, shiyasa yabarta tagama duk guje-gujenta da duk wani abu da take yi kafin yawaiwayo kanta, kaunar da yake mata shine musabbabin rashin daukan mataki, da zaran ya yunquro don samun madafa sai soyayyarta tahana shi ta6uka komi, don haka yanzu yadena matsa mata baya shiga harkanta " sai dai in ranan kwananta ne zai zo part dinta yakwanta, da zaran gari yawaye zai fice sai kuma dare zai sake shiga.
Haka kuma *Ummee* tana zuwa time to time tayata hira duk da ita *Baby* sau daya tata6a zuwa part dinta, watarana dai *Ummee* sai da takasa hakura taciri baki tatambayi *Baby* ko bata da lafiya ne? Domin raman da takeyi da yanda takoma dole kace ba lafiya ba, but *Baby* ce mata tayi lafiyanta lau ba abinda ke damunta, ita dai *Ummee* bata yarda ba amma tazira mata idanu don aganinta ai *Al'ameen* shima yana kallonta yana ganin yanda tasauya be dubata ba kuma be kaita an dubata ba.
Ita kanta *Baby* tana cikin damuwa da yanda take fama da tsananin ciwo, duk akace dare yayi to bata da sukuni sai kuma in garin Allah yawaye, kwana take cikin matsanancin hali da ciwon kai mai azaba, gashi takasa fadama kowa, *Muhsina* ce abokiyar shawaranta kuma ita din yanzu bata zuwa sai dai suyi waya, kullum tana makaranta bata da lokaci gashi sun kusa fara Exams na first Semester kai ya dau zafi.
ciwon *Baby* qara gaba yakeyi ba sauki har yaci karfinta kusan kwana biyu bata iya motsawa ko nan da can ta matuqar galabaita gaba daya tafita hayyacinta, ana cikin haka Allah yakawo *Ummee,* koda tashigo tayita sallama shiru tazauna a palow ta dad'e " daga qarshe takoma part dinta, can yamma tasake komawa tayita sallama shiru " wannan karon hankalin *Ummee* bai kwanta ba, sai tashiga dakin *Baby* nan taganta bata numfashi tamkar matacciya, ba karamin razana tayi ba da ganin *Baby* awannan matsanancin halin, nan take takira *Al'ameen* tasanar dashi " cikin qanqanin lokaci ya iso, firgici tashin hankali su suka diran masa lokaci daya da ganin *Baby,* domin atunaninsa ko ba ita bane? Sai dai ko kadan bazai iya manta kamannin abar kaunar sa ba, tashin hankalin da *Al'ameen* yashiga adai wannan lokacin ba'a iya kwatantashi, domin shima din zubewa yayi anan wajen jikinshi na wani irin rawa kamar mazari tuni kuka 😭 ya kubce masa, ita kanta *Ummee* tayashi kukan takeyi tarasa inda zatasa kanta, dakyar *Al'ameen* yayi jarumta yatashi yadau *Baby* sai asibiti.
Nan likitoci suka rufar mata, shi kansa *Al'ameen* yakasa ta6uka komi sai kuka da yakeyi sai kace qaramin yaro. Bayan awa biyu suka shawo kan matsalan sai dai bata farfad'o ba but tana numfashi, kuma duk iya binciken su sun kasa gano ciwon dake damunta, sai dai Ulcer da yanzu yafara cin jikinta " kasancewar tadena cin abinci ad'an kwanakin nan.
*Al'ameen* yarasa ya zaiyi da ransa, gashi yagaza kiran kowa yasanar musu, me zaice ma danginta in sukaga yanda takoma?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..
Shi yaketa nanatawa aransa kafin yasami 'kwarin gwiwan sanar ma *Baba* sannan yakira *Dady* da *Momy* su ma yafadamusu.
Lokacin dasu *Dady* suka taho asibitin sukaga halin da *Baby* ke ciki hankalinsu yatashi, nan yayita ma *Al'ameen* fad'a kamar ya'ari baki " akan meyasaka yabar yarinyan mutane da ciwo be dau mataki ba? Ita kanta *Momy* sai da tayi masa fada, domin ba qaramin tausayi *Baby* tabata ba, lokacin da su *Baba* sukazo su ma hankalinsu yai qololuwan tashi, wai *Baby* ce takoma kamar skelator? *Mama* da *Muhsina* kam kasa jurewa sukayi sai kuka, kankace me ciwon *Baby* ya yad'a dangi da abokan arziki, kullum zuwa gaisheta akeyi har yanzu jiki ba sauki.
In kaga *Al'ameen* sai yabaka tausayi, domin shi kansa sai da yarame kullum bashi da sukuni
Sai da *Baby* tayi sati uku curr kafin tafarfad'o, hakan ba qaramin farin ciki ne yasamu azukatan masoyan *Baby* ba, in kaga yanda takoma sai ka tausaya mata " gaba daya tayi haske kamar mara jini sai qasusuwa, idanuwanta da suke fari sol sun koma kore sharr gunun tausayi, sai suka qara fitowa waje suka sake yin qwala-qwala 😃shashin kwarmin idanun sunyi ba'ki, komi yin mata akeyi bata iya motsa ko da yatsa.
Duk wannan bidirin 'kawarku *Nafeesa* sau daya tata6a zuwa gaisheta " shima din kar ace batazo bane, *Ummee* kuwa har kwana takeyi awajenta.
Cikin sati daya da farfadowar *Baby* ciwo rigigim yataso mata, sai numfashi takeyi sama-sama kamar me Athma, daga qarshe tasume, hankalin Doctors yatashi nan aka rufar mata wajen ceto rayuwanta har da *Al'ameen,* dakyar suka samu numfashinta yadawo da taimakon Allah da taimakon Oxygen.
.
.
_Anya fans bazamu shirya cin 'kumba bA?_ 🤔 _ko yakukace iye?_🤭😂