🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
*EPISODE (42)*
"Whatt.. Boka ya mutu fa kikace?"
Cewar Nafeesa tana miƙewa daga zaunen da take kafin tawaro idanu tana bin ƙofar ɗakin Al'ameen da kallo, kana cikin ƙasa da murya tace
"Mun shiga uku Samra yanzu ya zamuyi?"
Shiru tayi tana sauraron ta can tace
"Wai ya kike faɗin in kwantar da hankalina bayan da kinsan akwai matsala.."
"Ok yaushe ne zai dawo?"
"Shikenan Amma Gaskiya ki gaggauta samo Mana wani sabida tsaro, kinsan bazamu zauna ahaka ba.."
"Ok bye zan kiraki".
Tana sauke wayan Al'ameen yafito daga ɗaki fuskarshi aɗaure yazo kusa da ita yazauna
"Wai sweety har yanzu maganar ce? Inace min gama ko?"
Tafaɗa hakan tana kallon fuskar shi, ɗan sakin fuska yayi yace
"Nafee na bakisan yanda nadamu da Naga ƙwanyina bane, why not mu amso Nurr yazauna damu? Kinga sai.."
"Ya isa da Allah, nace maka bana son wannan maganan, inace Kai da kanka kaduba mu kuma kaga lafiyan mu lau? Kajira lokaci kawai zakaga mun Sami namu ƴaƴan, Amma ni bazan iya rainon yaron wata ba".
Murmushi yayi yace
"To menene naɓata rai kuma?"
"To ai Kaine da wata magana, ka ƙi haƙuri kafauwala ma Allah, yaushe ma mukayi auren ne da zaka damu kanka? Karka manta Nima fa ina son nahaihu, har yanzu mutuwar Arif yana damuna, Ina son naƙara samun wani yaron nima".
Janyo ta yayi yakwantar da ita a jikinsa yana shafa kanta yace
"Karki damu mun kusa samun wani, insha Allahu bazan sake miki maganar ba, kinji daɗi ko?"
Murmushi tayi tana kallon fuskar shi tace
"Sosai my sweety, shiyasa nake ƙara sonka sabida kana son farin cikina baka son ɓacin raina".
Sai tasakar mishi kiss a lips
"To muje ɗaki Mana sai kiyi min da yawa, kinsan nan akwai takwaranki ƴar sa ido".
"Kuma hakane sweety, ɗauke ni muje ɗaki".
Ɗaukanta yayi suka shige ɗaki suka barni nan baki sake da littafi ahannu, tsaki naja araina nace
"Baku burge ni ba, wai sunyi hakane don natsai da labarin akansu, to baku Isa ba, yanzu ma nafara sai naga ƙarshen ku lolx 😅
Agurguje da Allah, wlh ko nagaji gashi na ɗibo labarin da faɗi amma inaga bazai samu ba, naso daga nan kuma naƙara dasa rubutuna ne na faɗaɗa shi, sai dai Gaskiya bazai yiwu ba ana jirana 😁🤒, dole nagajarce shi narufe ƙarshen littafin, amma karku damu *Jikar Lawali* fa na tare daku zamu haɗu awani Book ɗin ai yanzu aka fara, Allah dai yadafa Mana, yasa mu rubuta abinda zai amfane mu.🙏🏼🙏🏼