🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne._wannan shafin naki ne KAKUS.. ADAMA ALIYU Ina jin dadin yanda kike nuna ma littafina kauna, nagode Allah yabar zumunci. Ina yinki sosai da sosai_
💓💓💓💃💃💃.
*EPISODE (21)*
*(Malam)*Kina nufin boka?
Cewar Nafeesa tana xaro ido
Koma me xakice what ever, indai kinaso to xan kaiki, nasan duk wata matsala taki to taqare " har ita wacce take cikin gidan taki xai fidda miki ita, ke dai kawai kikwantar da hankalinki kicire tunani aranki.
Samra taqarike fadin hakan tana dafa kafadan Nafeesa dake tunani. " Ajiyan xuciya tasauke
To shikenan na yarda kikaini indai xai raba wannan auren, ni wancan dake gidana bata ita nake ba, gwara in soma maganin ta wajen.
Hakane kam, to yaushe kikeson muje?
Cewar Samra da tatsareta da idanu
Ko yanxu ma muje, dan banaso lokaci yaqure mana.
Ok to bari in dauko gyalena mutafi.
Samra tace tana miqewa tanufi daya daga cikin qofofin biyu da suke jere a palon, bata jima ba tafito suka fice a motar Nafeesan, " minti 20 yakaisu qofar wani dan madaidaicin gida, basusha wahalan ganin Malam ba kasancewar ba layin mutane, bayan sun shiga sun gaidashi yakallesu cikin sakin fuska yace
"Hajiya Samra kwana biyu kin 6uya ina kika shige ne?
Uhm Malam kasan ai bana xama a garin, yau ma nadawo.
Dariya yayi yace
"Gaskiya ne Hajiya Samra, sai kuma an waiwayo mu ai muke ganinki in ansami cikas din wanda xa'a lashe, " yanxu kuma meke tafe daku na ganki da baquwar fuska?
Malam nakawota ne itama tana da matsala.
Samra tafada tana taunan chwingom
Ok to ba damuwa tayi bayani mana.
Nafeesa tace dama Malam mijina ne keson qara aure ni kuma banaso, inason arabasu.
Ok indai wannan ne ai abu me sauqi ne domin mun saba yin irinshi, bari mugani.
Jawo farantin dake gabansa yayi yasoma xane, yadade yanayi kafin yad'ago kansa yana kallon Nafeesa yace
"Gaskiya aikin nan ba yanda nadauke shi dasauqi bane, xai d'an bani wahala domin kuwa shi mijin naki naga alama yana matuqar son yarinyan kamar ransa, kuma yanada yawan ibada ba ya wasa da addu'a " kuma naga akwai aure a tsakaninsu".
Yanxu malam to ya xa'ayi?
Nafeesa tace cikin fargaba
Eh to hanya daya ce, kuma ta hanyar yarinyan ce " domin ita bata cika addu'a ba sosai xamu iya cin galaba akanta, aure dai wajibi xa'ayishi tunda akwai rabo a tsakaninsu, sai dai xan saka tsana me qarfi a tsakaninsu ta hakan ne kawai xasu rabu.