Part 4

62 6 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*Ina matuqar kaunarku masoyan littafin NAFEESA. I love u so much 💋❤*

NAFEESA
Littafi ne da xaixo muku da wani irin salo. Kudai ci gaba da bina danjin yanda xai kaya.

*EPISODE (4)*
*(Beby)*

*ABUJA STATE*

Budurwa ce da baxata haura 20yers ba, sanye take da baqar doguwar Riga, tana goye da 'yar qaramar jakar baya.., sai tsilla gudun ceton rai takeyi, jefa qafafunta kawai takeyi tako INA bata damu da duhun dare ba burinta kawai tatsira da rayuwanta.

Wasu qattin maza biyar ke biye da ita, ga bindigogi a hannunsu but sun kasa harbawa kasancewar dare ne kar hankalin mutane yadawo garesu, Allah yabata sa'a takarya kwanan da yarabu hanya biyu tafad'a gidan dataga qofa abude tarufe gamm harda saka saqata, ahankali taxame jikin qofan cikin tsananin gajiyawa, tana wani irin numfarfashi cike da galabaita, duk da yanayin datake ciki be hana kagane halin d'imuwa da furgici da tsantsan tsoro datake ciki ba, kuma duhun wajen be hana kahango yanda fararen idanuwanta suka firfito waje ba.

Ita kanta batasan iya mintocin data dauka ahaka ba, kafin taxame nan qasa takwanta xuciyanta na wani irin harbawa tuno abunda yafaru a wanni kadan da suka wuce, runtse idanuwanta tayi hawaye masu radadin xafi suka sulmiyo a kuncinta.

Ya Allah.. Ya Allah kataimake ni, Dadyna..Dadyna.. Dady Mami sun rabani dasu, wayyo Allah sun harbe min su, ya xanyi da RAYUWATA (tsohon littafina) na shiga uku ni BEBY, wlh sun rabamu "wayyo Allana wayyo Allana .

Wani irin gunjin kuka takeyi mai cike da ban tausayi.. Ahaka asuba tayi tana cikin wannan halin, ba qaramin galabaita tayiba ga wani irin axababben ciwon kai dake damunta.

Yunqurawa tayi tadafa bango tamiqe cike da jarumta, fita tayi agidan kar masu shi sufito suganta.. Bata wani tafiya mai nisa ba tafito titi lokacin dakyar take cira qafanta, xuqune tayi awajen har saida gari yafara haske kafin abin hawa sufara wulqawa, napep ta tare tashiga tare d tallabo kanta tariqe GAM

Hajiya INA xan kaiki?.

Me napep yafada lokacin da yasoma tafiya

Nima bansaniba, kakaini duk inda yayimaka ka'aje ni.

Kamar ya fa?

Yatambaya lokacin dayake kallonta ta mirrow

Hajiya in wani Abu ke damunki ki sauri kifadi inda xaki nakaiki ba wai kicemin baki sani ba.

To kasauke ni a shoprite mafi kusa please.

Basu jima ba suka iso, jakan dake bayanta tasauko taxage, bakomi aciki sai takaddun filaye da gidaje sai kuma bandir din 'yan dari biyu, xaro biyu tayi tamiqa mishi tafito.. Me napep na fadin

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now