Part 8 Babyna

53 4 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

      *EPISODE (8)*
        *(Babyna)*

Beby ce dauke da faranti akanta anjera robobin abinci asaman, xuwanta kenan wajen tadoshi wurin sana'arsu batare data kula da motan da tashanyo kwana xata shiga asibitin ba, saura qiris yabigeta yadakata lokacin kuwa Beby har ta tsorata taxube daga ita har farantin tallanta

Cikin hanxari yafito daga motan yanufeta lokacin har mutane sun d'an taru suna mata sannu da tambayan bataji ciwo ba?,. qarisowanshi wajen yayi daidai dasaukar idanuwansa kan hannunta da yagurje  yana tsatstsafo da jini "yayinda ita kuma taduqufa wajen kwashe shinkafanta da yaxube.. Cikin sanyin muryansa me cike da dadin sauraro tace

Baiwar Allah dan Allah kiyi haquri ban kula dake bane, inba damuwa muje cikin asibiti naimiki dressing hannun

Dara-daran idanuwanta tadago tasaukesu akanshi suka sarqe da nashi idanun, tsawon sakwanni suna kallon juna kafin tadauke kanta taci gaba da kwashewa, wani tsoho ne yace

Ai Allah ya auna arxiqi yarinya tashi kibishi, likita ne shima cikin wanga asibitin sai yawanke miki hannun

Beby tashi bari in kwashe miki kije kidawo

Cewar wata matashiyar yarinya da suke talla tare.. Miqewa tayi batace komai ba tanufi hanyan shiga asibitin, Al'ameen da yanufi motansa xai bude mata yaga tayi gaba abinta, shima shiga motan yayi yabi bayanta cikin asibitin, koda tashiga tsayawa tayi jiransa yaqariko yana mata murmushi yace

Bismillah ko..

Bayanshi tabi suka nufi office dinsa, nuna mata waje yayi taxauna yadauko first aid box tare da matso da kujera gabanta yaxauna yasoma mata dressing hannun, duk da ba kallonshi take ba tanajin yanda idanuwanshi suke yawo ajikinta, aranta tace

Oh wannan kuma aikin dake gabanshi yake ko kuwa kallona?

'Dago kanta tayi takalleshi shima itan yake kallo, 6ata fuska tayi takau da kai tana huro hanci 🤣, murmushi yayi aranshi yace

Kai wannan beauty girl din da alama xatayi fad'a ne

Janye hannunta tayi tayunqura tamiqe

Em baki jiba?

Kollonshi tayi taware fararen idanuwanta batare datace komai ba

Anan wajen kike talla ne?

Shiru tayi taci gaba da kafeshi da idanu

Emmata ko dai ke kurma ce?

Ciki-ciki tace

*Ina jinka, maganan ce dai banjin yi

Murmushinsa me kyau yayi

Da alama dai ke rigimammiya ce, anyway ko xan iya sanin sunanki dan Allah?

Beby..

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now