🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne._Wannan shafin naki ne KAKUS kisha sha'aninki, ADAMA ALIYU, INA godiya da nuna ma littafina kauna, Allah yabarmu tare_ 🤝💓❤
.
*EPISODE (32)*
*(Baby)*Shiga sukayi nan kallo yakoma sama, domin dukansu d'ib sukayi da ganin tsararren hadadden palon *Baby,* gaba daya sun gaza motsi sai idanunsu dake juyawa suna kallon tsadadden kayan alatu, *Nafeesa* gani take duk haduwan palonta ba komi bane akan wannan, ita kanta *Samra* ba karamin burgeta yayi ba duk da tasaba yawon kasashe tana ganin wanda sukafi wannan din, but daga ganin wannan kasan ba karamin '''yar gata''' bace me shi. kallon juna sukayi, cikin 'kasa da murya *Samra* tace
"Wow kinga wani palow? tabb dijam.. Kice mijinki ba 'yar karaman gida ya aura ba, uhm uhm abin ba'a cewa komai".
Yamutsa fuska *Nafeesa* tayi tanemi daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun tazauna, itama din *Samra* zama tayi "kana tad'aga murya tana kwad'a sallama
jimmm kadan *Baby* tafito daga ita sai wani 'yar yaloluwar jan riga da kadan tawuce gwiwa, ta saki gashinta ya saukar mata har gadon bayanta, ga duk kan alamu barci takeyi suka tasheta " domin sai mutsitstsika idanu takeyi. Tun fitowarta suka saki baki suna kallonta, yayinda itama tabisu da kallon rashin sani batare da taji kunyan fitowa ahaka ba, 'karisawa tayi tazauna still tana kallonsu tace
"Sannunku da zuwa".
Bayan da tafad'ad'a fuskarta da beauty smile dinta. *Samra* ce kadai ta'amsa tana murmushi, ita kuma *Nafeesa* dauke kai tayi cike da bakin cikin ganin kyawun *Baby,* ita sai ma gani tayi kamar taqara kyau ne duk da uban raman da tayi
Amarya baki gane mu ba ko? Ni kawar abokiyar zamanki ne, shine nace tarako ni mugaisa naga Amarya.
*Samra* tafadi hakan face dinta dauke da murmushi..
*Baby* jin hakan yasa takalli *Nafeesa* dake faman hura hanci tana yamutsa fuska, duk da bata ta6a ganinta ba taga kamannin *Al'ameen* atattare da ita, hakan yatabbatar mata da cewan itace dayar kishiyar nata.Hmm ashe shiyasaka naga tana wani shashshan kamshi, uhmm aikin banza kawai.
Duk acikin ranta *Baby* take wannan maganan still idanunta akan *Nafeesa* suke, kafin tamaidasu kan *Samra* tanaci gaba da murmushi tace
"Allah sarki.. Ai dayake bamu ta6a haduwa ba, bari in kawo muku ruwa".
Tashi tayi tanufi wajen fridge tadauko roban '''FARO''' daya da kwalin jus tahado da cups tazo ta'aje asaman center table " kana takoma tazauna tace
"Bismillanku ko".
*Samra* ce kawai tatsiyaya jus din tasha, *Nafeesa* kuwa ko kallon wajen batayi ba. *Samra* sai janta da hira takeyi ita kuma tana mata murmushi batacewa komai, *Nafeesa* ganin dai *Samra* ba tashi zatayi su tafi ba tamiqe tana fadin
Kinga tafiyana in kin gama shishshigin kin taho ke kadai.
*Samra* kallon *Baby* tayi suka had'a idanu tad'an yaqe hakora tace
"To Amarya mun gaishe ki sai gani nagaba kuma".
Tom nagode kigaida gida.
*Baby* tace hakan alokacin da kwakwalwanta ke harbo mata maganganun *Muhsina*
sai da suka fita part din ne *Samra* take cewa
"Hmm gaskiya mijinki ya iya za6en mata kyakykyawa da ita, wow wlh bazan 6oye miki ba ta burgeni matuqa, wannan har ma tafi dayan kyawu sosai, wa take da suna ma? Yawwa *Ummee,* duk da ina ganinta beauty ashe ga wacce tafi ta, hm haba ashe yaga yarinya me kyau dole yakwallafa rai ya auro ta, ko ni da nake mace ta burgeni bare shi".
*Nafeesa* da take faman hararanta tace
"To me kike nufi? Kinaso kice min ni ce kadai bani da kyau acikinsu ko?"
'Yar dariya *Samra* tayi tace
"Haba dai a'a wlh, karki manta fa kyawunku ke da *Baseera* yaja hankalina alokacin da nafara ganinku a school har nanemi yin kawance daku, sbd ni inason me kyau dan haka duk inda nagansu sai naso naqulla alaka dasu, amma dai maganar gaskiya zan fadamiki dole *Al'ameen* yamace akan wannan yarinyan " sabida kowa yaganta sai ta burgeshi tashigan masa rai, wlh ko idanun nan takafa maka sai ta shanye ka, da alamu dai tanada gadara da jijji da kai, kamar dai tashin out side ko kadan bata da ta ido, ina tunanin ko dai 'yar uwata ce?"
Kamar ya 'yar uwanki?
Cewar *Nafeesa* da mamaki. Dariya *Samra* tasheqe dashi tace
"'Yar uwata '''KARUWA''' mana, duk yanda akayi tata6a karuwanci saboda haka kawai naga tamun kama damu".
Dariya itama *Nafeesa* tayi tace
"Kai amma gaskiya *Samra* kin bani dariya, but ina ganin gaskiyarki fa " domin nima tun wurin party dana ganta nasaka alaman tambaya gareta".
*Samra* tace "ko kuma dai ba 'yar nan bace, domin dai naga tanamin kama da irin '''BUZAYEN''' nan, kin gane su? Yauwa 'yan Niger, suna kama sosai tunda na zauna garinsu".
Ta6e baki *Nafeesa* tayi tace
"Can mata.. Ni kawai yanzu hankalina yaqara tashi da ita, wlh bakiji yanda nakara tsanarta cikin raina ba, dolene ma tabarmin mijina".
Hmm naga kuwa fa aikinki kamar yasoma ci, bakiga yanda tarame bane sosai? Dan dai tana da kyau ne yarinyan sai raman yaqara fito da kyawunta sosai.
Tsaki *Nafeesa* taja
Kinga mudena wannan maganan mukarisa ciki " mun tsaya nan muna abinda be da amfani.
Tace "no daga nan tafiya zanyi sabida inada inda zani, sai kuma naqara leqowa.
Ok muje to nataka miki zuwa wajen mota, tunda baki da aiki sai yawo kamar Leda sai kace ba yanzu kikazo ba, gwara dai muyi mu miqaki wajen *Mukhtar* ko ma huta.
*Samra* dariya tayi tace
"Karki damu very soon zaki neme ni kirasa tunda kin gaji da ganina, kibari dai muna dawowa daga tafiyan nan da zamuyi dashi nan da two month zamu san madafa".
Idanuwa *Nafeesa* tazaro tace
"Kai kawata kina wuta fa.. Yanzu tare zakuyi tafiya kenan?
Sosai kuwa, zan rakashi Gamarny wajen business dinsa daga can sai mu d'an yawata, eh kin gane ai?
Hmm lallai ne kawata, amma shine baki fadamin ba sai yanzu? Koda yike dama haka kike min sai dai naneme ki narasa sai kin dawo nake sanin inda kike zuwa, yanzu din ma nasan zumudi ne yasaka kika fadamin tunda tare da rabin-ranki zaki tafi.
Tace "i'm sorry kawalli Allah ba haka bane, amma dai zan gyara na dau laifina.
Uhmm.
Kawai *Nafeesa* tace. Daga nan sukai sallama tashiga mota taja, ita kuma takoma part dinta.
.
More comments More Post 🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️