🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*EPISODE (6)*
*(Ihsan)**YAU BIKI SAURA KWANA 15*
Ihsan ce riqe da hannun Ummee suka fito palow, tunda suka shigo tanemi xame hannunta sbd jin yanda gabanta ke faduwa "amma taqi sakinta har saida suka qarisa inda Al'ameen ke xaune, ya daura qafa kan daya yana latsa waya
Yaya gani, anty Baseera tace kana kirana
Ihsan tafada lokacin datake xama hannun kujeran dayake kai.. Ummee kam kwace hannunta tayi da qarfin tsiya taxame nan qasa taxauna kanta aduqe, cikin rawan murya tace
Yaya ina wuni?
Sai lokacin yadago kanshi yakallesu kafin yamaida ganinshi wajen Ummee, shi sai yau ma yaganta sbd ba ya xama ynxu agidan yana gyaran gidanshi acan ma yake kwana, sai dai yaxo gaishe dasu Dady, ta6e bakinshi yayi aranshi yace
Kamar wata munafuka, qauyancin kenan ai, amma ba laifi yarinyan kyakykyawa ce
Dago kai Ummee tayi caraf idanuwansu suka hadu dasauri tasake sunkuyar da kanta.. Muryan Ihsan sukaji tana fadin
Yaya gani nace
Ai na ganki
Yafada har yanxu idanuwanshi na kan Ummee
Me kikace ma Dady ne?
Ihsan tace cewa nayi yabada kudin dinkin aunty Ummee tunda ba'asa mata dinkakku acikin akwatunanta ba, shine yace xaimaka magana sai kabani
Miqewa yayi yana saka wayanshi a aljihu kafin yadauke kanshi daga kallonta yamaida ga Ihsan
Kibari xuwa anjima da daddare in nashigo xanbaki
To yaya
Ficewa yayi ita kuma Ihsan tashi tayi tawuce dakin Momy, tashiga da sallamanta.. Tana xaune saman gadonta ta'amsa mata, kusa da ita tanemi waje taxauna
Momy kayan Ummee xaki bani, xamu xa6a wadanda xa'akai mata dinki ne
Da Allah gafara can
Cewar Momy tana hararanta
Tashi kibani waje banxa wacce bata kishin 'yar uwanta
Baki taturo tamiqe xata fita, har takai bakin qofa takirata
Xo kikwashe min su anan, kikai can dakinki ku qarata
Dawowa tayi tanufi inda aka tsibire wasu kyawawan akwatuna guda biyar masu kalan ruwan xamba, na saman wanda xata iya dauka taja tafice,,. Ummee na xaune taxuba uban tagumi tana faman murmusawa tashigo jaye da akwati, ajewa tayi tsakar dakin
Aunty Ummee tashi muje mukwaso akwatunanki dakin Momy
Tashi tayi suka fice, koda sukaje ma Momyn bata dakin sai dai sunji qaran ruwa acikin toilet, kwasa sukayi suka maida dakin,. Ihsan kam xama tayi tsakar dakin tasoma xaxxago kayan "yayinda Ummee tasami waje gefenta taxauna talula tunanin hadadden guy din data gani