🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*EPISODE (11)*
*(The touch Heart)*Ina zaune adakina wajen qarfe 08:00pm ina duba books dina, Dadyna yashigo da jaka a hannunsa yamiqa min
Yi sauri Mamana kigoya wnn jakan
Ba musu na amsa nagoya ina kallonshi dason qarin bayani, harbin da naji anayi ne yasani tsananin mamaki da shiga firgici, sai yanxu nakula shima Dadyna a wannan yanayin yake, bud'e baki nayi da ninyan tambayanshi "naji ya janyo hannuna munfita, ta door back yabi dani yabude min yana kallona cikin hawaye yace
Mamana kimaxa kibar nan wajen karki tsaya ako ina sai Kaduna wajen Uncle dinki, inba hakaba xasu kashemin ke in kika tsaya anan, wannan jakan komi nawa ne na qadarorina aciki kuma nasan baxaki rasa kudi ba.. Kitafi kinji kitafi Mamana karki tsaya aka maki
Rud'u da tashin hankali yakasa sa nafahimci me Dadyna yake fad'i.. Harbin bindiga nasakeji da ihun Mamina tana salati.. Turani Dady yasoma yi yana qoqarin rufe qofan
Mamana Anas yaci amanarmu sabida dukiya, kitafi kar yakama min ke..
Builet din da aka sakar masa yasashi kasa qarisawa amma be dena qoqarin turani yarufe qofan ba, "ni kuma kuka kawai nakeyi ina riqe da qofan na tirje naqi matsawa, d'agowan da xanyi yayi daidai da hango Anas ya nufomu yana sake sakarma Dadyna halbi...
Cikin sheshsheqar kuka Baby tadago tafukan hannayenta
Doctor ahannuna Dadyna.. Dadyna mafi soyuwa agareni yacika, wlh bansan yanda akayi natsira daga hannun wadannan axxaluman ba, ni dai nasan natashi nafara gudu kuma wasu sun biyo ni, Allah ne kawai yatsirar dani
Sai dai abinda nakasa tunawa shine "saida nasauka Kaduna natuna cewa bansan anguwan da Uncle Bashir yake xaune ba, nayi dana sanin meyasaka ban tsaya a Abuja ba, tunda dole Uncle xaixo can sai mutaho tare "kuma in fadamasa duk abinda yafaru inyaso sai aka masu, kuma nayi dana sani da ban wuce police station kai tsaye ba, alokacin tunanina da hankalina baya jikina burina kawai nabar garin, aikin gama yagama baxai yiwu in qara komawa ba "that's why nayanke shawaran nemansa kawai tunda naxo
Ana cikin haka nahadu da yaya Yusuf yataimaka min, sai dai matsalan da nake samu na matarsa, duk wani aikin gidanta ni take sawa, abinda yasa nayi haquri najure naxauna nidai burina kawai nasami Uncle, na xa6i nayi tallan da tasamin ne duk sabida nafita neman Uncle
Aqarshe kuma sai nahadu da kai alokacin da nayanke qauna da samun farin ciki, kashigo rayuwata kuma kadawo min da farin cikina da narasa., ina matuqar qaunarka Al'ameen "ina sonka da dukan xuciyata, dan Allah karka bari narasaka kamar yanda narasa kowa nawa
Taqarake maganan tana kifa kanta saman laps dinta tana sakin kuka😭 me tsuma ran me sauraro... Al'ameen da idanuwansa sukayi ja dajin labarin mafi soyuwa a xuciyanshi