🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
*EPISODE (41)*
*(Ikram)*Agurguje plx.
*THREE YEARS AGO*
Abubuwa da dama sun faru acikin wannan shekarun, ciki kuwa har da haihuwar da Baby tayi (hmm wa yaga Baby da ɗa) ta haifi yarinyan ta mace kyakykyawa irinta sak, basu da maraba ko kaɗan kamar tayi kaki ta tofar, sunan mahaifiyarta aka saka mata RABI'ATU suna ce mata IKRAM, sosai yarinyan tayi wayau ba inda bata rarrafawa, su Momy da Dady suna zuwa ganinta sabida ba ƙaramin shiga ransu tayi ba, sosai suke ƙaunar yarinyan, shima yanzu Nurr ya girma sosai, in kaganshi tamkar Arif basu da maraba, gashi da tsawon ƙafa sai kazata ya kai 5yrs, duk wani so da ƙauna da Baby take ma Al'ameen yanzu duk ta ɗaura shi kan ƴar ta, sosai take mutuwar son ta, bata son ko ƙuda yataɓa ta, kullum tana nane da ita, yarinyan bata sabawa da kowa sai ita kaɗai, yanzu haka takoma makaranta wata biyu da suka wuce, taci gaba daga level 2 ɗinta, kuma da ita take tafiya, ɗai-ɗaikun rana ne zaka ganta bataje da ita ba.
Walid yayi aure shekara ɗaya kenan, ya auri Hajara ƴar Kano ce, ƴa ce wajen shugaban su kuma a Kano ɗin suke zaune, tana mutuwar son shi sosai, Dan haka Koda Babanta yasani sai kawai yabashi ita, yanzu haka kuma bikin Muhsina ya rage saura wata ɗaya kacal.
.... ....... ............
A fannin su Al'ameen kuwa sati biyu kenan da dawowar su, tun yana can yabada aka tsantsara mishi katafaren gida me hawa biyu, Dan haka Koda suka dawo a sabon gidan su suka sauka, kuma yana Gina asibiti nashi na kanshi duk da har yanzu be fasa aiki inda yake yi ba, abubuwa sai abun da yaci gaba a zamantakewar su da Nafeesa, sosai tasake mallake shi duk da wani lokacin in asirin yayi kamar zai karye sai asake wani, wani lokacin in yazauna sai yariƙa tunanin kamar yataɓa wani rayuwa, sau tari sunan Baby yana yawan faɗo mishi, har yariƙa tunanin matar shi ce baya ga Nafeesa kafin kuma yamanta ta gaba ɗaya, shi mallakan da akayi mishi yana sawa ne yamanta baya da wata Mata in ba Nafeesa ba, ita kaɗai ce yake ganinta a macen da zai iya so har ya iya auren ta, ba macen da take iya burge shi in ba ita ba, Amma da zai iya soyayya da wata be aure ta ba zai iya tuna ta, sai dai kuma ba ma zai iya son wata ƴa mace bane, kuma har yanzu basu sake haihuwa ba, da zaran ta sami ciki Boka ke bada jinin yaron wa Aljanu masu mishi aikin tun suna ciki.
ita ma Samra tayi aure wata takwas kenan, suna zaune anan Abuja ita da mijin nata, tariga taraba shi da kowa nashi.
Baseera ta haifi ɗanta namiji, ko arba'in ma basuyi ba, haka ma Ihsan ta haifi ɗa namiji, yanzu har tana da wani ƙaramin cikin.
.
*****
*THREE WEEKS*
"Wai Ruƙayya bazaki ƙyale yarinyan nan ba? Duk ta wani ishe mutane da kuka, fitinanniyar yarinya ita kuma, da wani sakakken baki kamar uwarta".