🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
*EPISODE (35)*
Tun sanda yaganta yagane aljanu ne akanta kuma su suka sanya mata ciwon, nan yasa aka kwantar da ita adaki yafara sauke mata al'qur'ani me girma, sai da yasauke mata duk kanta amma Baby bata ko motsa ba, hakan yatabbatar masa ba k'aramin gaggan aljanu aka had'ata dasu ba, nan yasoma karatu ba ji ba gani, wajen awanni kafin tafara ihu tana kururuwa, nan tatashi zata gudu k'attin maza biyar suka rik'eta tawatsar dasu, dakyar da sud'in ludayi k'atti goma suka danne ta, nan tadunga ihu tana fizge-fizge, ga uban gurnani da takeyi kamar zata tada gidan, ku kanku in kukaji sai kun firgita kun gudu, 😄 Malam yaci gaba da mata ruk'iya amma sunk'i su bayyana kansu, sai da sukasha wahala kafin sukace
"Malam dan Allah karka k'ona mu zamuyi magana".
"To ina jinku menene alakan ku da wannan yarinyan? Meyasa kuka shiga jikinta?".
'Daya yace
"Mu aiko mu akayi mushiga jikinta, amma wlh bamu da wani alak'a da ita".
"Har ku nawa ne ajikin nata?".
"Zamu kai mu saba'in".
"To ina son ku fadamin wa ya'aiko ku?".
"Gaskiya munyi alqawari bazamu fad'a ba, kuma bazamu sa6a ba".
"Haka kukace?".
Cewar Malam, suka had'a baki wajen cewa
"Eh haka mukace".
Yace "yanzu kuwa zan saku kuyi magana".
Nan yaci gaba da karatu su kuma suna ihu kamar zasu tsaga gidan, sai da sukaji wahala kafin su fara bashi hakuri
"Dan Allah Malam kayi hakuri zamu fita ajikinta, kuma bazamu sake dawowa ba, amma bazamu iya fadin wanda ya aiko mu ba".
Malam yace "kunyi alqawari in kuka fita bazaku dawo ba?".
"Eh munyi alkawari".
"Shikenan ku tattara komi naku kufice, karku sake ku dawo, duk sanda kuka dawo zan kashe ku gaba daya".
"Mun yarda, yanzu zamu fita".
*10min ago*
Baby tasoma atishawa kafin takwanta yarab tasoma barci, nan Malam yabada magungunan da zata rik'a sha, dana wanka dana turare da kuma na sha, sannan yak'ara jaddada musu subar barinta tana wasa da sallah, azkar tarik'a yi kullum, tarink'a zama da alwala koda yaushe, bayan wata daya sai su dawo su fadamishi ci gaban da aka samu, godiya sosai sukayi mishi kafin suka komo Kaduna, anan gidan Mama taci gaba da zama ana mata amfani da magungunan, cikin k'ank'anin lokaci sauki yasoma samuwa ga Baby, sosai take samun sauki kuma bata wasa da sallah, azkar safe da rana da dare, sallan nafiloli ba wanda yake wuce ta, in kukaga yanda takoma baza kuce itace wancan Babyn mara lafiya ba.
Sau biyu Ummee tana zuwa gaisheta, duk da itama bata jindadi, tana fama da ciwon ciki ad'an kwanakin, ranan da tadawo gaishe da Baby ne ciwon yamatsa mata sosai sai da Al'ameen yakaita asibiti, nan yaduba ta yagano tana dauke da cikin wata bakwai, mamaki da farin ciki su suka tabaibaye Al'ameen, ya ma rasa me zaiyi tsaban murna, ya akayi besan tana da ciki ba har wannan lokacin? Yasan hakan na da alak'a da samuwar ciwon Baby, kusan wata hudu kenan da be da nutsuwa kullum yana kan samun lafiyanta, wannan dalilin ne yasaka hankalinshi be kai gareta ba, kuma yasan ita kanta batasan tana da ciki ba, Allah sarki Ummee sai yaji tsananin kaunarta da tausayinta ya k'ara mamaye mishi zuciya
Koda yasanar mata zance muku tafishi farin ciki, sai da tayi kuka sabida tsaban murna da farin ciki, Al'ameen rungume ta yayi yana rarrashinta cike da tausayinta, maganad'isun sonta na k'ara tabaibaye shi, ji yake yi tamkar yataya ta kukan shima, tun daga ranan wani irin kulawa na musamman yake bata, ga wani irin soyayya da yake nuna mata kamar zai cinye ta.
***
Kamar yanda Malam yace bayan wata daya su dawo, wannan karon Al'ameen ne da Babyn suka koma, Malamin sai da yaqara mata ruk'iya yatabbatar babu su kana yaqara basu wasu magungunan, sukayi mishi godiya tare da ihsani me girma suka tafi, daga nan gidan anty Kharima sukaje, acan suka wuni har yamma kana sukai musu sallama suka wuce, Al'ameen be bar zaria ba sai da yaje gidan wani abokinsa Lecturer ne anan FCE Zaria Dr. Nafisudden Ahmad Shureim, ai kuwa ba k'aramin dadi Dr. Nafeesuddeen yaji ba da ganin abokin nashi, sosai itama Baby tasaki jiki da matarsa Sabra, kamar sun dade da sanin juna, sai dare suka shiga Kaduna.
Tun daga ranan aka fara shirye-shiryen komawar Baby dakinta, Al'ameen yasa an gyara mata part dinta fes sai zuwan Amarya yake jira, sai da tak'ara sati daya kafin takoma, hmm anan Amarya da Ango aka bud'e babin soyayya da ba'ayi ba ada, yanzu ne aka samu dama akeyi.
Sai da Baby tayi kwana biyar kafin Nafeesa tasan da dawowarta sabida bata zama agidan, tana koyarwa na NYSCE da tafara zuwa, lokacin da Al'ameen yake sanar da ita suman zaune tayi, hankalinta be qara tashi ba sai da yasake fadamata Ummee na da ciki har na wata bakwai, tsananin tashin hankali da firgici ta shiga har takoma bata jin me Al'ameen din ke fad'i, sai da yata6o ta yana fadin
"Wai lafiya Nafee na? Kalau kike kuwa?".
Firgigit tadawo hayyacinta tana binshi da idanu kafin tace
"Me kace ne?".
Kallonta yayi yace
"Yanzu baki ji me nace ba duk maganan da nayi?".
"Ahmm naji mana, ban daiji me kace bane k'arshe, amma kuma shine har matarka tana da ciki na tsawon wata bakwai baka ta6a sanar dani ba? Itama Amaryan tadawo har kwana biyar ina gidan bansani ba sai yanzu? Yanzu kenan kayimin adalci? Ko kuma dama bani da muhimmanci shiyasa baza'a sanar min ba?".
Kallon da yake mata na yanzu ya banbanta da wanda yasoma mata
"Hmm wai ke kina tunanin bansan me kike aikatawa bane iyee?".
Rasss gaban Nafeesa yafad'i, cikin tsanin tsoro da rawan baki tace