Part 44-45

107 6 2
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

_naji ra'ayoyinku masoyan Littafina kuma insha Allahu zan yi ƙoƙarin faranta muku duk kanku, nagode_ ❤️

.

      *EPISODE (44- 45)*
         *(The End)*

Da yamma Baby na kwance a ɗaki tana karatu, gefe kuma Ikram ce da kayan wasanta tana wasa Mama tashigo

"Baby kije kinyi baƙo yana nan a Palon Babanku".

Baby bata ɗago kai ta kalli Maman ba kuma bata da alaman magana

Mama tace "wai ba dake nake ba kina jina kinyi kunnen uwar shegu dani?"

Buga littafinta tayi saman gadon har sai da Ikram taɗan tsorata tajuyo tana kallonta, zumɓuro baki tayi tace

""Kai kai kai Mama, nifa nariga nace miki ba aure ne a gabana ba ya ake maida min da zance baya? Dan Allah ki sallami koma waye yatafi ni bazan iya fita ba".

"Yayi miki kyau ai, bari inje in faɗama Mahaifin naki kince bara kije ba tunda shi ya'aiko ni".

Kukan shagwaɓa Baby tasaki tana faɗin

"To kice ganinan zuwa".

Mama da har takusa fita cikin ɗakin tace

"Ƴar nema, sai ki hanzarta kar yagaji da jira".

Sai da Mama tayi minti biyar da fita kafin Baby taduro daga kan gadon tana ciccin magani, Hijabinta dake ajiye saman gadon taɗauka tazumbula shi har ƙasa tasumfuci Ikram dake ɓangale baki ganin uwarta ta tasaka Hijab tasan fita zasuyi, tana fitowa Palow Mama tabi ta da kallo

"Ba dai da yarinyan nan zakije wajen taɗin ba?"

Kamar zatayi kuka Baby tace

"Mama kinsan ko na barta kuka zatayi shiyasa zan tafi da ita".

Mama tace "kukan banza, kawo ta nan nariƙe ta".

Dasauri Baby tayi hanyan ƙofar da zata sada ta da ƙofar Palon Baba don bataso Mama taɓa ta mata shirinta, kaɗa kai kawai Mama tayi tunda tasan sarai taji ta tayi kamar bataji ba, aranta tace

"Gwara kikaita itama taga Ubanta".

Ahankali tamurɗa ƙofan tashige har da rufewa, juyuwan da zatayi tasauke idanuwanta akan shi wanda shima yazuba mata nashi idanun baya ko ƙyaftawa, kamar ko yaushe kamar yanda yasanta, kamar yanda take bata sauya ba tana nan hakanta sai dai girma da taƙara, kyakkyawar yarinyan dake hannunta yabi da kallo me kama da ita sak, sai dai kallo ɗaya da yayi mata yatabbatar da jininsa ce ita, wani irin ƙaunar yarinyan ce yasaukar mishi a zuciya, ahankali yamiƙe yafara takowa inda take wanda duk taku ɗaya yake tafiya da numfashin ta, a gabanta yaja yatsaya idanunshi akan ta kamar yanda itama tatsai da nata idanun ƙyam akanshi, babu abinda ke motsi a jikinta illa hawayen dake zubowa suna sauka akan kuncinta, hannu yasaka ahankali yasoma share mata hawayen still bata motsa ba duk da tana jin abinda yake mata but halin da tashiga da ganinshi  ta gaza tamotsa, hannu yasake miƙawa yaciri Ikram a jikinta, ita kuma kamar jira take tayanka uban ihu, sai alokacin Baby tasamu taƙyafta idanunta kuma daidai lokacin wasu hawayen suka soma sintiri acikin idanun, hannun ta dake rawa tamiƙa mishi ba musu yaba ta Ikram ɗin, shiru ne yagibta a tsakaninsu yayinda ita kuma takeso tatambaye shi

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now