🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
*EPISODE (13)*
Tunda suka shiga gidan take bin ko ina da kallo, ba wai dan qauyanci ba sai dan kyawu da tsaruwar gidan, gaskiya gidan yayimata duk da baikai nasu ba, tare suka jera har xuwa ciki
Ummee na xaune tana kallon maimaicin TARKON KAUNA atashar Arewa24 taga shigowarsu, dasauri tamiqe tanama Al'ameen sannu da xuwa idanuwanta akan Baby "yayinda itama take binta da nata idanun, cikin sakwannin da basu gaxa uku ba taqare mata kallo aranta tace
"Masha Allah".
Al'ameen ne yakatse masu gajeren tunaninsu dacewa
Ummee ga baquwa sunanku daya da ita amma Baby ake kiranta, xata xauna damu nadan wani lokaci ne that's why nakawota tunda kinga Nafeesa tana fama da kanta, ki sauketa wancan dakin bari nayi sallah nadawo
Kallon Baby yayi da itama takarkato kanta gareshi, murmushi yasakar mata
My Feenah bari naje sallah, take care of your self kinji?
Gyad'a masa kai tayi tana maida masa da martanin murmushin har yafice tana binshi da idanu "kafin tajuyo ga Ummee da takafesu da idanu tanajin tsananin kishi ya tokareta, dakyar tadaidaita kanta tare da qirqiro murmushi tace
"Muje to".
Bin bayanta tayi har xuwa dakin da xata xauna, one bedroom ne da toilet aciki komi akwai na buqata, xama Baby tayi agefen gadon tare da xame jakanta ta'aje, kallonta Ummee tayi tace
"Kina buqatan wani abu kuma? Ina nufin ko akwai abinda xan nunamiki?"
No bana buqatar wani taimakon ki, kije kawai nagode.
Baby tace da ita lokacin data miqe tashige toilet.. Kad'a kai Ummee tayi kamar qadangaruwa "cike da sanyin jiki tafice tana rufo mata qofan, dakinta tashiga tafada saman gado tana lumshe idanuwanta xuciyanta cike da wasi-wasin wadannan mutane
Tabbas kallo daya kaimusu xaka gane akwai wani abu a tsakaninsu "to amma yace ita din baquwa ce?
Wani sashe na xuciyarta yace
"To ke banda abinki meye na wannan tunanin? Yaushe ma ya aureku dakike tunanin akwai alaqa a tsakaninsu? Ko kin manta Nafeesa ce xa6inshi ke kuma qaddara ce tahada ku?,, to ita kuma wannan fa"?
Shiru tayi tare da daura hannunta saman fuskarta, tajima ahaka tana saqa da warwara kafin tamiqe tafada toilet, alwala tayi tafito ta tada sallah, bayan ta idar tana xaune tana laximi Al'ameen yashigo da sallama ta'amsa mishi
Ummee me kike buqata xamu fita da Baby shopping? Zata siyo kayayyakin da takeso.
Kanta asunkuye tace
"A'a yaya bakomi, kudawo lafiya".