Part 29 The Friends

30 1 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat Ismail lawal
          *(Nafeesat jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

 
*3irls with the same name*❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Ismaeel Lawal*

*GARGADI*
_Ban amince asauya min littafi ba. Duk wanda yasanja min shi da Allah_

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

*Episode* (29)
*(The Friends)*

*WASHE GARI*

Wajajen 11:00am *Baby* na xaune a palow tatasa t.v gaba tana kallo sai jin qaran bude gate tayi sai kuma hong da diran motoci, ahankali tamiqe tanufi bakin windo tad'aga cotten tana leqawa, " motoci uku ne duk da na *Al'ameen* , gaba dayansu suka fito har dashi, abokan aikinshi ne su hudu *Doctor Gali* da *Doctor Abdul* sai *Doctor Blus* da kuma *Doctor Anwar* ,.. " ganinsu yasa tatuna da yafadamata xai kawo abokansa tayi musu girki, sam ta manta sai yanxu data gansu, kasa motsi tayi awajen saboda batasan me xatayi ba, tana kallon *Al'ameen* na nuna part dinta sai kuma taga yanuna part din *Nafeesa* suka nufi sashin.

Dasauri tasaki labilen tanufi kichen aguje jikinta sai rawa yakeyi, gaba daya tarasa ma me xatayi tabi nan tabi can, dakyar tatsai da hankalinta tadauko tukunya tawanke ta'ajiye kana takunna gas tadaura tukunyan, mangyada tadauko tatsiyaya taqara dauko albasa komi cikin sauri takeyi kamar xata tashi sama, cikin minti goma ta harhada komi cikin tukunya har taxuba ruwa yasoma xafi, kayan miyan ma yayyanka shi tayi da wuqa taxuba, taxaxxage taliya biyu cikin farantin rover tana jiran sanwarta yatausa taxuba

Lokacin su *Al'ameen* sun shigo har ya saukesu a palow yanufi dakinta, abude yaga qofan yashiga but sai dai yaduba babu ita ciki hakan yasa yanufi kichen, " tana tsaye gaban girkin nata jikinta sanye da milk din doguwar riga but da kadan yawuce gwiwa kuma hannun siriri ne, kanta ko dankwali, " a jikinta taji ana kallonta tayi saurin juyawa, hada idanuwa sukayi tayi saurin kau da kai sai dai gaba daya ta dauke wuta, kallonta kawai yakeyi daga sama har qasa na tsawon daqiqu kafin yasoma takowa yana nufota " saurin kallonshi tayi ganin yanufo ta hankalinta yayi matuqar tashi har gumi yasoma tsatstsafo mata, ga wani bugawa da xuciyanta yakeyi har *Al'ameen* na jiyo bugawan, dab da ita yatsaya tayi saurin sauke kanta qasa tana ja baya, " ahankali yadaga hannunshi yanufi fuskarta ko me yatuna yajanye hannun yakai kan tukunyan yabude, xaro idanuwanshi yayi cike da mamaki yakalleta

"Me xangani haka my *Feenah* baki gama girkin ba?".

Yafada hankalinshi atashe tunowa da yayi har abinci *Nafeesa* takawo musu sukace baxasu ci ba yau ranan Amarya ce abincinta xasuci, haka ma *Ummee* sai da takawo musu me rai da lafiya amma sukaqi ci, gashi yanxu Amaryan batayi komai ba

Wannan wani irin abin kunya ne *Baby* tajawo min? Ya xanyi?

Yafad'a aranshi yana tsareta da idanu

"Meyasaka bakiyi girkin ba sai yanxu?".

Yasake tambayanta cikin sanyin murya duk da ranshi a matuqar 6ace yake amma baxai iya nuna mata ba koda afuska ne... Cikin dauriya da danne tsanarshi da takeji tace

"Kayi.. haqu..ri wlh na..man..ta ne".

Shiru yayi yana kallon d'anyen naman dake ajiye a Vowel " ita kanta ma batasan ya xatayi dashi ba sabida tasan ba yanda xa'ayi a qurarren lokaci tasarrafa shi

"Ok yakamata kije kitarbesu koda da drinks ne sai ku gaisa kafin kigama, kibar wannan Naman xanbi ta wannan qofan in aiki *Bala* yasiyo gashashshe sai kixuba musu".

Gyad'a kai *Baby* tayi tafara takawa xata fita, cikin sauri *Al'ameen* yadakatar da ita, cak tatsaya batare da tajuyo ba

"Kitsaya bari in dauko miki hijabi".

Yafad'a yana wuceta yafita... Kafin yadawo har taxuba taliyan, amsan hijabin tayi taxumbula shi har qasa tabi bayanshi suka fita

"Hmm ni wlh har ina tunanin mutashi mutafi tunda wadannan masoyan sun manta damu suna can suna soyayyarsu".

*Doctor Abdul* yafadi hakan yana dariya

"Ai ni shiru nayi but araina ina tunanin awanni nawa xamuyi anan xaman jiransu".

Cewar *Doctor Blus* kenan.. *Doctor Gali* yace

"Ku fa kunsan gidan Amarya kukaxo " kuma kunsan dacewa Amarya bata laifi, ni dai banga laifinta ba dan tariqe mijinta, ai ni aganina sun fito da wuri".

Dariya sukayi... " xama *Baby* tayi hannun kujeran da *Al'ameen* yaxauna " tagaidasu cikin fara'a, suka amsa suna xolayanta ita kuma sai murmusawa takeyi bata cewa komai, tashi tayi tanufi frige takawo musu kayan motsa baki kana takoma kichen taci gaba da duba girkinta

Shima *Al'ameen* tashi yayi yanufi kichen din gaba daya suka fashe da dariya suna tsokanarshi, baibi takansu ba yashige yabi ta qofar baya yafita ya aiki *Bala me gadi* yasiyo mishi gashashshen Nama, cikin mintuna qalilan yakawo mishi kasancewar ba nisa da inda ake saidawa, dawowa yayi yabata yakoma palow, " ita kuma sai da tatabbatar girkin yasoma tsotsewa sannan taxuba tajuya tarufe yad'an turara kafin tasauke, xuba musu tayi takai musu " sai da tatabbatar ta tanadar musu komi kafin tashige dakinta

Ataqaice dai basu bar gidan ba sai wajen biyu saura bayan sunyi sallama da ita, tare da *Al'ameen* suka fice ita kuma taxo tatattara plates din takai kichen, " tsayawa tayi tana kallon kayan wanke-wanken da suka taru har dasu koololin da *Ummee* take sawo mata abinci, " ajiyan xuciya tayi tabugi goshinta da tafin ✋ hannunta afili tafurta

"Ohh ni *Baby* ko me ke damuna? Sai tara wanke-wanke nakeyi ban ta6a tunanin wankewa ba, Allah yashirye ni".

Cikin qanqanin lokaci tawanke takifesu tafito palow, tsintsiya tadauka tasoma sharewa, bayan tagama tayi moping tasaka turaren wuta nan da nan qamshin dadi yasoma fesowa " dama gashi akwai qamshi dake tashi na sabunta" ita kanta sai taji dadi acikin ranta domin tunda taxo bata ta6a sharewa ba duk da ba wani datti amma dai akwai qura " dakinta tashiga nan ma tashare tagyara ko ina tasa airfreshna nan take qamshin dakin yasauya salo.

Wanka tashiga tayi tafito tashafa lotions kadai ajikinta tanufi wadrobe taciro wani baqin yadi me laushin gaske, jikin an mishi xanen flower da pich and brown colour " dinkin riga da wando ne, rigan iya cinya yatsaya mata, wandon burgujeje me fela, sai d'an siririn dankwalinshi da taxixara akanta, gaba daya tulin gashinta dake tsakiyan kai abude yake " haka ma gashin goshinta, ba qaramin kyau *Baby* tayi ba kamar kasaceta kagudu duk da ba makeup a face dinta, tahadu sosai sai tashin qamshi takeyi

Wayanta tadauka tanufi palow tana tafiya tana dannawa, wajen t.v tanufa takunna takoma 3 sitter takwanta taci gaba da latsa wayanta batare da tabi takan kallon ba, tana cikin danna wayan barci yadauke ta.

.

***

Cikin barci *Baby* tasoma juya kanta tana mutsu-mutsu nan da nan tahada gumi duk da pan da a.c dake aiki xikin palon, " *Al'ameen* dake xaune gabanta ya qura mata idanu ko kyaftawa bayayi yana ganin yanda tasauya mishi " face dinshi cike da damuwa..,  ganin halin da take ciki ne yasashi matsowa yana kiran sunanta, har yanxu idanuwanta arufe suke kuma bata dena juya kai ba " ga hawaye da suka fara xiraro mata suna sauka gefen kunnenta, nan hankalinshi yafara tashi yai saurin daura hannayensa akanta yana girgixata yana kiran sunanta

Cikin qanqanin lokaci *Baby* tasoma mimmiqewa tana banqarewa sai kuma jikinta yasaki tadena motsi, xuwa lokacin hankalin *Al'ameen* yayi qololuwan tashi yarasa ya xaiyi still yana kiran sunanta, miqewa yayi yasungumeta yai waje da ita " motanshi yanufa yasakata a back sit yashiga yaja yanama me gadi hon

Fitowar *Nafeesa* kenan daga part dinta taci ado tana goye da *Arif* , tahangi *Al'ameen* dauke da *Baby* " tana tsaye nan har yafice tasaki wani shu'umin murmushi aranta tace

"Lallai ne nafara gazgata maganan *Malam,* hmm just to begging".

Itama motanta tanufa tashiga tafice daga gidan.

.

_dafatan anyi sallah lafiya fans? Allah yamaimaita mana amin_

Jun [2020]

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now