Part 27 Muhsina

37 3 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

.

      *EPISODE (27)*
        *(Muhsina)*

A kwanakin nan dai da sukayi *Al'ameen* yagaxa gano me ke faruwa? Meye matsalan *Baby* take gudunshi, tun abin na bashi mamaki da dariya har yasoma bashi tsoro, bata ta6a bari sun hadu ba, ko da zai kwana ya wuni a palow yana jiran tabude kofa baxata ta6a fitowa ba, yayi magiyan yayi har yagaji amma ina ko magana bata mishi, da xaran taji motsin yafita xata fito takwashi drinks da ruwa dake frij takai dakinta, shi xata wuni tana sha ko kichen bata iya xuwa kar yaxo yatarda ita, ko kadan bata kaunar su hadu batason taganshi, ji take kamar takashe kanta sabida tsanan datake mishi, ba abinda take yanxu sai barci kullum cikin kasala take ga gajiya da takeji ajikinta kamar ta wuni yin aikin qarfi.

Hakan da *Al'ameen* yagani bata ta6a yin girki ba sai drinks da takesha that's why yadena xama jiranta sai tabude kofa sabida a tunaninsa ko takura mata yakeyi? *Baby* kuma hakan yabata daman fitowa palow yau sabida ita kanta batajin dadin xaman dakin, tana xaune a two sitter ta kwantar da kanta idanunta a lumshe, wlh baxakai tunanin *Baby* bace sabida xabgewan da tayi akwana uku kacal dama gata ba auki ba, tayi firi-firi da ita, tana sanye cikin doguwar riga sky blue, kanta ba dankwali sai gashinta data daure da bak'in ribom

Nocking taji anayi hakan yasa tabude idanuwanta tasauke kan qofan, bata motsa ba still kuma ba'a dena nocking din ba, muryan *Muhsina* taji tana kiran sunanta, dasauri tamiqe tanufi kofan taxare lock tabude " fuskarta kadai in kakalla xaka gane farin cikin da take

Ayyo ashe kina jina naketa nocking kinqi kibude min, ko Angon na ciki ne in juya?

*Muhsina* tafadi hakan cikin xolaya tana kallon *Baby* .. Ita kuma murmushi tayi tace

"Shigo mana, ba..ya nan..shi".

Tafadi maganan kamar me koyon magana cikin sanyin murya. *Muhsina* kallonta kawai takeyi ko kyafta ido batayi sabida mamaki, batare data furta komai ba tashige ita kuma tarufe kofan tabi bayanta, akan three sitter suka xauna still *Muhsina* kallon *Baby* takeyi kamar wacce taga sabon halitta

Wai *Baby* ciwo kikayi kika rame haka kmr naman jikinki ake diba ayi miya? Kinga kuwa yanda kika koma? Meke faruwa ne?

*Muhsina* take fadin hakan cikin tsananin mamaki da al'ajabi. 'Yar dariya *Baby* tayi cike da sanyin muryanta tace

"Kinji ki ke kuma da wata magana, in ba ciwo nayi ba kin ganni ahaka?"

Subhanallah..  Ke kuwa wani irin ciwo ne yaxabgar dake alokaci guda haka? Kamar wacce take amai da gudawa? Ni da naxo in ganki kinyi 6ul-6ul Amarci ya amshe ki sai in ganki ahaka?

Hmm ciwon kai nake fama dashi tun ranan da naxo.

Ciwon kai? Mijin naki ya dubaki ne ko kunje asibiti?

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now