🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3grils are the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.'''Wannan shafin naki ne yar uwa qawata. Ako INA nake inhar xan daga alqalamina to ke kike fara fadomin arai.. Kin kasance masoyiyar littafaina shiyasaka nake alfahri dake. Baxan ta6a mantawa dake ba aduk halin da nashiga SA'ADATU .M. NASIR ana mugun tare''' 🤝 ❤
.
*EPISODE (20)*
*(Samra)*Nafeesa ce xaune saman gado ta rungume Arif dake ta sharan barci jikinta, yaron baxakace d'an watanni takwas bane yanda yagirma yai qatoto, kamanninsa da ubansa sai qara fitowa yakeyi har yafi mahaifinsa jan fata, " ko dan yana jariri ne? 🤷🏻♀.,, wayan dake hannunta tana latsawa yasoma ringing "dasauri tai answering call din takara a kunninta
Hmm ai fushi nake dake wlh, sai yanxu kikaga daman kirana? Kuma ni in nakiraki bana samu.
Daga can 6angaren Samra dariya tayi tace
"Ayya sorry qawata kin san ni kamar wutar nefa nake bani da tabbas, wlh bana qasan ne that's why kikaji wayata akashe, yanxum ma dawowa na kenan ko cikakken 3 hours banyi ba nace bari in kiraki, kinsan nadade banxo ba tun bayan suna".
Nafeesa tace hmm dama ai ke 'yar wulaqanci ne, wanda ma yace xaiyi abin kirki dake ai yajawo ma kansa ne, baki da aiki sai bin qasashe.
Samra na dariya tace
"Afwan dai qawalli tuba nake, kinsan yanayin harqallan namu " dole sai muna biya musu buqatarsu kafin subiya mana, kinsan Allah ba qaramin kudi nake samu ba duk akace miki nabar qasar nan, hmm kema kinsan sauran, " ba yanda xa'ayi inbi namiji wata qasa ace be jiqani da naira ba, shiyasa nakeson kema kishiga wnn harkan da tuni kin fantsamo gari but kinqi amincewa".
A'a ke dai da kikaga xaki iya sai kitayi, ni kam da aurena baxan iya wannan shashancin ba.
Cewar Nafeesa
To ai nace miki akwai matan aure a wnn harkan indai xakiyi din, abu me sauqi kina xaune agida ma xakiyi komai (hmm sharrin qawa kenan! Muguji qawayen banxa wlh.. Dan xasu kaimu su baro mu ne).
Yanxu dai mubar maganan nan tawuce, kinsan ko kadan banada ra'ayin bin mazaje awaje, tun ina budurwa ma banyi ba sai yanxu?
Nafeesa tafadi hakan tana yamutsa fuska
Ok mun bari, yakike kwana biyu ya Arif kuma? Ina fatan yanxu ya girma?
Lafiya lau gashinan yana barci.
Samra tace "aiko xan shigo ko dan naganshi, kinsan yaron yana burgeni wlh, xanso inga yanda yakoma yanxu".
Uhm aiko akwai labari fa, dama inason muhadu, amma xanso ni naxo nasame ki ne.