Part 26 Baby

43 3 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat Ismaeel lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

.


      *EPISODE (26)*
         *(Baby)*

Malam agaskiya aikin da kaimin bana tunanin yayi, domin ko kadan banga tsana a idanun yarinyan ba, hasalima sai so  da nagani, kuma kace ko kusa da ita baxata bari yaxo ba amma wlh malam ajikinshi ma naganta.

Nafeesa take fadin hakan lokacin da tagurfana gaban Malam. Baice mata komi ba sai janyo faranti dayayi, bayan yagama xane-xanensa yadago kai yana kallonta

Hajiya nayimiki aikinki kuma yaci, sai dai matsalan da aka samu yanxu yarinyan tana yawan ibada kuma tana axkar hakan yasa aikinmu yai rauni har yasoma 6aci, sai dai ba duka bane ya6aci da sauran tsanar shi a ranta,  yanxu me kikeso ayi kuma?

Malam asake saka mata tsanarshi arai sabida banason tashiga gidanshi, bana son ko kadan wani abu yashiga tsakaninsu har sanda xasu rabu don Allah Malam.

Hajiya bana tunanin xamu samu nasara akanta yanxu domin hankalinta nakan ibada.

Nafeesa ciro zoben hannunta tayi tamiqa ma Malam

Dan Allah Malam dan girman Allah karkayi tunanin bani da kudi ne ko nawa xan baka, wannan zinare ne da kudinsa yakai dubu dari biyar, ko ya zakayi banaso suyi rayuwan jindadi daga wnn daren, inaso arabasu banaso 'ya'yana su samu 'yan uba, banason mijina tare da ita, ji nake a xuciyata xata mallake min shi inhar ban rabasu ayau ba.

Dariya Malam yayi bayan da ya amshi zoben yagani

Shikenan so kike akashe ta ko so kike a haukata ta?

Xaro idanu Nafeesa tayi

Kisa Malam? Gaskiya rashin imani na be kai nan ba.

Wa yace miki dama kina da sauran imani tunda har kika hada Allah da wani kike nema wajen wanin Allah?

Malam yafada yana babbakewa da dariya

Yarinya in xakiyi aiki kiyi aiki, domin in kika tsaya tunanin imaninki ko makomarki to baxaki ta6a cin nasara ba, kin riga kin soma aiki don haka ki qarisa shi saboda dole xaki girbi abinda kika shuka in bakiyi anan ba acan lahira xaki sami makomarki, gwara kiyi da hujja kisan kin aikata laifi an miki hukunci.

Cikin sanyin murya Nafeesa tace

"To amma in ka aikata hakan xa'a iya xargina? Kuma inka haukata ta xata iya warkewa nan gaba asirina yatonu".

Malam yace in kinaso xan iya kasheta kuma ba za'a ta6a zarginki ba.

Taya kenan Malam?

Wani qunshin leda yadauko yana kallonta

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now