Part 28 Al'ameen

34 2 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱
      *NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
          *(Feenah jikar lawal goma)*

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''

         *⚜{{H.Q.W.A📚}}*

     
*3girls with the same Name* ❤

*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat*

*SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal*

*GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah

*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.

.

.

      *EPISODE (28)*
       *(Al'ameen)*

*Baby* daukan abincin da *Ummee* takawo tayi tashige dashi daki tarufo qofan, kwanciya tayi saman gado nan da nan barci yadauketa, har *Al'ameen* yadawo bata tashi ba, kamar koda yaushe sai da yabuga kofanta yaji shiru kafin yawuce dakinshi cike da matsanancin damuwa, kayan jikinshi yatu6e yashiga yayi wanka kana yafito yashirya cikin blue T.shirt da baqin wando yafeshe jikinsa da turare yafito yanufi part din *Matansa* domin duba lafiyansu, bashi yadawo sashin *Baby* ba sai da yayi isha'i a masallaci " koda yakoma daki ma bai kwanta ba sai da yagama aikinsa cikin Computer kafin yatashi yafara jero Nafiloli.

Karfe 10:25pm na dare *Baby* tafarka, abinci taci tayi wanka tadauro alwala, agaggauce tayi sallan magrib da isha'i tasake komawa takwanta.

Ba ita tatashi ba sai da sha daya na safe tayi 11:00am,  kasancewar tatashi da yunwa sosai sai da taje kichen tad'umama taliyan da *Muhsina* tabari bayan data tabbatar *Al'ameen* baya nan, daki takai taci taqoshi tashiga wanka bayan tafito tayi sallan subahi da batayi ba " sannan tanufi wadrobe don daukan kayan da xatasa, " kanta ne yasoma sara mata nan da nan tasoma jin jiri dasauri tadafe jikin wadrobe din da hannu daya " dayan hannun kuma takama goshinta gam, wani axababben ciwo takeji da baxata iya misalta shi ba, ji takeyi kamar xa'a raba mata kan biyu kwanyanta yafito, dasauri tarumtse idanu sabida axaban dataji ya tsarga mata idanu

Tsananin daurewa *Baby* tayi daga qarshe tafashe da kuka taxube nan qasa tana juyi, ta qanqame kanta da hannu biyu tana kiran duk sunan dayaxo bakinta har da sunan iyayenta, juyi kawai takeyi tana kuka har batasan sanda zanin data daura yakwance ba " hijabin jikinta kuwa tacire tayi wulli dashi, gaba daya tagama fita hayyacinta batasan ma me takeyi ba, kuma idanuwanta arufe suke ruf sai hawaye dake ziraro mata ta gefen kunnuwanta 👂

Sai da tashafe awanni biyu ahaka kafin tafara dawowa hayyacinta, ahankali tasoma bude idanunta da suka soma washewa daga canxa kalan da sukayi na kore, tashi tasoma yunqurin yi sai dai ko kadan bata da qarfin sisi sai tsananin kasala da takeji, tadade ahaka kafin tasamu tamiqe tana kallon jikinta da babu kaya, mamaki ne yakamata ya akayi haka? Sai dai kuma bata tsawaita ba da tunaninta tabude wadrobe taciro abaya blue black colour taxira ajikinta takoma saman gado takwanta, barci ne yadauketa sai dai bata dade ba sallaman *Ummee* a tsakar palow yatashe ta.

Ahankali tamiqe cike da kasala tashiga toilet tawanko fuskarta tafita palow, " *Ummee* na xaune da abincin da takawo mata, sai da suka gaisa kafin tamiqa mata abincin *Baby* ta'amsa tayi mata godiya, " *Ummee* bata tafi ba xama tayi nan tanata mata hira, duk da *Baby* bata wani magana but taji dadin ganinta dama xaman kadaicin ya isheta.

Bayan *Ummee* tatafi tashi tayi tanufi dakinta tadauko wayanta tadawo palow takwanta tasoma neman layin *Mama* , sai da suka gaisa suka dan ta6a hira kafin takashe takira *Baba* shima gaisawa sukayi daga qarshe takira *Walid* , sun dade suna hira *Baby* har da dariya kamar ba itaba, sallama sukayi tahau facebook taci sa'a friends dinta na kai *Ikilima* da *Saudat,*  nan suka fara hira cikin nishadi, sai jin sallaman *Al'ameen* tayi yashigo, batasan sanda tawuntsilo akan kujeran ba tatashi cikin sauri tanufi hanyan dakinta, shima din cikin sauri yataka yasha gabanta yaxube yayi kneeldown yariqo gefen riganta, cakk tatsaya tana sauke numfashi cikin sauri, tadauke kanta xuwa gefe, " kallonta *Al'ameen* yayi baisan sanda xuciyansa yakarye ba hawaye suka soma zubo masa

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Wai *Babyna* ce takoma haka acikin gidana amma bansani ba?

Yafada afili yana qara qaremata kallo. Sauke kanta qasa tayi xuciyanta na faman bugawa kamar xai faso yafito

Dan girman Allah *Nafeesa* kifadamin meyasaka kika xa6i ki quntata mana akan laifin da bansan na aikata ba? Meyasa kika xa6i muyi wannan rayuwan mara dadi me cike da quntata? Bayan kinsan munyi ma junanmu alqawarin farin ciki a xaman takewarmu me dorewa na har abada? Me nayimiki ne *Nafeesa* meyasaka kika sauya? Wani laifi nayi miki da har kika kasa yafemin? Ashe dama ba son gaskiya kike min ba? Duk kaunar da kika nunamin da farin cikin da kika bani abaya ashe duk yaudara ne? Tunda kin kasa yafemin, kin kasa yarda muyi rayuwan jindadi, duk burin da mukaci kin rushe shi.

Wlh wlh my *Feenah* ina kaunarki, kaunar da nake miki shiyasaka baxan iya xaukan mataki akanki ba naxira miki ido naga iya gudun ruwanki, ashe bani kadai kike axabtarwa ba kikalli kanki kiga yanda kika koma duk adalilin quntata mana da kikeyi, ni kaina nakasa samun nutsuwa kullum cikin fargaba nake da tsananin damuwa, meyasa baxaki fadamin abinda nayi miki ba? In wani abu ke damunki meyasa baxaki fadamin muxauna mu fuskanci matsalan ba? Ko dan kinga na mutu a qaunarki ne kike min haka? Iyee tell meee?

Yaqarake maganan da rawan baki har yanxu hawaye na xubo mishi, ya tsareta da idanu yana jiran yaji tayi magana amma me? Sai ma janye riganta tayi tara6a shi xata wuce har lokacin bata kalli inda yake ba, sake ruqo riganta ta baya yayi taja tatsaya tana runtse idanu cikin dauriya

Kin za6i muyi wannan rayuwan ko *Baby?* kin fison naxauna cikin baqin cikinki damuwa yakashe ni ko?

Shiru tayi hawaye na gangaro mata

Shikenan baxan takura miki ba, but kisani ina qaunarki baxan ta6a iya rabuwa dake ba, amma kiyimin alqawari baxaki rabu dani ba xan iya xama dake ako yaya ne har lokacin da xaki sauko, nayi miki alqawari xan xauna dake baxan takura miki ba kinji? Kinji my *Feenah?*

Ahankali tagyada mishi kai

Dan Allah kiyimin wani alfarma, gobe friends dina na Hospital xasuxo dan Allah na roqeki kifito ki tarbesu kinuna ba  wani abu dake faruwa, inason kiyi musu girki " ko ba komai xanyi farin ciki dan Allah kiyimin wannan alfarman kinji?

Nan ma gyada mishi kai tayi taja riganta yasaki yana fadin

"Nagode".

Cikin sanyin murya.. Ita kuma tashige daki tagarqame, *Al'ameen* yadade awajen yana bin kofan da kallo kafin yatashi yashige daki yafad'a saman gado yana sauke numfashi take nan yadulmiya duniyan tunani.

Itama *Baby* hakan take wajenta, saman gado tafada tana jera ajiyan xuciya " sai kuma tafashe da kuka tana riqe qirjinta, cikin kuka take fadin

"Wannan wani irin bala'i ne? Meyasaka tsana da So yake nuqurqusan xuciyata? Wai menene laifina? Waye ne yake bibiyan rayuwata? Ina sonshi na matuqar tsanarshi bana son ganinshi, ji nake kamar xan mutu sabida tsanarshi.

Taqarike maganan tana kuka sosai, tadade tana kuka kafin tayi shiru tana sauke ajiyan xuciya, aranta tanason tashi tayi sallah taroqi Allah amma bata iyawa, da xaran tadauko al'qur'ani ko Hisnul Muslim xata karanta yanxu xata soma jin kanta na mata xafi idanunta na mata ruwa-ruwa yana xugi takasa sarrafa harshenta ga gajiya da xataji ya saukar mata kamar ta dauke dutsen dala, ko aranta tayi ninyan yin addu'a sai taji tana jin xafi a xuciyanta nan da nan sai tamanta me takeson yi!!!

.

_insha Allahu sai bayan sallah zamu ci gaba, dafatan za'ayi sallah lafiya? Kar amanta idan anci nama awanke hannu 🤝 kuma INA jiran nawa naman sallan, kar aci amanta da Nafeesa, love you Fans_ 🤞🏽 🥰

[2020].

NAFEESAT 2020Where stories live. Discover now