🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne.*Wannan shafin nakine MAMANA. Bani da tamkarki aduk kan duniyar nan. I love you with all my heart* ❤💕💘💟
*EPISODE (10)*
*(The LO❤e)*Tun da Al'ameen yakai Beby gida, tun daga ranan sai yasai abinci wajenta, ada dai sai dai yaga su abokan aikinsa suna sayen abinci "har wani lokacin yayita musu fad'a, sai gashi shima yajone dasu kuma shi yayi hakan ne becouse of Beby, shi dakanshi yake xuwa yasiya wani time din kuma tana kai mishi har office
Ahankali Al'ameen yasoma shige mata yayita janta da hira, to dama itama din rayuwan kadaicin ya isheta bata da wani abokin hira ko wanda xata fadamishi damuwanta, hakan yasa tasaki jiki dashi tadauke shi tamkar abokinta gaba daya tagama yarda dashi, shaquwa kuma tasoma shiga tsakaninsu har takai ga sun fallasawa junansu sirrin dake ransu, ma'ana dai soyayya me qarfin gaske yashiga tsakaninsu wanda sukejin baxasu iya rabuwa da juna ba komi rintsi, duk wani qunci da damuwa da Beby take ciki gaba daya sun kau xuwan Al'ameen cikin rayuwarta bcox tunda take bata ta6a shiga yanayin soyayya ba, har mantawa ma takeyi da abinda ke gabanta, yanxu tadena ma fita neman uncle dinta gaba daya soyayya yarufe mata idanu, Al'ameen ke kaita gida kullum inta tashi daga tallanta
***
Yau Beby bata samu xuwa talla ba sabida Hafsa tatashi da xaxxa6i "kuma dama itace qarfin girka abincin, domin kuwa intace Beby ne xatayi sai dai tasata asara 😃
Yau Al'ameen gaba daya yadamu da bai gantaba "kasa jurewa yayi yaxari keeys yanufi gidan, koda ya'isa yaro ya'aika yakira mishi ita, lokacin da yaron yashiga gidan Hafsa na xaune tana shirin yin alwala yafad'i saqon
Jar uba.. Yarinyan nan har tafara taramin qattin banxa agida? Aiko baxai sa6uba, kai je kace baxa taxo ba
Hafsa tafadi hakan cikin masifa... Beby na xaune cikin daki "jin abinda Hafsa tace tayi saurin fitowa
Kai kace ganinan fitowa
Tafada hakan tana saka hijab dinta... Da masifa Hafsa tace
Gidan uban wa xakije ina magana kina tafiya?
Cikin fushi Beby tajuyo xatai magana kuma ko me tatuna.. Sai tajuya fuuu tayi waje xuciyanta na mata xafi, wajen motan taqarisa tabude tashiga
Lafiya my Feenah? Wa yata6a min ranki ne?
Cewar Al'ameen da shima yashiga cikin damuwa ganin sanyin ranshi a wnn halin
Ni da wannan Hafsan ne doctor, but wlh billahi nakusa daukan mataki sabida naga bakinta nason kauce hanya, duk ranan data sake taxagarmin iyaye sai na bata mamaki sai dai in su koreni agidansu
Beby tafad'a cikin fushi kamar Hafsan ce agabanta... Al'ameen da yasaki baki yana kallonta da tsananin mamaki yace
Bangane ba my Feenah; Wacece kuma Hafsa?kimin bayani dan Allah
Kallonshi Beby tayi, saima ynxu hankalinta yadawo jikinta, cikin sanyin murya tace
Bakomi my Doctor; share xancen nan
Haba my Feenah ya xa'ayi kice inshare bayan naganki cikin damuwa? Ko dai dama baki daukeni da wani matsayi bane a xuciyanki? Kifadamin me yahadaki da Hafsan "kuma meyasaka kike cewa saidai su koreki agidansu?
Jimmm Beby tayi kamar baxatai magana ba sai kuma tafara da cewa
Shikenan Doctor, tunda ka buqaci kasani xan sanar dakai ko ni wacece
Juyowa tayi takalleshi sai kuma tamurmusa har kumatunta na lotsawa "taci gaba da fadin
Becouse na aminta da kai, na yarda kaxamo sarkin dake mulkan xuciyata
Numfashi taja kafin tasoma da fadin
***
*WACECE BABY NAFEESA*
Ni sunana *Nafeesa Ismaeel Audu,* mahaifina Alhaji Ismaeel Audu da qaninsa Alhaji Basheer Isah haifaffun qasan Zazzau ne, sunan mahaifiyarsu Hajiya Nafeesa wato kakata, dafari kakata ta auri Alhaji Abdullahi Audu tahaifi Dadyna dashi sai yarasu "kafin ta'auri Alhaji Isah tahaifi qanin Dadyna Uncle Bashir; Alhaji Isah yariqe Dadyna tamkar shi yahaifeshi baya nuna musu banbanci da Uncle Bashier har tasowansu
Dadyna kasuwanci yakeyi hakan yasa be cika xama ba bashinan bashican, anan ne yahadu da Mamina Hajiya Rabi'atu 'yar qasan Niger, ba'a jima ba Allah yamallaka ma Dadyna Mami sukayi aure yafantsama gidanshi anan Zaria.. Ana nan Alhaji Isah yarasu, da mutuwarshi da auran Uncle Bashir baifi 3month ba
Rayuwa taci gaba da tafiya cikin nasarori ba ga Dadyna ba baga Uncle dina ba, sai dai rashin haihuwa da Allah be ba Dadyna ba "awannan lokacin kuwa har Uncle yasamu qaruwar 'ya mace kuma ba jimawa akaimai canjin wajen aiki xuwa Kaduna yatafi da iyalanshi, sai yaxamana Dadyna da Mamina da Kakata ne anan Zarian
Bayan wasu shekaru masu yawa shima Dadyna yakoma Abuja da xama "kasancewar kasuwancinsa yafi qarfi anan kuma sai yataho da Kakata, xuwan Dadyna Abuja sai yaxama kamar *NASARA CE* (sabon littafina) tajanyo shi, domin kuwa ba qaramin bud'i yasamu ba, a Abuja baxa'a ambato mutane biyar masu kudi batare da an sako Dadyna ba "sai dai abinda suka rasa haihuwa
Sun dade kafin Allah yabasu NI, hmm farin cikin da suka nuna asamuna Allah kadai yasani "kuma tun daga kaina basu sake haihuwa ba, sunan kakata naci *NAFEESA,* Dady ne yasamin Beby amma yana cemin Mamanshi
Na taso cikin gata da soyayyan iyayena, duk tsananin qaunar da Dadyna yakemin be kai yanda kakata take min ba, domin kuwa kakata tanuna min son da kaf duniya babu wanda yata6amin, kuma bana tunani akwai wanda xaimin, ta sadaukar da duk qaunarta da komi nata akaina kamar ni ce kadai jikanta, nataso bansan babu ba bansan meye baqin ciki ba sai dai farin ciki da tsantsan qauna
Lokacin da nakai 12years aduniya kakata tarasu, nayi kukan da har saida nakwanta ciwo, Dadyna hankalinshi yai matuqar tashi har saida yadaukeni yafiddani waje, yawon qasashe da dama yakaini dan dai duk inmanta da *KAKATA* but hakan xaiyi wuya sai dai nacire tunaninta nadawo normal, ni tunda nake a *RAYUWATA* (tsohon littafina) ban ta6a neman abu narasa ba komi nakeso Dadyna yanamin that's why nataso cikin sangarta kuma nake tsula tsiyata yanda nakeso, Mami tana iya qoqarinta wajen nunamin hanyan da yadace amma ni a'a
In kaji Mami tanamin nasiha abu daya ne shine: rashin xuwa dangi, amma xan iya cemaka tafi kowa sangartani bcox saida nagirma sosai kafin tadena min wanka, koda tadena bata dena samin kaya ba har saida ni da kaina nace tabari, kuma ta'ajemin masu aiki har biyu komi xanyi su xasumin
Lokacin da nake ss2 Dadyna yakawo wani saurayi kyakykyawa gidanmu sunansa Anas, yabashi masauki yariqe shi tamkar d'an shi kuma yadaura shi akan harkokinshi., xuwan Anas gidanmu ba qaramin farin ciki yasakani ba "domin ni arayuwa inaso naga inada yaya ko qanwa sai dai ni rashin bin dangina da rashin son xumunci, but duk ranan da 'yen uwana sukaxo gidanmu ba wanda xaikaini farin ciki, nariqe Anas tamkar yayana shima yariqeni tamkar qanwarshi, duk wani so da qauna muna nunama juna "har wasu suke tunanin soyayya ce tsakaninmu, but ni dai awajena ko kadan banason Anas da soyayyan aure becouse aganina be kai matsayin ba
Rayuwa taci gaba cikin nasarori da farin ciki har xuwa lokacin da nakai level 2 a National Open University.. Ranan da baxan ta6a mantawa a rayuwata ba shine?...
Wai kuna kuwa jin dadin littafin? Ko kuwa abarshi ne?