🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3grils are the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
.
*EPISODE (25)*
*(Nafeesa)*Ko wani 6angare tuni sun soma gabatar da al'adunsu gunun sha'awa " biki yayi biki fa duk inda kagibta afadin Kaduna xancen bikin akeyi, to biki ne da yahada sanannu tako ina, kowa kagani cikin farin ciki yake
Matan Al'ameen fa?
Uhm tun sanda aka soma shagulgulan biki Dady yasa Momy ta'aika direver yakwaso matan Al'ameen, koda ta'aika Ummee shiryawa tayi takwaso kayanta na fitan biki suka taho da direver, ko kadan bata bada qofan da xa'a gane damuwarta ba saima shigewa cikin qawayen Ihsan tayi tasaje dasu akaci gaba da hidima da ita, while Nafeesa qin xuwa tayi, Momy tasake aikowa tataho can gidan ayi sha'ani dasu sabida nan din ba kowa sai su kadai " abinda Dady yahanga kenan shiyasa yace suxo nan ayi sha'ani dasu, amma me firr Nafeesa taqi xuwa " saima kulle kanta tayi a part dinta tadunga shar6an kuka kamar xata mutu, ko kadan takasa samun nutsuwa a xuciyanta duk da abinda ta'aikata ma Baby.
Shi kuwa Arif yana palow sai faman 6arnansa yakeyi bame kwa6arsa, to uwarsa tashige daki ta garqame kanta tahana kanta sukuni kamar yanxu ne aka soma mata kishiyan.
Ranan friday 11:00am aka daura auren *Al'ameen Abubakar Khabeer Chindo* da Amaryansa *Nafeesa (baby) Ismaeel Audu,* " sai kuma *Khamis Khaleed* tare da amaryansa *Baseera Abubakar Khabeer Chindo,* " *Haidar Muhammad Sani* da *Hannatu (Ihsan) Abubakar Khabeer Chindo,* daurin auren da yatara dubban jama'a iri da kala... qarfe 05:00pm aka shirya kai amare, xa'a wuce dasu wajen party daga can kuma akai kowacce gidanta, ita kuma Baseera qarfe 04:00pm akaxo daukanta " kasancewar Zaria iyayen Khamis suke dan haka xa'a fara kaita can ne, washe gari kuma saisu daga xuwa qasan London kasancewar acan kasuwancinshi yafi yawa dan haka acan yake da ninyan xama
Gidan biki fa yacika da kukan amare da hayaniyan 'yan biki " hakan yasa na lalla6a nafito na nufi gidan Alhaji Bashir Basho dan inje inga wani wainar ake toyawa.
Acan kuwa Baby har angama mata nasihanta tasha kuka ta gode Allah, ba komai yasata kuka ba sai iyayenta data tuno, sai da me makeup taxo tadena kukan aka soma mata kwalliya bayan tasaka wata farar doguwar riga gown me dogon hannun net, rigan irin wanda 'yan american suke sakawa in xasuyi biki.
Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, godiya ta tabbata ga Allah dayayi wannan halittan.
Nafad'a lokacin da nayi toxali da Baby time din da aka gama mata makeup aka shiryata tsaf, hohoho kuxo kuga yanda Baby tasauya " ni wlh bangane taba sabida gaba daya tasanja kamar ba ita ba, to abinka da wacce batayin make-up sai gashi tayi, manyan idanuwanta kawai sukasa nagane ta duk da sunsha toxali rad'au dasu eye shadow, dogon gashinta baqi sidik anmata packing dinshi a tsakiyar kai, na gaban goshinta kuma ya kwanta ya lafe gunun sha'awa, an rufe mata rabin fuska da white net amma duk da haka ana ganin face dinta, white hill shoes tasaka, komi dai fari ne ajinkinta ta bala'in yin kyau duk wanda yakalleta sai dai yace masha Allah, ga wani sihirtaccen qamshi dake tashi ajikinta.