🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱*WRITTEN*
Nafeesat I lawal
*(Feenah jikar lawal goma)**بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
'''{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}'''*⚜{{H.Q.W.A📚}}*
*3girls with the same Name* ❤*Wattpad : Ummuh 'Dahirah*
*Facebook : Muh'd Lawal Nafisat**SADAUKARWA*
Na sadaukar ga Mahaifiyata *Khadijah Lawal* da Yayana *Muneer Isameel Lawal**GARGADI*
Ban amince asauya min littafi ba. Duk Wanda yasanja min shi da Allah*Free Novel*
(Littafin kyauta ne) Mallakina ne..
*EPISODE (43)*
Agurguje please.
Sannu ahankali duk wani asiri da akai ma Al'ameen yafara sakin shi, dama addu'a bata faɗuwa ƙasa banza, har wannan Lokacin da Dady yasaka ariƙa sauke mishi al'ƙur'ani anayi ba'a fasa ba, dama sabida Boka na sabunta musu aiki ne to yanzu babu shi, lokacin Al'ameen na tsaka da barci yatashi afirgice yana salati gaba ɗaya ya haɗa gumi jikinsa sai rawa yake yi, duk abinda yafaru gaba ɗaya sai da yadawo mishi cikin kwanyan sa, addu'a kawai yake yi aransa Allah yasa mafarki yake yi abinda yagani ba gaske ne ba, dasauri yaduro akan gadon yanufi hanyan waje, so yake yaje part ɗin Baby yatabbatar da mafarki yake yi, amma tunda yafito yaga gidan ya sauya mishi yasan da cewa ba mafarki bane, agaske ya aikata duk abunda yafaru, zubewa yayi ƙasa yasaki wani uban ihu me haɗe da kuka, zuwa lokacin jikinsa wani irin ƙyarma yake yi kamar an jona mishi lantarki, ƙanƙame idanunsa yayi ƙam yana roƙon Allah yasa idan yabuɗe idonshi yaga mafarki yake yi be saki Baby ba tana cikin gidan nan, amma da yabuɗe idon sa sai yaga wannan gidan ne dai da yake rayuwa cikinsa batare da Baby ba
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."
Yafaɗa yana sake fashewa da kuka
"Meyasaa?"
Abinda yatambayi kansa kenan, dasauri yatashi kamar ana hankaɗa shi yasoma duba gidan, domin shi har yanzu be amince da abunda yafaru ba, ya yarda mafarki ne yayi ba gaske ne ba, but duk inda yaduba be ga kowa ba, domin Nafeesa tabar gidan tun ɗazu, sunyi da Samra zasu haɗu agidan ta na nan Kaduna zasu tattauna matsalan su, dasauri yazari keeys ɗin motan sa cikin ɗaki yafito a sukwane, yanda yake danna hon ɗin motan kaɗai ya isa yafirgita duk wani mahaluki dake gidan, cikin kaɗuwa me gadi yaja mishi gate, be kai ga ƙarishe buɗewan ba ma yaja motan da wani irin speed yabar gidan, gudu yake sosai akan kwalta kamar wanda zai tashi sama, duk inda yagibta sai an juyo an kalli motan.
Abakin gidan Alhaji Bashir yaja yatsaya batare da yashiga da motan ciki ba, yafito yanufi gidan tare da buɗewa yashige, me gadi na zaune a benci yaga shigowar shi dasauri yanufe sa yana gaishe sa, domin ya gane shi ne mijin Baby, batare da ɓata lokaci ba Al'ameen yace "yai mishi iso ciki" dasauri me gadi yanufi ƙofar da zata sadashi da palon Alhaji Bashir, jimm kaɗan yadawo yace mishi "yashigo".
....... ............ ..........
Sosai Baba yayi mamakin ganin Al'ameen agaban sa, cike da sanyin murya yakira sunan sa, sai dai Al'ameen yakasa amsa wa sai kuka yake yi kamar wani mace, bayan wani lokaci Baba yace"To ya isa kadena kuka, kafaɗamin me ke tafe da kai?"
"Baba ina Baby? Dan Allah Baba ku dawo min da matata ina ƙaunar matata, wlh bansan meyasaka nasake ta ba".
Tsananin mamaki ne yakusa kashe Baba ya kasa ma magana sai kallon Al'ameen ɗin yake yi, ƙara matsowa Al'ameen yayi yariƙo ƙafar Baba yana roƙon shi yana kuka, daƙyar Baba ya rarrashe shi kana yace