Chapter 2

41 6 0
                                    


who is fatima zahra
- Ni haifaffiyar abuja ce birnin tarayya mahaifina bafullantani jahar katsina ne dan karamar hukumar dabai tun suna kanana mahaifinsu watau kakana ya daurasu akan business di shi zuwa lagos saro kaya tun daga nan mahaifina dama na shawa'an kasuwan moto daga kotono zuwa gida nigeria daga siyan daya a saida har allah yasa ma abun albarka wani zuwa da yayi kotono sunje cin wata kasuwa a kauyen sangayu allah ya hada shi da mahaifiya wadda ko hausan ta baya fita sosai bafullatanan can ce babanta shine hakimi sangayu haka ya bita har gida sai da ya kasance duk zuwa sai ya biyo tun tana jin kunyan shi har ta saba soyayya mai karfi ta kulu tsakanin su sai da ya zama sai yazo har yayi sati biyu a anan magana su har ta kai ga magabata wanda da kyar mahaifinta ya yadda saboda babanci kasa ga nisa amma da sharadin cewa zai dinga kawota ganin Gida haka kuwa akayi anyi bakin su ba dadewa aka haifeni lokacin Allah ya buda ma Alh malik sabo har ya hada da harkan mai abuja suka koma dan ma daidaicin guri ina da shekaru uku mahaifiyata ta kara haihuwa aka samu na miji inda aka sa mai umar Farouk Allah yayi ma mahaifiyata ne rasuwa sakamakon hadarin motan da muka samu muna hanya katsina zuwa dabai bikin kanwar mahaifin mu duk da hadarin yazo da sauki amma karar buguwa da firgicin wata mota data gita mana shine yayi sanadin bugun zuciyan mahaifiyar mu cikin kankanin lokaci tace ga garinku
- Alh Malik sabo ba karamin mutuwar uwargidanshi yaji ba kasancewar yadda sukayi shakuwa gashi yana mata wani irin so na daban bayan wata biyar da rasuwa aka hadashi da zainab yar uwa shi daga Gida Zainab matace yar raayin kanta kawai ta Sani haka rayuwan mu kullum tana a wajen masu aiki in mun samu ta kirki muji dadi in kuma akayi rashin dace mu sha wuya dan ma dai Baban mu tsaye yake akanmu yana dai dai kokarin shi gashi ya dauki son duniya ya daura akan mu bama kaman ni da komai na mahiafiyata na debo muna kama sosai dan wata haka zai zauna yana hira damu har sai munyi bacci koh abinci yace tare zamu ci wanan abu ba karamin batama Mamy rai yake ba shiyasa ta dauki karan tsanan duniya ta daurashi a kaina
- Imran :-
- Emran Alee Akeel Karar disco kawai ke tashi a dakin amma mai dakin na kwance akan gado ya rufe ido a kan shinfidaden gadonshi da sha gara na alfarma cikin baccin rai na bude kofar dakin tare da daukan remote volume din na kashe gaba daya wanda yasa shi saurin bude ido tare da dan bata rai mommy ina kwana yace mun kara bata rai nayi nace haba Emran wanan shine gaisuwa ka tashi baza kazo ka gaishe mu sai ka cika Gida da disco sai kace ba dan musulmai ba sosa keya ya fara yi inda tayi murmurshi tace oya maza kayi wanka kazo muyi breakfast kuma ka zama ready please by 8pm jirginmu zai tashi bai ansata ba amma tasan duk abun tace yaji kuma hakan zaiyi fita tayi tare da bar mai dakin
- 8pm dot jirgin mu ya tashi sai Cyprus ni da mommy dama wanan sabon ta duk komawa sai ta rakani sanan hankalinta yake kwanciya sanan takan zo mun hutu har ta kai sati biyu kafin ta koma wata ranar suna zuwa da dad amma most of the time indai zata kwana biyu toh ita kadai take zuwa
- Who is Emran Alee Akeel Alh Alee Akeel fulani jimeta ne a jahar adamawa auren zumunci yayi shi da matan shi ya kasance Baban dan boko ne mai ji da ilimin shi ga son rayuwan Turai yanzu haka suna daya daga cikin manya gwannati a birnin taraya wanda ake damawa dasu duk da wanan bai hanashi business ba da kasashen ketare ga jini saurata tun taso warsu sun tashi cikin Baban Gida hajia Asiya matar shi mai matukar kirki da Sanin ya kamata tun auren su sun dadde basu haihu har Allah ya basu Emran tunda ta haife shi kuma sai haihuwa shiru abunka da bature bai damu haka ya dauki son duniya suka daura ma yaron basa ganin laifinshi ko kadan

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now