Chapter 44

14 3 0
                                    

life goes on
Haka rayuwa ta kasance mana ma zahra da imran cikin soyaya da kaunar juna shirin gama makaranta ya kankama da taimakon imran na gama project, rahama ma anyi nauyi haihuwa koh yau koh gobe , yau mun tashi kasancewar weekend muna mane da juna sam imran yaki bari koh site dinna inje mun fito wanka kenan waya ta fara ringing rahama ta haihu aikuwa ba shiri mukayi asibiti murna wajen mu ba'a cewa komai tun daga ranar na zama busy kullum ina wajen mai jego ranar suna yarinya taci sunan kakarta Maman Mahmoud salma,
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah yau auren mu har ya kai 4 years later inda rahama na da yara biyu salma da Suraiyya amma mu shiru koh batan wata, tun abun baya damuna har ya fara damuna shi kam gogan naka koh ajikin hatta master degree dinna na gama a USA kasancewar aikin shi yafi yawa acan kullum ina kai kukana wajen Allah shi kam imran daga yagani cikin damuwa toh yanzu hankalin zai tashi yayi ta kwantar mun da hankali, wani hutu karshen shekara da ya dauka munje Nigeria dukka kwanan mu uku, yasa ni wani shirin zamuyi tafiya ni dai binshi kawai nayi dan yaki gaya mun kawai sai gamu a Cotono, ya gama arranging komai nashi aka zo aka dauke mu da wata Hilux wanda sai da mukayi ma su Inna shopping bayan mota cike da kaya sai sangayu baba tsoho muka fara hangowa waje yana ta karantun kur'ani da daliban sa a gefe, shi ya fara tarbo mu Inna kuwa dan dadi hadda kwala, a sabon  gini da Abba yayi musu ana muka sauka abunka da fulani basa ma amfani dashi sai da a gyara a kule, komai na zamani ne dakine da fallo da toilet, wajen inna naje tuwo ne naci dan ko imran ban jira ba haka naci na koshi gamawa ta keda wuya sai amai da gudu nayi toilet sai da na amayan dashi dukka koh huran kasan sha nayi sai da inna tayi mun farau-farau , ranar dai haka muka kwana sam jikina ba dadi, munje da niya kwanar uku amma kwana biyu da kyar akayi shima dan ba ticket dan tun washegari yazo mu juyo saboda asibiti, muna sauka abuja asibiti muka wuce straight wanda ba bata lokaci aka hau gwaje gwaje nan da nan aka gano inada ciki aikuwa murna wajen imran baa cewa komai , sai ya bani tausayi dan yau na tabbatar da yana son yara kwantar mun da hankali kawai yake , tun gurin Dr na sha kiss a goshi yafi a kirga he can help him self, tun da muka koma gida komai ya hanani inyi hatta wanka shi yake mun ga cikin yazo da laulayi , duk abunda muke ba wanda yasani banda rahama dan sam yaki yadda a gaya ma su mommy ace wan shi is a surprise
Dole imran ya kara hutu saboda baya son mu tafi ciki baiyi kwari ba, ciki na wata uku mukaje scanning nan ake gaya mana yan biyu ne ai murna sai ta karu, hamdalah kawai nikeyi ma ubangiji muna hanya mommy ta kira cewar in dai baza muzo ba toh ita tana hanya ta gaji kullum a kawo mata diyar ta amma shiru, ganin imran bai da alama ce mata zamu yasa ta katse wayar mun dan biya shopping mall muka siya one or two things kafin mukayi gida, a fallo muka iske mommy cikin farin ciki na gaida ta sam na manta da takardar scanning na hannu na kan table na aje, ansawa tayi amma hankalin ta na kan paper dauka tayi wanda kunya ta ida rufeni dai dai shigowar imran , kallo tabi dashi nikam inata kasa da kai salati ta rafka, tace dama yaran nan abunda kukayi mun kenan, imran yayi tsuru-ru hakura ya fara bata tace rufe mun baki, dama raina ya bani da wata kasa kwana biyu diyata shiru, ban ganta, dan bata rai yayi yace mommy nifa ba kina ganina ba , paper scan din ta kara kallo sai farin ciki gani jika ba daya ba har biyu ma hugging zahra tayi tana ta shi musu albarka hadda kwala, imran banda sosa keya ba abunda yake yi, sumi sumi ya wuce na mommy tace dawo nan bamu gama ba yau kafa ta kafar zahra, gidana zata koma, gara bata rai yayi cikin shagaba yace mommy nifa, please mommy am taking good care of her here, da kyar da mommy ta barsu a cewarta sai dai su koma gidanta dukkan su, da kyar imran ya lallaba ta tayi hakuri

Hasken-taurari book 1Where stories live. Discover now